FOREVER YOURS

By Ayshasamira

54K 3.4K 1.3K

Khadijama Is half Shuwa Arab,a Gentle and simple lady in her mid twenties,follow us as we peak through the li... More

Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 35

Chapter 34

1.2K 73 15
By Ayshasamira

💞💞💞💞FOREVER YOURS 💞💞💞💞By AyshaSamira💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
Chapter 34.........
Wattpad@Ayshasamira
Twitter @Scarlet_Samie

Ba shiri ya ce ma Suraj Daddy ne yake nemana just bari naje if dare baiyi ba zan dawo,ya fita da sauri......

Yana zuwa Aunty Saima kawai ya gani zaune da Asmah,ya shiga ciki ya samu Daddy yana daki,daga can yace shigo mana Abbaty......

Ya yi sallama ya shiga yace Daddy badai jikin bane ko?Yace bana jin dadi yau dinnan amma nasha magani....

Ya tashi zaune,Yace bani ruwan can ya miki mashi swan da cup ya zuba mashi ya sha yace yauwa nagode.......

Yace Abbaty a gaskia kayi dacen mahaifiya wallahi Hajiya Maryama mutum ce kuma uwa ce ta gari a kullum ina alfahari da auren ta da nayi....

Kana gani Shatu kanwata ce amma bata son Yar danuwana kawai saboda kawar ta tayi son Hussain sai shi kuma a school ya hadu da Rahama yace shi lallai Rahama yake so.....

Nan tace an asirce mata danuwa ban taba zaton tsanar Rahama zata shafi Duk abunda Hussain zai aura ba but Shatu is beyond that kana gani....

Amma mahaifiyarka son da take ma Kubra ni kaina abun na bani mamaki kuma tuntuni haka take tun Hassan na raye taso ta amshe Kubra sai shi kuma Allah ya sa ita kadai zai haifa.....

Abbaty ina jin dadin mu'amalar mahaifiyarka da Khadijatu da duk zuri'an Khadijatu ma,and i really appreciate.....

Kaga tayi fushi sosai yau da kai dinnan wallahi abun ya mata haushi ni kaina i felt bad da kasa ka mun Khadijatu kuka.....

Amma nasan bazai wuce zancen breastfeeding din ba ita kanta Hajiyan tayi magana amma tace may be saboda tana kunyar su ne....

And ni i realized yanzu wani irin kunya yake damun Khadijatu and i dont like it saboda she is trying to distance herself daga jikinmu tana daukan mu In laws which shouldnt be but we arw humans......

So please Abbaty ka yi hakuri nasan mata da miji dole akwai obstacles i wanted to scold you but then nace ba lallai laifin ka bane.....

Amma ka mata a hankali you are a Doctor ka fimu sanin may be akwai abunda ke damu ta or something,you are her husband please Abbaty a dinga fahimtar juna.....

Kaga bana son ana bata mata rai amma kuma nasan dole zatayi laifi watarana ka dinga hakuri kai kanka ina kula dakai Abbaty duk ranar da kayi fada da Khadijatu baka sakewa ko yanzu kalla yanda duka idonka yayi ja.....

Yayi murmushi yace Daddy ayi mun hakuri sharrin shaidan ne,kuma nagode sosai da yau baka ga laifina ni kadai ba,insha Allah zan gyara amma sai inga kaman ko kallon Babyn bata sonyi....

Daddy yayi dariya yace kunya na ke gaya maka ya kama Khadijatu kaman wata bafilatana amma larabawa ma suna da kunya amma Kausar tace idan ba kowa tana kallon yaron sosai ta dinga murmushi su Hajiya take kunya.....

Abbaty yaji dadin wannan maganar amma dai Daddy baisan yr tasa kishin ta ne ya motsa ba,tab ashe haka take da kishi har tayi kokarin zama da Fareedah.....

Daddy yace kaga duka yaushe ta haihu ka lallabata kafin Hajiya ta hanaka daukan matarka,suka yi dariya....

Dan Allah Abbaty amanar Khadijatu na baka kaji bance wai ba zata saba maka ba amma adai rika amana dan Allah....

Ana tsawatawa amma ba kayi fushi har ka fita kana fushi ba bakyau hakanan ku zauna ku yi understanding juna kaaina babba kaine miji kai ne Allah ya bama wannan girman.....

Yace insha Allah Daddy zan gyara kuma na rike amanar da ka bani zan ci gaba da rike ta insha Allah....

Yace to shikenan zaka iya tafiya kada dare yayi maka ai,Yace Daddy amma yakamata kaje check up fa naga ciwon yana so ya kwantar da kai ne,....

Yace to yanzu kamata yayi idan ka natsu zuwa next week sai ka rakani tunda Rashid is somehow busy yanzu....

Yace to Daddy zanyi booking appointment insha Allah,nagode Allah ya bar mana ku,Yace Ameen Abbaty Allah ya maka albarka.....

Na samu na daina kuka,ina zaune ni kadai ma a dakin ina missing Mamana,Kausae ta shigo nace yauwa kinga Kausar ga wannan na janyo jakata na bata kudi nace kinga 500k ne ina so ki siyo mun sarka na Gold da earrings masu kyau....

Tace to amma ai naga kina da wannan da kika siyo daga Riyahd ba ita zaki saka ranar suna ba?

Nace eh kudin ne bana so na kashe ban siya wani reasonable abu ba,tace eh to hakane gobe zan siyo miki insha Allah....

Nace Kausar kiyi hakuri ina sakaki wahala kema ba wani karfi ne da ke ba,tace haba Andeeja me kike yi haka ni taki ce ke tawa ce....

Wanne sauki ni garas nake ko yanzu sai na je turakar Faisal,nayi dariya nace meye ne wai Turaka?

Tace wurin miji ko ince dakin miji,nace lallai ma ai nikam akwai aiki anya zan iya bari miji ya matso ta saka dariya tace traumar haihuwan bata sake ki bane Matar Mijinta?

Nace eh fa nidai,tace yauwa me ya sakaki kuka dazu kinsan bama blye ma juna komai ko?

Nace eh ina ta so na gaya miki ko zan ji sanyi a raina,ina wannan Dr din da tazo aka amshi haihuwan nan?

Tace Fateemah?Nace A'ah ai Fateemah tana da aure ko?Tace eh Tana da aure mijin ta Chief judge ne....

Nace to ba ita ba,tace au wannan gajeruwar Asiya ko me?Nace ita fa kuwa rashin tsawo ya ma isheta kinga sai naga ta kirashi shine fa nayi magana ya bini da masifa....

Kaman zai kai mun duka kawai ya tashi ya fita ba dole nayi kuka ba nama rasa me ke mun dadi kinsan ina son Yaya fiye da tsammani da ina hiding kishina amma yanzu na rasa dalili wallahi Kausar ba zan iya ba ina son Yaya sosai......

Ke kinsan na dade ina son Yaya,na samu yanzu ni kadai ce sai a jajibo mun wata likita.....

Kausar tayi dariya tace gaskia bazan san halin namiji ba amma Yaya Abbaty da kaman wuya ya kulata ai kinsan abun Fareedah ya taba shi sosai....

Abbaty yana sonki Khadijama trust him mana da a hankali kika bi abun amma i promise zan binciko miki....

Nace to ni yanzu ya zanyi y daina fushi dani?Kausar tace to ai kinfi kowa sani muryarki kadai rikita mijinki takeyi jikinsa har wani rawa yakeyi gaskia Abbaty nasonki Andeeja na miki murna fa sosai.....

Nace nagode kinga bari na kwanta kafin Boy ya tashi bacci nakeji amma ina so naji muryar Yaya kuma bazna iya kiransa ba.....

Tace ai kuwa yana ma wurin Daddy idan ba yanzu ya fito ba dan Aunty Saima tayi jiransa bai fito ba....

Nace to Allah ya huci zuciyansa tayi dariya tace oh wai Yayan nan mai yelling ne ake missing haka iyyeh....

Na kai mata duka,na kwanta nayi bacci na banma san wanda ya kawo mun Babyn ba......

Shi kuma Yaya yana fitowa dakin Daddy ya nufato dakin Hajiya,yana kaiwa bakin kofa yaji Khadija na gaya ma Kausar abunda ya bata mata rai da son da take masa......

Yayi murmushi ya juya ya tafi a gida ma juyi kawai yake yayi missing nata muryar nan mai dadi,ya janyo wayarsa....

Past 2 am ya kirata yana kira ta dauka yace Baby dama baki kwanta bane?Nace eh ban kwanta ba lafiya dai?

Yace na kira na baki hakuri ne kan abunda ya faru,nace ai bani zaka bama hakuri ba Yaya Abbaty idan aure kake so sai ka je kayi Allah ya baku zaman lafiya kawai na sa kuka na kashe waya.....

Ya dafe kai wai ni yaushe Babyn nan ta fara irin wannan kishi na masifa i thought ta huce fa shikenan bara na daga mata kafa dukanmu mu wahala kenan......

The next day daren suna kenan around 2 su Ammin Abuja,Ayaana,Falmata da su Aunty Yagana suka diro birnin kano...

Farin ciki guna ba'a cewa komai nayi kewarsu sosai wallahi,na ji dadi sosai muna ta shan hirarmu....

Ammi da nata kayan gyara ta zo ta shiga gyarani cikin raina ina cewa wanda ma fushi yake dani....

Yaya Abdulrauf kuwa baki baya rufuwa,can da yamma ya shigo ya gaishe da su Ammi kai a kasa......

Suna ta shirin biki nidai gani nan Hajiya sun gayyato yanuwa da abokanan arziki hankali na nakan kishin Abbaty.....

Ban saka shi a ido ba sai da yamma ya shigo, yayi musu sannu da zuwa banma daga kai na kalle shi ba,Kowa ya fita daga ni sai shi sai Ammi,Ammi tace ga Andeeja nan muna fama da ita....

Yace ai Ammi sai an mata fada duk ta canja ne nima na rasa meke damunta,nidai ina nan kwance kan kafar Ammi,banma saka musu baki ba....

Yace Ammi ki bata hakuri dan Allah,Ammi tace ai ka barta zan mata fada insha Allah Abbaty Allah yayi muku albarka......

Aunty Yagana ta shigo suka gaisa tace munga fa hidima an gode sosai Allah ya kara budi,ya sunkuyar da kai yace ai Ammi bakomai....

Ammi ma tace mungode sosai Abbaty gaskia kasha hidima Allah ya kara hada kawunan ku......

Rashid ya shigo suka gaisa suka fita tare can kasa ya hadu da su Kausar yace au ina Matar Yaya Abdulrauf a cikinsu?

Kausar tace gata nan mai sunan matarka suka saka dariya,Falmata tace to nidai kasan ba ni bace yace ai kema Matar Yaya ce ....

Falmata tace ni banga Angel din Kaduna ba,Yaya Rashid yace ni kaina ita nake ta neman wayanta baya shiga.....

Ya tambayi Innah tace ai sunje ne siyo abu ita da Matar Yaya Abdulrahman da Asma.........

Suka gama harhada surveniers din suka dawo sama,Ni kadai a dakin Babyn a hannuna na kura masa ido ina kallansa nace Allah sarki kaga Abbanka yana fushi dani.......

Idona ya kawo kwalla,Kausar ce ta fara shigowa tace Andeeja yadai?I swiftly wiped my tears nace Kausar sannu da aiki,tace wai baki saka kayan kika gani ba?

Nace kinsan bana son saka kaya sai ranar da zanyi using ne,tace please daure saka ki gani nace to na ajiye shi na gwada tace wow perfect....

Nace nayi kiba ko?Tace ke kika sani dama ke da mijinki ai ba ramammu bane,muka saka dariya.....

Su Falmata suka shigo ana ta waya ,nace wai me ya hana Ayshatu zuwa naga Babynta tayi 3 months ai....

Tace ai next week zata dawo gaba daya shi yasa kinga tazo ta koma nace eh haka ne kuma,Kice next week Suraj ba sauki.....

Kausar tace nima fa upper week ne zan tafi,na rike hannunta nace ki bari dan Allah duk har hankali na ya tashi....

Tace ai na yi kokari Andeeja watana 6 fa,ina missing Faisal dina Farha ma jiya sai da ta tambaya fa yaushe xamu bar gidansu Aunty Khady.....

Da gaske?Na tambata tace eh ai ita fa nan gidanku ne bansan waye ya bata notion dinnan ba....

Falmata tace to kullum a anan take ganin Andeejan,nace ina yaran ne yau gaba daya basu hawo nan ba.....

Kausar tace ai Kinsan tunda Hajiya na kasa tana aiki ba zasu hauro ba,ke in baki labari kinga yanda Yayanki ya iya soyayya?

Nace ke wanne Yayan wai?Tace Yaya Abdulrauf mana kingansa nace eayyo me yasa baki kirani ba naso na gani wallahi muka kwashe da dariya.....

Falmata ta ce au Kausar harda ke surukin nawa,mukai dariya tace ai bai kai Abbaty ba ma,ai kuwa akayi kiran Kausar ta sauka da gudu.....

Muna ta hira da Falmata nace ke gumbar nan da Ammi ta bani akwai dadi sosai kaman a kara tace ai gumbar shinkafa ne da kankana aka hade....

Nace oh Ammi akwai iya gyara tace ke fa su Ammi suna ji da ke ranar da naje Abuja ba yanda banyi ba suka ki su bani wannan din.....

Nace kindai san ba zaki hada son da Ammi ke mun da naki ba,tayi dariya tace ai ke yar gata ce jifa yanda Hajiya ke ta kai kawo duk da larabci muke magana....

Tace ban baki gist ba kedai wai kinsan Dangin Fa'iz akwai wata cousin dinsa da ita wai sonsa take?

Nace ki bari dan Allah bata san waye Falmata bane ko?Muka saka dariya tace ki barta ai tazo gidana ranar tana wani kaudi na taka mata birki shine taje take cewa ashe bani da kirki....

Mamanshi tace idan ta kara ganinta a gidan zata mata rashin muntunci nima wai sai gashi ana cemun dangin Shuwa masu larabcin karya....

Nace ai ke saukinki cousins dinsa ne ko?Tace eh da kanwarsa kinsan su biyu kadai aka haifa ita bata sona dai kanwar tasa.....

Nace oh ai ki fita iskansu kiyi kaman basa duniyar ma, ni kinga su Ramla ko kallo basu isheni ba sam manta nake anyi ruwansu a duniya....

Tace muyi gulma ne?Ga fa Ayaana can tana kula da Yaranta nace uhm ai Ayaanah da Yaya Abdul kawai a daura mu huta.....

Nayi dariya nace ai nima na kagu ayi na kara samun Yar uwa anan,ni ba friends ba bansan effect din rashin friends ba sai yanzu.....

Nan dai suka shigo ana ta hira har 2 na dare kafin kowa ya kwanta,da safe suna kenan shi dama an zana suna a masallaci.....

Nayi kwalliyana photographer yazo akayi pictures muna pictures sai ga Yayan ya shigo yasha Getzner dinsa sky blue da babban riga nima dama pitch lace na saka......

Ban gaishe shi ba shima bai mun magana ba mukayi pictures,Kausar tace ma photographer ya dawo anjima amma bara a kawo mashi abinci.....

Na tashi na hau sama,na mikawa Ammi Babyn na kwanta nace Ammi na gaji tace ai gajiya sai anjima....

Nan dai naci abinci na koshi muna ta hira nace wai Ammi da gaske gobe zaku tafi?Tace to dan ubanki zamu ta zama ne a gidan nan?

Nayi dariya nace ai zan zo bada jimawa ba nima na gaji da zaman Kano,tace kuma dai yanzu,sai gashi ya shigo suka gaisa da su Ammi....

Da naga Ammi na kallona ne nace masa ina kwana?Yace lafiya kalau ya jikin ki?Nace lafiya kalau.....

Ya jiya ya fita,can ya samu Yaya Abdulrauf shi kadai a chalet yace ina su Rashid ne?Yace Rashid ya fita yanzu shida Fateemah ko zasu karbo ma Khadijama wani abu....

Sai ga Sallama da sisiriyar muryarta,Ta shigo dauke da abinci ta ajiye a table ta durkusa ta gaishe su....

Yaya Abbaty yace au Ayaana shi yasa ban ganki a daki ba ina ta nemanki,tace to gani Yaya Abbaty Allah yasa dai lafiya.....

Yace lafiya kalau,ga wannan ya bata paper bag yace ki bama Khadijatu idan kin koma sama tace to shikenan an gama....

Ya ce to zanje na dawo,Yace au naga ma driver ya kai abinci hospital dazu ko Abbaty?

Yace eh nace a kai musu kafin walima anjima suma su san ana suna,Yaya Abdulrauf yace haka ake so.....

Yaya Abbaty ya tashi ya barsu,suna hiransu,tace naje na kaiwa Aunty Khady na dawo ko.....

Yace to je ki ina jiranki kinsan bazanci komai ba sai tare dake?Tayi murmushi tace ai har ka koya mun shan lipton gashi to 11 baka karya ba ina zuwa ta fita da dan gudunta.....

Ta shigo ina tsaye gaban mirror tace kai Aunty Khady kinyi kyau hakanan,nace a'ah bari kedai zan cire makeup dinne sai anjima......

Falmata tace ke meye ne a hannunki?Tace Yaya Abbaty ne ya bayar a kawo ma Aunt Khady gashi nabar ma Yaya Abdul shi kadai sai anjima.......

Ta juya ta tafi sukayi breakfast dinsu,suna ta hiransu,Su Ammi nacan wurin Hajiya Yanuwan Hajiya kab dinsu ba wanda baizo ba.....

Kausar nata hidima da Yanmatan sai ni da Falmata ne a dakin,na bude gift bag din na ga cards a ciki na dauko na ga wani box daban....

Na bude naga ring da Sarka na English Gold da initials dinmu AK,hmm!na bude card na farko naga sorry da words masu dadi,na biyu I love you....

Wow lallai na nunawa Falmata sarkar,na boye cards din mahaukaciyar Kausar ta shigo na nuna mata tace wow iyyeh Yayan naki dai ba dama.....

Ina ta smiling ni kadai,can da rana mai makeup tazo aka sake mun makeup nayi shirin walima,yanuwa da abokanan arziki duk sunzo.....

Na gama shiri ashe Kausar ta kirashi ayi pictures kuma mukayi pictures mukaje nan kasa akayi walima....

Ana kammalawa na shiga wanka,Babyn ma aka masa wanka,nazo na zauna na kara duba cards din naji dadi sosai.....

After Ishah dukanmu a gajiye muke har dai su Kausar da sukayi ta Up and down,nan muna hira nidai bacci yayi awon gaba dani.....

Da safe nayi wanka na shirya mukayi breakfast suka harhada kayansu nace haba Ammi dan Allah mana ku bari gobe....

Tace shi Abbu na Abuja fa ga Aysha du kadai sai Aunty Nafee ai yakamata mu koma hakanan kada ki damu zamu zo....

Nace to Ammi tace yauwa Falmata ku bani wuri zanyi magana da Andeeja,Na dawo kusa da ita kan couch na zauna...

Tace Andeeja nasan kw yarinyace mai hankali da sanin yakamata kada ki biye wa su Falmata,idan wuni kikayi kina breastfeeding ba abun da zai sami ke....

Sai kunya ya lullubeni,tace yauwa dan Allah ki kula da kanki ki kula da Hussain,bana son ki dinga take sani,Abbaty yana sonki kema kin sani.....

Kin samu surukuta ta gari dan Allah Andeeja kada ki bari muji ba dadi wallahi har kunya nake ji nazo gidannan saboda duk abunda yakamata uwa tayi Hajiya maryama tana maki shi.....

Y then would you be giving him hard time?Dan Allah ki dinga kamantawa koda Hajiya batai magana ba kema kinsan dole abun na ranta....

Amma ba wanda zai iya miki magana ki ji dan Allah?Nace Ammi kiyi hakuri wallahi tunda yayi magana na canja kema kingani ina breastfeeding sosai dama kwanakin can na rashin sabo ne nake jin zafi....

Wallahi na daina nasan dole abun dama kadan kadan zai daina,Ammi shine ya gaya miki?

Ammi tayi shiru tace eh ki daina miskilancin nan Andeeja ni a kullum ina jin dadi kina hannun kwarai sai ki bijiro da tsiya?

Nace kiyi hakuri Ammi na daina wallahi,tace to ki tabbata kin ba ma Abbaty hakuri bana son jin wani magana....

Nace to Ammi nayi promising insha Allah,Amma zanyi missing naku sosai,tayi murmushi tace kada ki damu ki dai ci gaba da kula da kanki kinsan yanzu kina bukatan gyara amma na tabbata ko a yanzu zai jiki zamzam.....

Na rufe ido ita Ammi ba ruwanta da kunya,muna ta hira har time din flight dinsu,nace Amma Ammi ita Matar Fa'iz da kun tura ta kaduna direct....

Aunt Falmata tazo zata kai mun duka Ammi ta hana tace Allah Falmata ki fita idona,Yar tawa to....

Suka tafi duk sai gidan ya mun shuru kaman ni kadai ba dadi,Kausar suna ta sallaman baki kwata kwata ranar tunda ya ma su Ammi sallama ban ganshi ba....

Duk sai naji ba dadi na rasa me yake mun dadi,Nace Kausar ina Abbaty ne kwana biyu?

Tayi murmushi au wato Abbaty bama Yaya ko?She furrowed her brows nace ba mijina bane?

Muka saka dariya Yaya Rashid da ke shigowa yace lallai masu miji,mukai dariya tace yana shigowa ai sai dai lokacin kina bacci....

Nace oh to na kwana biyu ban saka shi a ido bane Yaya Rashid,yace to kin daina leka ko parlour wai ke mai jego ko.....

Kausar tace harda fa wai kunyar su Hajiya da take ji ne kai Yaya R ka bar Andeeja kawai.....

Yaya Rashid nayi kewansa ne ban ganshi ba kwana biyu,Kawai sai gashi ya fado da sallamansa,na sha jinin jikina....

Shina bai kalleni ba ya je yaga Babyn a cikin Cradle Kausar na rocking dinshi while Yarta na cikin Vibrator...

Yace eh lallai ma Kausar ita wannan ce ake sakawa a vibrator dama Farha ce dana daga kafa....

Tace haba Yaya kai ma zaka bi layin matarka ne dan Allah?Yayi shiru yace oh ai ni ina yinta sosai amma a dinga saka mata hula akwai sanyi sanyi....

Tace to Yaya insha Allah,yace au Rashid na zata yau zaka tafi,yace bari Yaya gobe zanje yau din bacci yaci karfina.....

Yace you are lazy Rashid tafiya kwana biyu kawai da yanzu ka kusa dawowa,Rashid yace insha Allah goben dai Yaya Abbaty....

Bai cemun ba nima ban ce masa ba,ya gama zamanshi ya tafiyansa,Rashid yace wai Kausar kinga wani ikon Allah?

Tace haka suke kullum mu kawai
Suke damu da zancen missing wai su masu fada da juna.....

Yaya Rashid yace wai da gaske Kausar?Tace lallai Yay Rashid abun har Daddy da Hajiya sun ci masa mutunci shi kuma yasan laifin kanwarsa ne....

Nace Kausar da gaske Daddy ya masa magana?Tace kam ranar da kika dinga kukan nan wallahi a fusace Hajiya taje ta samu Daddy ta gaya mishi cikin daren nan aka kirawo Yaya Abbaty kai yabani tausayi....

Nace wayyo ni banji dadi ba,Yaya Rashid yace to ke Andeeja kiyi hakuri mana ku shirya tunda kinga abun yana damunki sosai....

Nace to Yaya zanyi bana son bacin ran Daddy da Hajiyana,yace to haka yafi Matar Yayanta.....

Da safe na shirya Kausar na hada ma Baby kayansa da aka wanke,Babyn was sleeping soundly beside me,tace ke Andeeja na kusa tafiya fa ni kaina abun na damuna....

Duka bazan kara sati ba,i smiled nace wallahi na kagu kuyi parking ku dawo Nigeria gaba daya nima zaman nan bana jin dadinsa ba kowa a kusa dani..

Tace chill sauranmu 1 year mu dawo gaba daya,amma dai zanyi missing naki,Farha yanda ta saba da gidannan bansan yanda zata yi ba can ba kowa sai mu kadai......

Nace to gashi kuma may be bakyanan zaayi auren Ayaana da Yaya Abdulrauf,tace ke haka ne fa gaskia da sake bari naje naji yaushe su Daddy zasu saka date din saboda if zasu taimaka su mayar nan da 1 month zan iya jira.......

Sai ga Hajiya da Daddy sun shigo,Muka gaishe shi yace to Zan tafi Abuja check up,ku kula da kanku da Hussain....

Nace to Daddy Allah ya kiyaye ya kaika lafiya,yaushe ne zaka dawo Daddy?Yace kwana biyu kawai wednesday kenan.....

Nace to Allah ya kara lafiya,Kausar tace ashe su Farha zasuyi missing mijinsu,Hajiya tace bari sai sunyi gashi kafin suce mijinsu ne......

Daddy yace haba Hajiya kina dai yin kishi ne,aka yi dariya,Rashid ya shigo yace Daddy a dawo lafiya.....

Daddy ya tafi,nace Yaya na zata kai zaka raka Daddy,yace no tare da Likita zasu tafi....

Nace au Dr din da zai masa check up din,ya kalla Kausar sai suka saka mun dariya,i frowned meye hakan?

Yace mijinki nake nifi Abbatyn naki tunda ba ki san waye likita a gidan ba,na daki kirji nace Yaya dashi fa kace yace eh mana.....

Na zare ido nayi sauri na tashi na fita waje ina bude kofar suna wucewa na rasa ya zanyi.....

Jamila tace Aunty kina son wani abun ne?Nace a'ah Jamila yauwa zo ki wanke mun bathroom dinnan dazu Hauwa ta wanke amma ki kara.....

Tace to Aunty bara na dauko,na hau sama duk zuciyana a cunkushe nan parlour naga su Kausar da Yaya Rashid suna kallo na zauna na yi tagumi.....

Yaya Rashid yace yau munga ta kanmu,ya dauki wayarsa ya kira yace Yaya kunyi sallama da Khadijama ne?

Bansan me yace masa ba yace ai kasan tun jiya bata jin dadi a kwance take alright to shikenan sai ankaita anjima....

Ya kalle ni nace haba Yaya meye na akeya kana so ya fasa tafiyan ne?Yace a'ah so nake dai ya kiraki duk naga kin damu......

Nace hmm!Nan dai wasa wasa ma zazzabi mai zafi ya rufeni,sai na kai kwance,Hajiya tace muje hospital nace a'ah ai naji sauki....

Yaya Suraj ya dubani ya bayar da magani aka aiko mun,yace duk missing mijin ne haka?

Nace Yaya Suraj ni wanne missing bana wani missing nasa kai ne dai kake missing Ayshatu zan sa a maido maka da ita ya saka dariya yace da na baki kujeran Makka kuwa.....

Nace ai kuwa bara na kira Abbu yanzu yanzu,yace to shikenan A shafa mun kan Abul khair,nace to yace wai Babyn nan yanzu shima gado yayi ko?

Nace gadon me Yaya Dr?Yace gadon suna shima sunansa sunkai 3 irin naki Daddy j,Abbul khair yanda Abbaty ke kiransa kenan,asalin sunansa da kuma Boy yanda Ayshe ke kiransa....

Nayi dariya nace ai duk kashe su zanyi kawai zaa dinga ce masa Abul khair din ina ga zaifi......

Yace anya dai saboda shi Yayanki yafi so ko?Nayi dariya nace Yaya Suraj Yayan nawa fa ma fushi yake dani ko magana baya mun....

Yace subhanallah anya Abbaty zai iya fushi dake kuwa?Nace eh mana ko sallama bai mun ba kuma tunda ya tafi bai mun waya ba.....

Yace to fa abun babba ne kenan,amma nasan Abbaty baya iya 10 good minutes baiyi maganan ki ba definetely yana can yana wahala shima ki kirashi mana ke Khadijama....

Nace to bana so na kira ya ki daga wayan kaga bazan ji dadi ba ai,yace ki gwada ai ana gwada sa'a amma wannan son da kauna da Abbaty ke miki bazai iya fishi me tsawo haka ba.....

Nace to nagode Yaya Dr zan maido maka Ayshatu,yace nagode amma dan Allah ki cire komai a ranki ki kuma sha magungunan nan nace to......

Ina kashe wayan na kira Yaya Abbaty bai daga ba na kara kira bai daga ba,duk sai raina ya kara baci na rasa abunda ke mun dadi ma.....

Nan dai Kausar ta dauke mun hankali muna ta hira nace nayi missing Asmah,Yaya Rashid yace wato bakiyi missing Fateenah ba?

Nace wannan masifaffiyar ya zanyi missing nata naka fi kowa murna da ta tafi,yace kinci sa'a dai yau bana jin fada muka yi dariya.....

Hajiya da ta taso daga bacci tazo ta zauna ana ta hira tace Kubra ya jikin naki?

Nace naji sauki Hajiya kaina kawai ke ciwo yanzu,Yaya Rashid yace duk fa ba wani ciwo Hajiya Daddy ne take missing....

Hajiya tace kasan ka kiyayeni ko Rashid idan ma tana missing Daddy ai da gaskiyanta gidan ai ba dadi idan Daddy baya nan....

Yace ni Hajiya Rashin Fateemah ne ke damuna,ta wurga masa throw pillow tace kinga mun mara kunya kawai....

Kausar tace wallahi Hajiya kawai a hada Yaya Abdulrauf da Yaya Rashid kowa ma ya huta,ya kuwa zama tuzuru ma ya kai mata dundu a baya....

Nidai ina kallonsu ina smiling,minti minti na duba wayana ko zai kira shiru,na kira Daddy na gaisheshi yace Daughter ya jikin naki?

Nace da sauki Daddy,yace to Allah ya kara baki lafiya gobe insha Allah zamu dawo morning flight ma zamu biyo saboda ina da meeting da rana.....

Nace Allah ya dawo mana da kai lafoya Daddy,muka gama magana na kashe,na kira Mamana mukayi magana na kira Ammi da su Falmata.....

The next morning na tashi nai wanka aka goya Abul khair sai na nemi guri na kwanta nayi bacci na can cikin bacci naji Muryan Daddy na zabura na mike sai gashi ya shigo....

Yace Daughter ya jikin?Nace da sauki sosai Daddy amma kunyi saurin dawowa yace eh wallahi ina da meeting 12 kinga its past 11.....

Bara na je ko sai na dawo naga Hussain ai ya kara zama babba nace kwana biyu kawai Daddy yace sosai kuwa,ita kum Farha gata ta makale mun mukayi dariya.....

Daddy ya tafi nace Jamila yunwa nake ji tace bara na kawo miki abinci,nace pepper soup zaki kawo man bana jin cin abinci......

Tace to ta kawo na zauna ina ci sai gashi ya shigo,na kalle shi nace ina wuni Yaya?

Yace lafiya ya jikin?Nace naji sauki sai kawai hawaye ya ciko mun a ido na dukar da kaina,yace yanzu meye ke damunki?

Nace bakomai na warware nasha magani,Kaman ulcer ne yake damuna,yace idan kika jama kanki ciwo ba ruwana yanzu kam,kina lacking wani abun ne da har zaki zauna da yunwa kinsan illar yunwa a wurin wanda ya haihu.....

Your body is elastic now you need to take care of your health amma naga ke baki da time din wannan sai kici gaba....

Nan hawaye ya dinga zubo man a ido,hannuna a cikin plate,ya tashi zai tafi na bishi da ido nan kuka yaci karfina wai me Yaya yake nifi daga magana shikenan bazan yi kishinsa ba....

Hmm!Shikenan insha Allah bazan kara damuwa da sha'aninsa ba,na ji motsin Kausar nayi sauri na shige bathroom,na yi zamana nasha kukana na goge hawaye na......

Nan ma na dauki wayana na goge numbersa na fito na samu Kausar tace ke Andeeja an tafi anyi ma Abul khair immunization fa.....

Yaya Abbaty na dawowa ya kaishi,amma kinga bai yi kuka ba kaman na farko,nace Ayya bawan Allah ai shi akwai hakuri idan ya tashi.....

Tace har da Yarki aka je tana can ta tsala ihu har ta gaji,nace yo ya akayi banji ba ko dai kinci mata Amana tace na isa inci ma Hajiyar Faisal Amana da ma Farha ce.....

I smiled tace ai ke kinfi kowa sa'ar suruka duniya Andeeja,nace kedai kya fada ai ni sai dai in godewa Allah.....

Amma kinsan me yake bani mamaki ne Kausar?Tace a'ah Mamana duk ta canja    tama fi son Abbatyn a kaina bansan me zan mata ba....

Tace wallahi kawai kiyi yanda take so ne ki daina bata masa rai to amma shi meye na gaya mata,nace kedai ina na sani shakuwansu ko yafi na Yaya Abdulrauf da ita kinsan dai yanda take dashi ko?

Kausar tace ki kwnatar da kai kawai ki daina barin ana samun matsala babba,kinga ni dana san Mahaifiyar Faisal ba wani sona take ba taka tsantsan nake da ita da kanta kuma yanzu ta sauko caring sai  na ture......

Nace hahaha ai dole ta soki Kausar ai ke akwai shiga rai,kuma mai girma Faizal wannan irin son da yake miki.....

Tace kya ji dashi naga Yayanki ya shigo kin soye ko Andeeja,nace ke ni fa tsoron Yayan nawa nakeyi bana so ya matso kada na kwasa,ta kwashe da dariya tace ai mantawa zakiyi can zamu ji anyi wani.....

Nace bada ni ba ke kaman zan mutu kyaleni kawai,muka ci gaba da hira muna dariya,Amma cikin rayuwana ina tuna abunda Yaya ya mun......

Wasa wasa har nayi three weeks da haihuwa,Ina kwance Abul khair na kan kirjina naji kamshin turarensa ina bude ido na ganshi....

Yace au dama ba bacci kike ba?Jikina har rawa yake,na dauke Abul na zauna nace ina kwana?Ya kalleni sama da kasa yace lafiya kalau.....

Ya jikin?Nace na samu sauki,ya miko hannu na mika mashi Dansa,na samu  Ya zauna bakin gadon,yana kallonsa yace kawai kin hana shi bacci.....

Bance komai ba ya yi masa wasa ya tashi zai fita nace Yaya sai kuma nayi shiru,ya ajiye shi cikin vibrator ya tashi yayi tafiyanshi.....

Na rasa yanda zan mashi,na tura masa text na bashi hakuri,ni bana jin dadin irin zaman nan,bayan na tura na kira yaki ya daga nima sai zuciyana ta hau nace to daga yau bazan kara kulashi ba tunda baya hakuri......

Can da dare ya shigo gidan ina dakin Kausar muna hira nida ita kadai,Ya shigo ta gaishe shi ko kallonsa banyi ba na mishi banza....

Yace Kausar ina kuka bar yaran ne?Tace suna parlour wurin su Daddy suk su Yaya Abdulrahman da Yaya Abdulrauf suna ciki ma.....

Yace to ku kadai kuka ki shiga kenan,Rashid fa?Tace ya fita fa tun dazu shida Yaya Zafar,yace ok...

Ya kalleni kaina a kasa ya fice,ya shiga parlour ya same su duka,Hajiya tace a'ah Abbaty sannu da zuwa...

Ya gaishe su ya mikawa Daddy ledae magani yace yanzu aka aiko dasu,Daddy yace nagode Abbaty gwanda da kazo muna maganar auren Abdulrauf ne.....

Yace to abun ya matso ne?Daddy yace eh nan da 3 months yakamata,Kausar taso ayi tana nan amma ba zamu takura su ba,Abbaty yace eh to Daddy hakanan din ma ai yayi......

Yaya Abdulrauf ya hararo Abbaty ya dunkule dariyarsa,Hajiya tace to yanzu Kausar ce zata harharda lefen kafin ta tafi.....

Tunda Khadijama ba tayi arba'in ba kuma bana jin zata ma iya zurga zirga dan naga jikin nata har yanzu sai a hankali.....

Abbaty kafin ya sani ma he swiftly say Meke damunta?Tace mun ba abunda yake damunta,dukansu har Daddy kowa ya hau dariya.....

Abdulrahman yace haba Abbaty baka barin halak dan kunya ne kai wai,sai lokacin ta fahimci abunda yayi,ya dukar da kai.....

Daddy yace a'ah ka tambaya mana ku barshi shi da kanwarsa,kai nan Abdulrauf ai kaima kasa hakurin kayi kace a maido auren baya,Hajiya tace Alhaji kai ne dai kake daure musu...

Yaya Abdulrahman yace ai Hajiya ki barsu kawai wadannan,yace yauwa jiya Gwaggo Shatu ta mun waya wai ayi hakuri dan Allah....

Nace mata kawai a ci gaba a haka kowa yafi jin dadin rayuwansa a haka,Daddy yace kayi daidai Abdulrahman kowa ya fita harkar su ne,duk na gane take takenta ni sai account number ma ne ta tura mun kawai.......

Abbaty yace oh sai hakuri ai abubuwan ba dadi,Allah ya kyauta dai,Daddy yace sai a ci gaba da Shirin auren,Gidajen nan na unguwansu Abbaty na baka daya kai Abdulrahman kaima Abdulrauf na baka daya so duk inda kuke so ku zauna is left to you.....

Hajiya tace zanfi so duk ku koma unguwa daya da yanuwanku kuyi zamanku kanku a hade,Abdulrahman da ba cika zama yayi ba kaga Abbaty na nan kuma akwai tsaro.....

Abbaty yace hakan ma zaifi duk inda mutum yaje hankalinsa zai kwanta sanin daya na nan....

Daddy yace har Rashid gidajen wasu na ta bayan Abbaty wasu na adjacent wasu na opposite so duk wanda aka zaba zan saka a karasa gobe sai kuje ku duba.....

Suka ce mungode sosai Daddy amma ka bari mu karasa da kanmu,Daddy yace a'ah Abdulrahman idan ban muku ba waye zan mawa dan Allah ku bari na muku kawai......

Yace kuma ai kuna dawainiya dani in one way or the other Allah yayi muku albarka,suka ce Ameen....

Nace ke ni Kausar na gaji da zaman nan wai haka mutum zai ta zama ba fita kaman kurkuku ina so nayi tafiya ne .....

Tace lallai ma Abbaty wannan kallon da yake miki ko ina bazai bari ki tafi ba ina tabbatar miki da hakan......

Haka muka ci gaba zai shigo ya duba yaronsa ya tafi,baya mun waya wata rana da tsakiyar dare hakanan na kasa bacci ciwon ciki sosai yake damuna....

Abun yaci tura dole aka taso Hajiya ta mashi waya,yace yana hospital suzo dani kawai muka antaya sai hospital.....

Nan aka saka mun drips da injections sai bacci lokacin ne pain din yayi subsiding nasha wahala.....

Kukan Abul khair ya tashe ni,naga Kausar tana jijjiga shi Jamila na goye da Hajajjun Kausar sai Hajiya da take zaune kan kujera.....

Nace Hajiya me ysa baki tafi gida bane?Tace ina zan fa tafi na barki a anan baki farka ba,nayi murmushi dakyar da taimakon Hajiya na zauna nace naji sauki Hajiya ki je ki samu bacci.....

Tace cikin ya daina ciwo?Nace eh dama nan ne na taba gefen cikin tace Allah yasa ba amosanin ciki bane bari naje gida zan aiko Innah da maganin gargajiya kisha koma meye zai daina amma Kausar kada ku bari Abbaty ya gani kinsan shi baya son gargajiya.....

Nace nagode Hajiya tafi tinda anyi sallah asuba,Can sai ga Innah da Rashid suka bani Innah ta saka nasha tasteless  wai sassaken Magarya ne da jan kanwa....

Ina sha bayan few minutes sai naji wurin ya daina zafi da radadin da nakeji,koda Abbatyn ya shigo nayi sauri na rufe idona,yana taba gefen cikina na saka ihu.....

Ya harareni ya juya ya ce Kausar zanje nayi wanka gida na dawo,tace to Yaya sai ka dawo......

Rashid yazo da Breakfast nan ya koma da Innah su Hajiya da Daddy suka dawo can Drs suka shigo suka dubani suka ce naji sauki amma suna so su barni under observation for 24 hours Daddy yace ai ba damuwa......

Su Drs dinnan suna ta tururuwa zuwa dubani ashe yana nan a waje shigowa ne baiyi ba,bayan wurin Yayi shiru ya shigo......

Yana waya raina a bace Jamila dama taje ta zagaya da Hajjaju ita kuma Kausar Faisal ya kirata tace ba network tana goye da Abul ta fita.......

Ya matso dap dani ya kama hannuna ya matse na saki kara,yace ban gaya miki ki kula da health dinki ba kinsan ciwon nan yana da hadari ko?

Kawai an gaya miki sai ka daina cin abinci ka abri ulcer ta maka yawa,nace ai kai ne ka janyo min ita,.....

Ya cika mun hannu yace ni na janyo?Ko kallon kirki kina mun ne?Nace ai kana da wacce zata maka na Khadijatu ba wani abun damuwa bane....

Ya numfasa ya zauna yace wai ke wanne irin kishi ne dake haka?Na dukar da kaina hawaye na zubo mun nace ka taba ganin matar da bata kishin mijinta?

Yace kalleni Khadijatu,na mishi banza ai sai yayi yelling yace look at me ba shiri jikina na shakin na daga ido na kalleshi,duk a tsorace nake......

Yace ni na saka miki ulcer?Na daga kai alamar eh,yace na cene kada ki ci abinci?Na ce a'ah.....

Kawai hawayen nawa kaman an karo su sai ya saka yatsansa ya share mun hawaye,ya matso fuskarsa kusa da tawa yasan abun da ke sakani loosing control jin numfashinsa a fuskana.......

Yayi joining lips dinmu ya fara kissing dina ina protesting amma ina yafi ni karfi,sai akai knocking kofar,yayi brazing kansa yace come in....

Sai ga Dr Asiya da Dr Fateemah,sai ya janyo ni ya dora kaina a kirjinsa,haka suka same mu suka mun ya jiki suka tafi.....

Gaba daya ya kashe mun jiki yace Khadijatu ina sonki so mai tsanani ina kaunarki bazan iya son wata Ya macce ba bayan ke,i really love you stop misunderstanding me......

Ke kinsan ko zan nemi macce badai Dr ba a hospital da nake i had a bitter experience ni da nake da Sarautar mata me zanyi da wasu matan?

Nace dadin baki kake mun nan naji kana waya da ita ai,yace na zata tana so taji ya jikinki ne tunda na fahimci inda ta saka gaba na yakice ta da wuri amma ke nan kikayi punishing dina Khadijatu.....

Kinga irin wannan abun zai ita sa na nemi wata din,nan take zuciyana ta harba nayi lamo a sume a jikinsa sai fadin innalillahi yake.........

Suraj ya shigo kenan jin ance bani da laifiya,yace Abbaty meye ne?Yace ta suma ne taimaka Suraj.......

💞💞💞💞FOREVER YOURS 💞💞💞💞💞💞💞AYSHSAMIRA💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Read,vote and comment thank you............

Continue Reading

You'll Also Like

414K 30K 41
ပဲပြုတ်သည်ငပြူးနဲ့ ဆိုက်ကားဆရာငလူးတို့ရဲ့ story လေးတစ်ပုဒ်
38.9K 4.4K 26
It all comes down to LOVE and SACRIFICE. Follow me on this voyage and I guarantee you'll find it fascinating. Note: The pictures you will see here a...
Ice Cold By m

General Fiction

2.2M 83K 49
[boyxboy] Wren Ridley is always two steps ahead of everyone, or so he thinks. His life seems out of his control when he starts having feelings for so...
1.4M 45K 30
Grace Cooper is a fighting girl. She lived with her brothers Grayson and Ace. Her mother worked day and night but spent her money on drinking. She s...