✨MIJIN AMMINA NE SILA(COMPLET...

By NoorEemaan

7.6K 310 5

labari mai matukar ban tausayi, son zuciya, soyaaya mai zafi da shiga rai, hadi da nadama..... More

1
2
3
4
5
6
7
8
9
10
11
12
13
14
15
16
18
19
20
21
22
23
24
25
26
27
28
29
30
31
32
33
34
35
36

17

165 9 0
By NoorEemaan

🍇🍇MIJIN AMMINA NE SILA🍓🍓
(A heart touching story)

written by noor Eemaan

page-33-34

kura masa ido yayi yayinda yake jin wani yanayi atare da kyakyawan saurayin da ko fuskarsa baya gani, haka kuma yaji hankalinsa gaba daya ya raja'a ga wanna saurayin wato Aabaan.
"oga ya kana yawa ne, kazo mu tafi muyi abunda ke gabanmu ko ya?" manu ya katse masa tunaninsa cikin muryansa wanda daga ji zaka tabattar da cewa shi din mashayine...

Ajiyar zuciya alhaji Shettima yasauke batare da ya kuma bawa manu amsa ba suka nufi cikin asibitin still hankalinsa naga Aaban,.... duk wani ward dake cikin asibitin suka duba amma babu ko me yanayin kalar fatar Abrar bare me kamaninta, guiwa asanyaye suka fito yayinda alhaji Shettima ya kurawa daidai inda motar Aaban ke fake dazu ido, sai de yanzu motar bata nan, huci mai zafi ya furzar ya kasa gane dalilin daya sa tunanin wanna saurayin kasa barin zuciyarsa.
"oga da dukkan alamu bakuyi nasara ba domin naga fuskarsa tayi ja jawur kamar jan kosai" kwaro ya fada ko dar be ji ba, alhaji Shettima ya saba da maganganun kwaro domin akwai yaba wa mutum magana mara dadi musamman idan ya shahu, maimakon ya bashi amsa se yace "kwaro baku ga wani saurayi tsaye a kusan da motata dazu ba?"
"Allah ya ja da ran oga ina mu ina lura dashi tunda ba abunda ya kawo mu ba kenan".
alhaji Shettima be kara cewa komai ba ya bawa motar wuta suka bar asibitin.....

bangaren Aaban kuwa yana isa gida ya tarar da mummy zaune kan kujera, gaisheta yayi ta amsa ba yabo ba fallasa, hakan ya kuma taba zuciyarsa domin ba haka ta saba tarban sa ba, part dinsa ya nufa yana fatan har yanzu Abrar bata tashi ba, mummy da kallon takaici ta bisa ganin wai saboda Abrar ya daina night duty ita shekara nawa tana fama dashi akan ya daina aikin daren nan amma yaki sai yanzu saboda mahaukaciya ta aiyana aranta....

yana shiga dakinsa ya dora hannu a kugu ganin yadda dakin ya dawo kamar ya shekara be ga gyara ba, kallonta yayi yaganta zaune da kayansa riga da wando ta dora saman doguwar rigar jikinta, murmushi dabe shiryaba ta tsubuce masa, domin kayan sunyi mata yawa matuka, cikin tafiyarsa ta lafiyayyen namiji ya shiga takawa zuwa gareta, kusa da ita ya tsaya yayinda ya kura mata idanunsa masu matukar kyau, sai a lokacin ta lura da shi, dariya ta shiga yi kana ta hau saman gadon sosai ta shiga tsalle tamkar yar shekara 5 kallonta ya dinga yayinda murmushi ya kasa barin kyakyawar fuskarsa, gasashiyar kaza mai romo daya siya mata ya bude mata ledan hadi da janyo yar table din glass ya dora akai, hannunta ya kamo ya zaunar da ita yayi mata nuni da naman, take kuwa ta fara ci da hannu biyu, hadi da debo romon da hanunnta ta dinga sha, kura mata ido yayi yana mata kallon birgewa... sai daya gama more kallonta kana ya shiga gyaran dakin domin duk gajiyan daya debo baya jin ze iya zama haka cikin dakin, bayan ya gyara ko ina ya dawo hayyacinsa kana ya bude sif dinsa domin daukan kaya sawa saboda so yake yayi wanka ana daf da kiran magriba, jiyayi ta rungummesa ta baya tana goge idanunta abayansa, kallon hannunta dake rungume akirjinsa yayi yaga gaba daya ta shafa masa ruwan romo da mai hannunta farar rigarsa, saurin juyo da ita yayi yaga tana ta runtsa idanunta, da alama tasa yaji ne idon, sai kuma ta sake daukan hannun yajin tana murza idon dashi, kamo hannun yayi ya nufi toilet da ita cikin sauri, sabulu yasa ya fara wanke hannu kana yasa tattausan hannunsa ya shiga wanke kyakyawar fuskarta sai daya tabattar dacewa yaji ya fita, bayan ta bude ido ta kalli kanta amadubin dake gaban sink, sai ta kuma juyawa ta kalle shi hadi da kyakyale dariya, kumatun ta yaja kana ya riko hannunta suka fito, direct kuwa ta nufi wurin sauran kazarta, cikin hanzari ya dauke ya shiga yagowa yana sanya mata a baki, haka ya dinga yi mata har ta cinye tas, hannunsa ta kamo ta sa harshenta ta shiga lashe hannun, kallonta kawai yake batare da ya hanata ba sai don kanta ta sakar masa hannun, a kwandon shara ya zubar da ledan kana ya shiga toilet, shower ya sakar wa kansa yayinda ya dafe bango da dukkanin hannayensa ruwan na dukan lafiyayyen farar fatarsa, yayinda tunanin yadda ze mallaki Abrar ke yawo azuciyarsa, yasani baya da matsalan komai se mummynsa yakuma rasa ta yadda ze bullowa al'amarin...
cikin toilet din ya sanja kaya kana ya busar da sumarsa da hand dryer ya fito, yana fitowa aka kwalla kiran sallah beyi wata wata ba ya bude kofar baya ya nufi masallaci dake cikin gidan, bayan ya dawo ya ganta kwance bacci ya dauketa, rigar nan ta tattare izuwa wajen cinyarta, take idanunsa suka gano masa kafarta da daya tafi daya kumburi, cikin sauri ya karasa gadon bayan ya gyara mata rigan, kafafun ya dora kan cinyarsa, ya kuwa ga daya yafi daya kumburi nesa ba kusa ba, dafe kai yayi cikin tausayinta yanzu dama kafarta tayi targade take tsalle tsalle hadi da gudu? shin bata jin zafi ya tambayi kansa, shi kam be taba lura ba domin rigar daman har kasan kafarta ta rufe gashi bata yi wata alama daze sa ya ankara ba, yama rasa yaushe taji wanna targaden? Gwada taba kafar yayi yaga bata motsa, sake tabawa da dan karfi yayi domin so yake ya gyara mata, takuwa farka ta sakar masa ihu hadi da kai masa bugu, be hanata ba har ta gaji ta daina, hadi da takurewa waje daya,
"am so sorry" ya fada yana kallonta, mutuniyar ko kallon gefensa bata yi ba.

Shimfuda sallaya yayi ya dauko qur'ani ya shiga karatu har aka kira ishaq kana ya mike, cikin nutsuwa yake gabatar da sallahn'sa bayan ya iddar yayi addu'oinsa masu tsaye, kana ya ninke sallayan, wayarsa ce ta fara ringing "my Dad" ya gani arubuce, amsa kiran yayi hadi sallama, daga bangaren daddy bayan ya amsa yace
"abokina ku sauko kuci dinner muna jiranku"
da kallo yabi wayar bayan daddy ya katse kiran, shi kam beso hakan ba, amma ba yanda ya iya, daukarta yayi cak suka fara saukowa, domin sam bayaso ta dinga take kafarta saboda dada kumburi ze kara yi tunda ba'a gyara ba, ya kuma san tana jin zafi kawai yanayin gushewar hankalin datake ciki yasa sam bata nuna alama..
suna daf da zuwa inda suke ya sauketa, kana ya rigo hannunta suka karasa wajen
"mum dad barka da dare" ya fada yana jawa Abrar kujera, daddy kadai yace "yawwa barka kadai abokina" yayinda mummy ta cika tayi fam tun lokacin da daddyn yace su sauko ta fahimci da Abrar yake nufi, ita yanzu komai ya jagule mata domin daddy ya dauke mata wuta sam yanzu baya shiga harkanta wanda tasan cewar fushi yake da ita domin sarai tasan halinshi, ga kuma danta mafi soyuwa aranta basa cikin yanayi me kyau, wanda hakan ke domunta domin ba haka suka saba rayuwa ba, gashi kuma bata san Abrar zuri'arta...

Bangaren Amal ma haushi ya cikata, ita wallahi ta tsani abrar, Hanan ce ta kai kallonta ga Abrar dake takure tace
"bestie Abrar yakike, how's your health"
Abrar kurawa Hanan ido tayi kamar meson tuno wani abu se kuma ta yi dariya hadi da maimaita abunda Hanan din tace, dariya daddy da hanan din suka mata, hanan tayi serving din su kana ta cikawa abrar plate hadi da nama da yawa domin tasan Abrar bata wasa da nama, tana direwa gabanta ta shiga ci hannu baka hannu kwarya, Amal da mummy se antaya mata wani mugun kallo suke yayinda Amal ke nata aboye domin tasan matukar ya Aaban ya ganta ta banu... sede Abrar batasan suna yi ba domin hankalinta naga abincinta...

Daddy ne zaune a bedroom dinsa yayinda laptop ke kan gado yana dannawa da alama abu me muhimmanci yake, fuskarsa sanye da medicated glass, ahankali ta bude kofar ta shigo, kan gadon ta zauna tace
"ina son magana da kai daddyn'su"
yakai muntuna goma be bata amsa ba, kana yace "ina jinki"
"haba daddyn'su laifi me na maka har haka"?
sai alokacin ya kashe laptop din hadi da zare medicated glass din idonsa yace" ni kike wa wanna tambayar? baki ji kunya ba? tsaya in tambayeki aysha mi kika dauki kanki eh? kina tunanin ita yarinyar nan Allah baya sonta ya jarrabe ta? ko kina tunanin Amal or Hanan bazasu iya shiga wanna halin datake ciki ba? shin idan sune awanna halin zaki ji dadi ace sun samu masu son su tsakani Allah amma uwar mijin taki amincewa? yi tunani ya zaki ji aranki, kamata yayi ki godewa Allah ya baki da nutsatse, kina tunanin cewa bazan iya aura masa ita ba ko ba da amincewarki ba? toh idan hakan ne tunanin ki, kinyi karya domin nine ubansa ina ko wani right akansa, dalili daya ne ya hana ni aikata hakan domin kawai yasamu albarkanki arayuwar auransa, kin ki tsaya ki ji abunda Hanan zata ce mana, ko Hanan bata ce komai ba ninasan kaddara ce ta fada wa Abrar domin aranar da'aka yi taron su a cyprus duban jama'a sun shaida nutsuwarta, cikinsu harda ni, amma saboda bakya ganin girmana muna magana a gaban yara kika zage yar mutane kika fice afalon bayan bamu gama magana ba, hakan da kika yi yadace? ya kamata ki nutsu kiyi tunanin, ace zabinki shine zabin danki batareda ku biyun ku san da hakan ba, bakya tunanin akwai wani alkhairi a tarayyansu? gaba daya kin aro wa kanki wata dabi'a mara tushe saboda kawai son zuciya da kuma bakin mutane, da bakin mutane na kisa da tuni bama a raye yanzu, idan bama taimakon juna tayaya zamu cigaba, mai kudi yace lallai sai me kudi, talaka sai talaka, mai hankali sai me hankali, mai lalura sai me lalura, gaya min idan bamu taimakon juna tayaya zamu samu cigaba akasarmu da ma duniya baki daya, arayuwarnan idan zaka yi abu yishi da zuciya daya hadi da kyakyawan niyya sai kiga Allah ya faranta miki ta hanyar da baki yi zato ba, ina shawartarki kiyi a hankali kada ki ji kunya nan gaba, ke musilma ce ki yarda da kaddara me kyau ko akasinta ta haka ne imaninki ze cika" .... daddy ya karasa maganar cikin fushi, sai kuma yace "ki rufemin kofana idan kin fita bacci zanyi" yana gama fadin haka ya yi kwanciyarsa hadi da juya mata baya, hajiya mummy kuwa hawaye ke zuba idanunta wanda na kasa gane ko na menene, takai mituna sha biyar masu kyau tana tunanin maganganun da daddy ya fada mata, kana ta mike asanyaye ta fice zuwa dakinta, nan ma kwanciya tayi kan makekken gadonta tana juyi yayinda kalaman daddy ke mata yawa akunne.

Wanna kenan

Washegari kuwa Aaban ya kai Abrar gidan wani gyara domin agyara mata kafarta, lokacin da mutumin ya fara gyaran ta runkunkumeshi, sosai take ihu mai dauke da kuka hadi da dariya, bawan Allah Aaban kuwa ya sha cizo, da yakushi, an dau tsahon lokaci ana gyaran domin kafar tayi tsami sosai, wani magani mai kamar mai ya bawa aaban yace a dinga shafa mata, kudi masu yawa Aaban ya bawa tsohon kana suka fito daga soro gidan mutumin tana rungume gefen sa...

yana kokarin sata a mota, daidai lokacin motar alhaji shettima daya bawa su kwaro domin neman abrar ta gifta, "wait wait mana, kwaro kamar ga yarinyar nan da oga ke nema fa" inji manu....

bangaren ammi kuwa gaba daya tasake lalacewa saboda damuwa, da abinci da bata iya ci, komai ya gama fice mata arai har da garin, tana add'ua Allah ya bata sa'an fita daga gidan idan ta nemo yarta zata koma kasarta ze fiye mata, tana awanna tunanin taji ana bude dakin alhaji ta kuma san da kyar alhaji shettima ya dawo awanna lokaci, cikin daga murya

tace "waye nan? abude ni dan Allah!!!"

cikin mamaki wanda ke kokarin bude kofar alhaji ya dakata hadi da nufar kofar dakin ammi yace
"matar yallabai ce?"

cikin rawan murya ammi tace
"eh nice, rufeni yayi adaki, batareda yasani ba"

mutumin be kawo komai aransa ba duk da yayi mamaki....ya kuwa zare sakatan hadi da bude kofar, take ammi taga mutumin ya bayyana wanna zeyi shekaru 38, cikin son daidaita yanayinta tace

"nagode bawan Allah"

"a'a babu komai ranki ya dade, dama sako ya aiko ni dauka yace ya manta ta adakinsa".

"ok toh je ka daukan masa"

tana ganin fitarsa ta zari hijab kana ta lallaba ta fito, tana fitowa haraban gidan ta daidaita nutsuwarta kana ta nufi bakin get, masu tsoron gidan na nan, duk da atsorace take domin bata sani ba ko alhajin yasanar dasu kada a barta ta fita? tana daf da isa bakin gate taji maganar daya daga cikinsu, cak ta tsaya jitayi yace
" hajiya bari a kaiki amota"
ajiyar zuciya ta sauke a boye kana tace "a'a barshi kawai, inason mika kafata ba nisa zanyi ba"... jinjina kai yayi alamun gamsuwa kana ya koma bakin aikinsa.

cikin gudu gudu sauri sauri ammi ke tafiya yayinda take fatan kada ta hadu da alhaji, sosai take sauri har tayi nesa da unguwar maraba ta fada unguwar masaka batareda ta sani ba, horn take taji abayanta gaba daya ta rude tama kasa motsi har motar ta bugeta... cikin sauri mutanen motar suka fito da sallati abakinsa macen ce tadago kanta tana fadin sannu! cikin zaro ido hadi mugun mamaki tace "Rahilat!"
"nadeem kanwata ce rahilat, kataimaka min kana ta mutu....

(ku cigaba da bina dan jin yadda zata kaya, shine, Abrar harma da ammi zasu kubuta ahannun alhaji Shettima? kuma su kwaro na samun nasaran gano abrar? shin wani yanayi ammi zata kasance idan taga yayarta? ya alhaji shettima zeyi idan ya fahimci ammi bata gidansa, sannan wani mutum ne ya taimaki ammi meye kuma alakarsa da alhaji shettima? shin mummy na amincewa da auran Aaban da Abrar? amsarku na nan duk cikin littafin mijin ammina, just be patient zan warware muku zare da abawa).😉👌

SHARE✔
COMMENT✔
VOTE✔
EDIT❌

Noor Eemaan✍☺

zaku ji ni gobe in sha Allah, son so my people😘

Continue Reading

You'll Also Like

59.3K 1.4K 40
standalone ~ mafia siblings series "You can't make me stay here! I will get an emancipation." I yell. Flashbacks of the gun in my hand, the almost-de...
64K 3.3K 54
The Rajputs well known as the most powerful and devil's for the people who tries to messed up with them people got goosebumps just by listening to th...
143K 7K 28
Hooked onto drugs, no family, no guidance or sanity until she met HIM. Cover Creds: @Triceynexttdoor ❀️ -BLICKY.
40.3K 3.7K 10
Wanna visit rajasthan than read this special book about my love Rajasthan πŸ’—