FOREVER YOURS

By Ayshasamira

54K 3.4K 1.3K

Khadijama Is half Shuwa Arab,a Gentle and simple lady in her mid twenties,follow us as we peak through the li... More

Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 34
Chapter 35

Chapter 33

1.6K 80 46
By Ayshasamira

💞💞💞💞FOREVER YOURS 💞💞💞💞By AyshaSamira
Chapter 33..
Wattpad@Ayshasamira
Twitter @Scarlet_Samie....

Na gama ANC kenan sai naje office din Yayana baya nan dama ya bar mun key din,na bude na shiga na zauna na dauko laptop dinsa ina kallo....

Nan Dr Shu'aib ya shigo muna ta hira yace wai gaskia Gentle ranar da zaki haihu ina ganin duka jamaan da ke hospital dinnan zasu taru....

Nayi dariya nace kaji Shu'aib saboda Yayana ne CMD ko,mukayi dariya yace to duk inda Yayanki ya tsaya ko meeting ake yo yaga timw ya tafi yanzu zai ce mana matanshi ta kusa haihuwa zai tafi....

Muka saka dariya nace wai Shu'aib harda kai ake teasing mijina ko,nace yauwa Shu'aib albishirinka kuwa,yace goro nace ina Ruth?

Yace wacce Ruth kuma Gentle?Nace Ruth mana ta FGC Zaria sai ya bude baki yana kallona ina kika ga Ruth Kekam?

Nace nan ina strolling na fito gida sai kuwa naji an kwala mun kira a mamaki na naga Ruthy mun jima muna hira har munyi exchanging number ma.....

Kai dan Allah wai tana nan,Allah sarki har cewa tayi idan na yarda zan aureta zata musulunta,na zare ido nace kai Shu'aib kuma kaki kayi wannan jihadi sai ya kwashe da dariya.....

Yace ke dinnan ko,wai baki san akwai wata da nake so bane kawai auren ne baya gabana yanzu amma tunda ga Abbaty zai zama Baba ai dole in tashi tsaye na yi aure.......

Muna ta hira har Abbatyn ya shigo ya same mu,na jima a office din tukunna ya mun wayo ya saka ni zagaye hospital da sunan yana neman wasu ai kuwa ina ta mita......

Muka koma gida kadan kadan nake jin nakuda amma ban mayar da kai sosai ba ni duk wannan abun ma da Abbaty keyi gida nake so na haihu......

Da safe nace Kausar tazo ta tayani hira bana jin fita yau,tace me yasa kodai zobon nan na Hajiya marasa sugar kike gudu,Nace a'ah na isa kawai nauhin jikina nakeji....

Tace man Hajiya bata jin dadi ma nazo na dubata mana ashe karya take mun so take kawai naje gidan.......

Na kirashi yace to ba damuwa Rashid baya nan amma Excellency ta mun afuwa bara na turo driver din Hajiyan.....

Tare da su Jamila muka tafi,Nan na sa aka hada masa lunch dinsa na aika driver ya kai masa,haka nan Innah ta aiko da zobon nan raina duk a bace ina ganinsa saboda nan zai dinga sakani yawan fitsari kuma zaki yana ta fita.....

Amma na ranar kaman yafi yawa tun dai ina daure pains din,da yamma naje strolling ni da Jamila kenan ai kuwa cikina ya fara wani irin juyi na tsugunna a kasa....

Sai da Na ma Kausar waya ta turo driver muka koma,Kausar nata mun tsiya wai bari Doctor yazo a ga yanda zan shagwabe masa.....

Yana zuwa muka koma gida,na kwantar da kaina a jikinsa nace Yayana na kagu na haihu na kwanta a jikinka....

Yace hmm!Ai Baby ni abubuwan da yawa fa na kagu nima wallahi dan hug dinnan like ki bari kawai i really want to cuddle up with you.....

He was just looking at my protruded tommy,Yaya wallahi kicking dinnan ka gani ba he saw the traces of the kick irin ba sauki......

He was noticing ne i wasnt my normal self,aftwr minutes na shiga toilet wannan zakin nan da na sani bansha zobon Hajiya marasa sugar ba...

Baby ya kike ji ne tell me,bakomai Yaya kicking dinnan ne,Ya girgiza kai yace kizo muje hospital kina Labour ne.....

Na zaro ido nace nifa Yaya ba wani labour da nake haba bazan je wani hospital ba,yayi shiru ya kyaleni sai da na dawo idan zanje bayi sai na rike bango......

Dakyar na cije lebe na ce Yayana na rike kunkuru da hannu daya ya taso a rikice yace Babyna menene?

Ya rikeni ya zaunar dani yace kin yarda Labour kikeyi ko tun dazu da na ganki gida nasan labour kikeyi to bana iya tilasta miki......

Ya je ya dauko hospital bag din da na hada tun ciki na 7months,ya ce in tashi mu tafi,Nace Yaya ka barni na huta bazan iya dagawa ba daga zaman nan.....

Yace haba Baby bansan ki da raki ba ya kira Jamila ta dauki kayan ya kamani ya sakani mota yace ta shirya Driver zaizo ya kaisu gida......

Tana ta mun sannu har bana iy amsawa gumi nake ta yi duk AC dinda ya kunna baya mun na cakumo hannunsa na rike gam,yace Baby ki dinga Addu'a kinji....

Ina nishi sama sama,nace Yayana mutuwa zanyi na shiga 3,yana driving yana kalloni duk a rikice Yake......

Yama kasa daga waya ya kira kowa to na rike masa hannu dayan yana driving,yana ta mun sannu.....

Muna sauka hospital aka kawo wheelchair ya tayani zama ya tura ni da kansa,sai Labour room.....

Muna shiga nurses suka kwantar dani yace daya taje ta kira Dr Fateema ita kadai,tace to.....

Taje tace Dr Fateemah bata nan sai dai Dr Asiya yace a kirata ta gaya mata matanshi ke labour shi badan rules din ba  ai bazai yarda ba......

Nan wayana dake ajiye parlour na ta fara ruri Jamila na dauka taji Kausar ce tace Aunty Kausar ai Aunty Khady nakuda takeyi sun tafi hospital nan Kausar ta buga salati take gaya wa Hajiya.....

Hajiya tace yo shi Abbatyn meya hanashi kira mtsww ta kira driver tace a aje a taho da su Jamila,Kausar dama ita tace dole a bar Asmah ta kwana mata ta tashe su daga bacci Asmah tace Asmah Baby ta kareki kafin ta fito ky muje hospital din.......

Fateemah tace wai naso dai naga Fuskar Yaya Andeeja kafin ta shige da na mata hoto nasha dariya nan dazu take mana kuri ita matar likita ce ko....

Suka saka dariya Asmah ta dauko ma Kausar Yar Babynta suka fito har da Daddy aka shiga mota biyu sai hospital.....

Aka ce ai private labour room aka kai Khadijama,dama Suraj yana on call so Nurse ta gaya masa Abbaty ya kawo matarsa,nan dai baya da halin shiga kuma Abbatyn yaki fitowa da shi ake labour......

Duk su Dr Shu'aib da Zaid suna zaune a corridor din,dole dai Dr Fateemah aka mata waya tazo,tace wai duk kuna nan a zaune ta rusuna ta gaishe dasu Hajiya.....

Kausar tace wai ki koro mana Yayan to ya abri taji da abu daya tayi murmushi kasa kasa kada Hajiya taji tace ai Kausar in gaya miki ko ANC aka zo Abbaty baya barin Matarsa yau akwai masifa ai dan ko me zamuyi ba zamuyi masa daidai ba....

Kausar tace gaskia yau kuna da aiki,Allah dai ya raba lafiya yasa ta haihu da kanta tace Ameen

Ta shiga tace Dr AT duk su Hajiya har Daddy suna waje ba zaka je ki gaisa ba?

Yace na bar Baby ita kadai a'a bazanje ba ya kara pecking dina in juya kai nan in juya nan duk gashina ya yakuce duk na cije lebana,after almost 30 minutes, tace to Dr AT tunda gani sai kaje su Suraj duk suna nan fa,patients gar tambaya suke matar Gwamna ce saboda cikar da akayi a wajen nan.....

Yana rike gam da hannuna yana caressing forehead dina ina ta addu'a can sai na yi ihu yace ni Dr Fatee ai bazan iya barin Khdijatu it kadai ba da ina da hali dana cire ciwon na maido a jikina wai sannu Baby......

Dr Asiya ta kalla Dr Fatee suka kwashe da dariya suka ce lallaina Suraj wasa ne haihuwa yazo gun Dr AT yanzu Dr namiji ko daya ba zaka bari ga shigo ba yace ina Dr Asiya daina wannan magana nidai ku mata a hankali.....

Sannu Baby sannu yayi pecking dina can ya goge man gumi can ya shafa gashi na can ya shafa fuskana haka yayi tayi yama fini fita hayyacinsa....

Nace Yaya ni bazan iya ba wayyo Yayana,yace kin gani ko Dr Fatee bari a yi mata CS ina ga zaifi sauki idan ba zata iya ba hour daya Babyna tana wahala i cant take it magana yake jikinsa na bari.....

Nan dai ake ta abu daya tun 2am har 4am,Dr Fatee ta saka hannu taji yakai 9CM to nan fa aka shirya komai na tarbon Baby aka matso da kayan aiki yace kiyi a hankali fa Dr Asiya dan Allah kada ku ji mata ciwo suka kwashe da dariya suka ci gaba....

Ai kuwa Dr Fatee tana dafa cikin nace wash,yace Fatee kiyi a hankali mana haba kina ji mata ciwo fa....

Tace sorry Sir ta kara nace wash Yayana na kara rike hannunsa gam,yace Fateemah idan ba zaki yi mata a hankali ba ki fita a kira wata....

Tana gintse dariyanta tace Sorry Sir wallahi a hankali nakeyi kaga gesture din hannuna,ya kara rungumo kaina yace sorry Baby we are almost there....

Suma Sorry din suke ta fada can tace push,kaman shi ke pushing yana hura mun iska na fara pushing hawaye na zuba daga idona shim kaman zaiyi kukan.....

Tace hold it nan sai na fara kuka shim hawayen ne a idonsa yace Babyna ki daina kuka kinji Dr Asiya da Dr Fatee are the best Gynae Dr's a kano nace uhum tana kara cewa push ai kuwa push din da zanyi sai na suma sai ga kukan Baby.....

Ya yi sujudush shukur tukunna ya dawo yace Baby bude idonki sannu,nan dai dama suka janyo placenta suka gyarani aka kwashe jini na samu kari kadan.....

Yace Dr Fatee bata tashi bafa,tace suma tayi ne Dr ta canja mun drip ta kawo ruwa zata shafa mun a fuska ya karba da sauri ya shafa mun.....

Yana ta kwala mun kira Dr Asiya tace she is weak ne Dr AT zata tashi aka saka wasu injection a drip din,Nurse ta karasa goge Bouncing Baby boy din ta miko masa shi duk hannunsa na a jikina ....

Yace wai ya karba yayi masa addu'a ya ce bawan Allah sak Khadijana,yace Ki kai musu shi a waje su Suraj bari na samu Babyna ta farka.....

Ta karba Babyn tace gaskia Dr AT kana tsananin son matarka ina ganin duk hospital dinnan ba mai son matarsa kaman kai Allah ya barku tare ta juya ta fita.....

Dr Fateema da ta gama wanke hannunta tace Ameen gaskia Dr AT dole suk macce ta haukace a kanka wai wannan soyayya haka....

Dr Asiya tayi dariya tace ai baki san soyayya ba wallahi ce nake De AT ne ke labour duk a rikice ya shigo wurin nan....

Yace hmm!Nan sai nayi ajiyan zuciya na riko hannunsa nace Yayana,na bude ido na juyo na kallesa nace wai ashe ba mafarki nakeyi ba?

Ya yi murmushi ya daga kansa yace eh you are not dreaming Baby,me ke miki ciwo ne?Nace komai ma ciwo yake mun Yayana.....

Dr Fatee tazo ta cire drip tace to ki zo ki watsa ruwa zaki samu relief muje na taimaka miki kinji matar Dr sannu....

Nace to,ta kamani shima yana rike da hannuna tayi murmushi tace Dr AT zan tayata komai kada ka damu,yace no ki bari zan mata ai nima Dr ne ko?

Tace to ya bude jakata ya ciro duk abunda zan bukata muka shiga tare ya mun wanka dan duk jikina yayi weak,nace Yaya wallahi ciwo nakeji koina har cikina yace sannu zai daina kinji?

Nace to ya goge mun jiki sosai ya sakamun kaya ya saka mun pad ya bani na saka,dama turban na dauko ya saka mun ya dauko ni kaman yar Baby,dama sun ajiye stretcher yana fitowa suka tafa suka ce lallai yau munga love....

Ashe haka Dr AT kake lallai kana tsananin son matarka ya dorani kan stretcher yace ai kune kuka bata wahala har haka musamman ke Dr Asiya haba tayi dariya tace tuba nake DR amma a gunka na koyi aikin....

Kawai dan tana matanka ne kake ganin kaman banyi daidai ba amma a mun afuwa dan Allah,yace bakomai nagode....

Dr Fatee ta mayar mun da drip din suka ce to kaga su Daddy na nan bari mu da kanmu mu tura ta zuwa ward room din nan VIP....

Yace to suka turani aka fito tare dashi shi ya dauko Baby bag din,nan ya samu su Daddy da Hajiya duka Drs dake hospital that night suna gurin....

Ya gaishe dasu Daddy suka masa murna,Hajiya na rike da Babyn kowa wurin Yayi congratulating nasa,su Kausar suka fara wucewa room din tana shigowa Dr Fatee na hadamun Tea mai kauri...

Tace lah Dr Fatee ga kayan tea din ai tace ai baki sani ba Kausar tun dazu da Yamma Dr AT ya hada dakin nan ya ajiye komai da Khadijatu zata bukata ki kalla ki gani,sai lokacin Kausar ta juya taga inda yasa welcome Baby girl thank you Khadijama....

Ta duba taga Kayan tea madara family size peak da Three crown,milo ma ga Sugar ga bournvita ovaltine,Bread tace motan bakery ma ta kawo masa....

Kausar ta jinina tace lallai Yaya Abbaty,na kalle ta nace Kausar bana son munafunci.Dr Asiya ta saka dariya tace kanwar mijin Matar Dr....

Dr Fatee tace ai kinsan Cousins ne ko?Dr Asiya tace ke haka fa na manta ne dole suna bama Kausar labarin abunda tayi a labour room ni kaina sai da na yi dariya.....

Nan su Hajiya da Daddy suka shigo na karasa shan tea din nama kwanta,su Dr's ma suka shigo suka gaisheni suka fita...

Fateemah tace Aunty Kausar kice ne Hajiya sujw gida su huta kafin anjima,Kausar tace to Daddy kunga jika ai kuje ku huta kafin mu dawo anjima....

Daddy yace hakane sannu Khadija nace yauwa ai banajin komai Daddy yace to Hajiya muje gidan,suka tafi suka barmu.....

Fatee na mun dariya wai yanda Yaya Abbaty ya rikice yaki ya fito daga labour room,nace wallahi ni da ke ne...

Sai da ya dawo sallah ya shigo,Yana shigowa tayi shiru,ya zauna a kusa dani yayi wanka ya canja kaya bakinsa baya rufuwa....

Fateemah tace Yaya Abbaty har yanzu matarka batace ina Babynta ba ko kallonsa bata yi ba na harareta....

Na lankwasa murya irin na marasa lafiya nace Yayana na gaji sosai duka jikina ciwo yake mun,na tabe baki....

Yace Allah sarki sannu Babyna sorry ya dora kaina a laps dinsa yana shafa fuskana yace kyale Fateemah ki samu bacci ai Babyn ma bacci yakeyi ......

Ya kalla Asmah yace kada ki bari Kausar ta bata ki kinsan Khadijatu tayi kokari sai ta huta zata iya daukan yaron....

Na mata gwalo Kausar ta ce hmm!Ai ni i am flabbergasted wallahi,Fateemah kina ganin yarinyar nan ba hira mukeyi ba yanzu amma kinji muryanta.....

Yace kin gani ko Asmah zata kara ma Babyna sharri haka Kausar take ai,suka saka dariya yace suyi shiru bacci zanyi...

Asmah na rungume da Babyn Kausar ita Kausar ta dora nawa Babyn a Baby bed yana baccinsa bayan yasha Zamzam......

Ya duka a kunne na yana gaya mun soothing words har bacci ya daukeni,Ina nan kan laps dinsa har gari ya waye kusan past 8 na bude ido na ganshi can kusa da Kausar rungume da
Baby....

Lokacin ne ya zo kusa dani da murmushinsa nace ina su Kausar yace tana nan waje tare da matar Abdulrahman nace ina Fateemah ita Asmah sai tai bacci....

Yayi murmushi yace suna nan waje na kira su ne?Nace  yaushe zamu tafi gida bed dinnan ba dadi,yayi murmushi yace to Baby rai bace kika tashi sannu...

Ga Babynmu,na rufe fuska,na karba Babyn ina kallonsa sosai,ya rungumo mu tare yace Allah sarki Baby sannu da kokari nagode sosai Allah yayi miki albarka,Allah ya raya Hussain(Daddy)na kallesa nace da gaske?

Yace eh sunansa kenan nama kira su Ammi sai hawayen farin ciki suka kamani na goge hawayen nace nagode sosai Yaya Abbaty i am grateful.....

He patted my shoulders stop crying my Baby it will tear my heart apart,stop it mana,let mw show you how to breastfeed him....

Yayana nifa bana so zanji zafi ne,Ba zaki ji ba i am here,i pouted he lifted my top and started he was holding it and the baby was sucking.....

His whole attention was with what he was doing,while i was feeling pains,i swiftly pushed his hand na mayar da bra dina....

He pushed his mouth menene?Yaya wallahi zafi kaman nayi kuka he stood up to Khadijatu ga breakfast a zuba miki nace eh....

Kausar ta shigo tace au Matar Yayanta kin tashi sannu,ta zuba abinci tace to gashi a ci abinci harda kunu aka aiko....

Na harareta nace uhm nidai ina wayana na kira Yaya Rashid,yace wayanki na gida ga Ammi kuyi magana...

Nace ta kira ne?Kunya nakeji bazan iya ba he smiled Ammi eh ta tashi gata,na karba a kunyace nake magana tace ke kiksa sani tunda bakya son magana dani zanzo ne ai.....

Nace to na kashe ya kira Aysha mukai magana Dr Fa'iz ma ya kira nace Yaya Abbaty ka kira mun Yaya Rashid mana ya harareni yace yana hanya ko na kira ba zata shiga ba sorry Baby.....

Kausar na gama waya ta miki man wai ga Faizal,na karba ya gama mun tsiya wai yanzu sai na sako masa matarsa ta koma......

Su Dr Fatee suka kara shigowa muka gaisa suka dubani Dr Asiya tace wai Dr AT tun dazu baka daga daga inda kake ba ya za'ayi ta huta to....

Yace oh tafi hutawa idan ina nan ai kusa da ita sukayi dariya,tace to Allah ya bani miji mai irin halayyarka ai ba Kausar ba har Asmah dake bacci sai da ta zaburo ta tashi....

Shima Abbatyn murmushi kawai yayi na kalleta naga irin kallon da take masa nan kawai nayi frowning face dina,na kalle shi.....

Na kalla Dr Fatee nace yaushe za'ayi discharging nawa na gaji sosai,tace yi hakuri Matar Dr AT hospital din namu baya so ki tafi....

Tayi murmushi nace haba dai ai ni bana son zama hospital dinne,Kausar tace ai nan ne gidanku sukayi dariya..........

I pouted Dr Fateemah,tace au i like the way kike cewa Fateemah wallahi  dama kowa haka yake kirana kaman wata balarabiya....

I smiled tace komai naki is interesting matar Dr AT,nayi murmushi nace Dr Fateemah mana na tura baki tace dole Dr AT ya dinga rikicewa.....

Yace to kin gani dai Fateemah shi yasa ko fita bana sonyi,sukayi dariya tace nan da two hours za'ayi discharging naki nace to.....

Kausar ta zuba masu abinci suka zauna suna ci saboda wannan Dr Asiyar nace mai zan kwanta ya ba Asmah Babyn ta saka a craddle na kwanta a laps dinsa.....

Suna hiransu ina jinsu na rufe idona wai bacci nake yi bayan sun gama ci sun fita ne can cikin bacci naji muryar Dr Suraj......

Na bude ido na ganshi a zaune yana cewa au Abbaty duk hospital yau labarinka akeyi yau matan hospital dinnan masu son halinka ai da yawa ne wannan soyayya kawai ake fada da kake ma kanwarmu......

Yace ai kaima haka kayi Suraj sukai dariya na tashi zaune nace Yaya Dr ina kwana,yace uhm sarkin shagwaba an tashi na kalla Yaya Abbaty nace na tashi dan Allah ku barni naje gidanmu na gaji......

Suraj yace ai nasan kin kagu yau gaki ga Hajiya,nan sai Abbaty ya zabura yace wai wanne gida hmm!Yau ke da Hajiya zamu sha fada daku yau kam....

Nida Suraj were giggling,Kausar tace ikon Allah ina zata je ne Yaya,yace ai dama kece zaki saka baki ko....

Suraj yace ina ruwan sarkin soyayya lallai Khadijan Abbanta nidai wallahi kuna bani sha'awa.....

Nace Yaya Dr kenan ai kaima haka kuke kai da Ayshanka,muna ta hira sai ga Yaya Abdulrahman ya shigo nai sauri na bar jikinsa,Suraj yace au ashe kuna da sauran kunya mukayi dariya.....

Yaya Abdulrahman yana tafiya aka sallamani,Ana hada kaya sai ga Hajiya da kanta tazo ta tasani a gaba ta sakani mota tace nasan halin Yayan naki yanzu zai ce gidanku zaki koma to bazan yarda ba......

Ya riko ni Hajiya na rike da Baby kta dai tana gaba muna baya,ai fa yan hospital nurses da Dr's suka rako mu har da cleaners...

Dr Shu'aib ya bude mun mota na shiga Yaya Abbat ya ce da Hajiya bata nan da daukoki zanyi har mota bance komai ba na kyaleshi.....

Muka shiga driver ya ja mu shi ya dauko su Kausar muka hadu gida,Muna parking yana parking yana rike da hannuna ina tafiya a hankali har sama......

Na zauna a parlour Hajiya tace sannu Kubra kinyi kokari ai ita waccan sarkin raki ai kin fita kokari,Kausar tayi dariya  tace nafi Kubra raki Hajiya tace eh......

Yana ta kallona yace Hajiya ya kamata ya samu breastmilk ko,tace haka fa da yake bacci yake bari na saka shi a craddle,kubra zo muje daki ki ci abinvi ki kwanta......

Nace to ina so na kara yin wanka ne tace ai dole na hada ruwan wanka kinsan wankan jego zakiyi an hada komai......

Inna tazo ta kai mun ruwan sai tafarfasa suke nace na shiga 3 yau,tace yi hakuri uwar dakina ga kunu nan kuma sai ki dora,nace Innah ni wallahi wai na koshi fa naci abincin nan....

Tace kinsan bana so mikiya ta kamaki ko Amosanin ciki,kinji?I pouted to Innah na fara wankan ne tace a'ah zaki sha kunun sai ki shiga wankan zan tayaki ma gasa jikin ne.....

Wayyo ni,tace ai ba sosai bane kinsan Dr yace kada a miki wannan wankan biki din ai kinga Kausar ma bata yi ba.....

Hajiya ta shigo tace kadan ne fa Kubra kinji kinsan yanzu jikinki danye ne you need strength,I smiled to Hajiya....

Nafi hour ina wankan nan naji dadin ruwan sosai,Innah ta tausa mun ta fita nan na sha wanka na ina jin motsin Yaya Abbaty na shareshi ni kunyar ma Hajiyana nake ji......

Na fito na tarar da Kausar na jijjiga Babyn,na zo na zauna nace ke naji dadin wankan nan wai na dauko drier na yi drying kaina,na shafa mai na saka kaya......

Kausar tace to ga Boy na jin yunwa,nace ke ni bana son breastfeeding wallahi kinga idan yaja zafi,tayi tsaki tace kindai san sunan Daddy ne kiyi a hankali nace au to na karba nace ya zanyi.....

Tana dariya tace au Dr din bai koya miki ba?Nace ke kika sani nidai ya koya mun yana ta tsotso ina ihu,tace oh haka Yayana ke hakuri da rakin nan naki?

Nace ke ni bacci nake ji sosai kuma tace ai ki bashi yasha naje na kwantar dashi sai kiyi bacci sannu kinma yi kokari fa,nace ke naga ya kara haske,tace eh an masa wanka ne ke ko ya darzu mukai dariya........

Na samu yana sha yai bacci na bata ta kwantar dashi na kwanta a gefenshi wai yaji dumin jikina,nan fa bacci mai nauyin gaske ya daukeni,bansan wanda ya dauka Babyn ba na bude ido naga baya nan na kara juyawa na ci gaba......

Can naji Hajiya nacewa wallahi Abbaty idan ka tashe ta ni da kaine kai ba likita bane baka fi kowa sanin tana son hutu ba?

Na bude ido na tashi naje na canja pad na dawo na zauna Hajiya ta shigo rungume da Babyn tace au kin tashi sannu Kubra....

Tace yauwa ga wayanki,ana ta kiranki,na karba na duba su Falmata su Aunt Yagana na ki kirasu suka mun congrats.....

Ammi ta kira ta bani mijinta,Yaya Abdulrauf ya shigo yace masha Allah kuce ne balarabe aka haifo mana na zata skin din Abbaty zan gani na saka dariya......

Yace ashe nima ina da rabon haihuwan balarabe,nan su Amra suka rugo suka rungumeshi duk suka bani tausayi.....

Suka ce Daddy kaga sabon Babyn mu,yace eh na gani nace nifa tunda na dawo hospital baku zo kun gaisheni ba.....

Suka zo suka gaisheni,duk sun canja yace da basa gaishe da mutane,nace to Yaya Abdul suna gidan nan ai Hahiya ba zata bari su koyi mugun hali ba.....

Yace au Ayyana ma ta kira tace wayanki baya zuwa,nace kaji munafuncin Ayyana ba zata kira Kausar ko Fatee. Ko Asma ba?

Yace eh lallai Khadijama kindai san yanzu ta zama Yayarki ko na turo baki nace shikenan Yaya.....

Abdulrahman ma ya shigo muna ta hira nace ni ina kewar Yaya Rashid na dauki waya nata kira baya shiga....

Kausar ta shigo tace Amra kuje ga abinci can na zuba muku suka ce to suka fita,ta zauna tace guess what Andee?

Nace menene Kausar bana iya guessing sai kuwa ga Yaya Rashid da katuwar akwatinsa ya leko nace Yaya Rashid dina oh i am so glad you are back....

Yace have i been missed?I pouted sosai ma,ya kalla Yaya Abdulrahman ya hango Baby ya saki akwatin ya yi sauri ya karba yace Yaya Abdulrahman baka ce mun balarabe aka haifo ba...

Yace to ai nadai yi kokari da ni na fara gaya maka an haihu ko sai ka bani giron albishir da kayi niyya....

Ya ciro zan baka mana Yaya dolena,Abbaty na shigowa na daurw fuska Kausar ta kwashe da dariya tace Yayan naki kuma......

Nace kyaleni dan Allah bana so,i pouted yazo ya zauna kusa dani,Baby an tashi he whispered i ignored him...

Me nayi ne?na tura baki na ci gaba da magana da Yaya Rashid ashe Yaya Abdulrahman ya na kula da mu ya girgiza kansa.....

Su Aunty Maryam suka shigo nan fa ake zaune muka ci abinci mu duka Abbaty ke bani a baki ana nan har sai da aka kira la'asar suka fita,Kausar tayi sallah da Aunty Maryam.....

Fateemah da Asmah suka fita nace uhm wato za'a tafi tarbon Yaya Rashid kenan,tayi dariya ta ja hannun Asmah suka fita......

Aka yi ma Baby wanka nima na shiga bani na fito ba sai kusan Magrib na saka yar Bubu dina......

Nasha Milo sai ga Aunt Ladi kawar Hajiya sunzo barka,Na yafa mayafina na yi crouching na gaishe su ni har Hajiyan kunya nake ji......

Suka fita ana gama sallahn Isha sai ga Abbatyn ya shigo na matse fuska,na juya su Kausar duka suka fita,yace wai Baby laifin me nayi ne da ake guduna....

Nace ai naga kana da wacce kake kulawa yanzu harda wani Allah ya bata miji irinka?Na kara daure fuska....

Baby abun ya kai haka wallahi har na manta shi yasa kike shunning dina?Haba Yammatana please mana kiyi hakuri kinji?

I pouted he held my hand and squatted Baby daka ke ba kari kinji ko?Me kike so na dauko miki a gida ne?

Nace bakomai ai Jamila taje ta dauko mun dazu dama na hada komai ne a wuri daya Ya shafa fuskata yace to a saki fuska mana.....

I smiled nace Yayana kafa na na ciwo sosai,ya zauna dirshan a kasa ya dinga matsa mun kafafuna,har nai bacci tukunna ya fita.....

Can cikin dare na farka na ga Hajiya ne da Inna suna jijjiga Babyn nace Hajiya yaki ya bari ku kwanta tace ai kinsan Babies,na karba na yi breastfeeding nashi sai yayi bacci aka ajiye shi nida Inna da Jamila muka kwana a dakin......

Da safe Innah ta tasheni nayi wanka aka ma Babyn wanka tare da Babyn Kausar nayi breakfast Innah ta bani Babyn sai na kura masa ido ina kallansa ya dauko haskena gashinsa kwance lub kaman na larabawa....

Idonsa abun sha'awa Allah sarki Baban mamanshi sai hawaye ya sirnano daga idona yau nice da Baby wai anwa ne nina haifeshi,ikon Allah.....

Da na samu ya koma bacci dana Jariri da bacci,sai nima na kwanta Hajiya ta hana Kausar surutu kada ta hanani bacci......

Yana kwance shi kadai a gidan duk gidan ya masa girma,Allah sarki Babynsa da yanzu tana nan tana masa shagwabar nan nata yayi missing Khadijansa sosai.....

Allah dai yaji kan iyaye,yana ta juyi yana tunaninta,kai son Khadijatu zai kasheni ya janyo pillow yana perceiving kamshinta....

Ya tashi dai ya shiga wanka,ya kagu yaje gida ya gan kyakkyawar fuskarta da Babyn shi......

Yana fitowa wanka yaji wayansa na ringing yayi murmushi yace kila Babyna ce,Yana duba screen yaga Dr Asiya sai da gabansa ya fadi.....

Yabar ta tana ringing ya gama shirinsa tsab ya buga table da wayan ya kara ringing ni fa duk emergency sai na je naga Babyna......

Ya hada lipton yana sha wayan ya kara ringing ya dauka tayi sallama ya ce ina jinki Dr Allah yas aba emergency bane....

Tace ko alama Dr AT dama na kira na gaisheka ne naji kuma ya Baby da Maman Baby,yace Allah sarki suna lafiya saurin da nake kenan ma naje na gansu sai nazo hospital din.....

Tace to Dr Allah ya kawo ka lafiya sai anjima a gaishe su,yace to ya kashe wayan duk yama rasa me take nifi ya share kawai a zuwan may be saboda da  ita aka karba haihuwan su.....

Ya gama hada komai,ya dauko abunda Khadijama tace ya shiga mota ya tafi sai gida....

Yana karasowa ya hadu da Aunty Saima suka gaisa tai masa barka,Hahiyq na kalle dashi tace Abbana yanzu ko hutawa ba zaka bar yarinyar nan tayi ba ka dinga zarya kenan.....

Ya sosa keya yace Hajiya ai Kausar ma ba zata barta ta huta ba ne,Hahiya tace ka ji dashi,Aunty Saima tace haba Yaya ki barshi yaji da murnar dansa haba dai ya kike ma Abdurazak haka ne....

Yayi dariya Hajiya tace ai dai ba za'a matsa ma Yar Kubran tawa ba yace Aunty Saima ke kadai kika zo?

Tace eh wallahi duk suna makaranta yan uwan naku shi yasa nazo ni kadai amma nasan zasu zo suna ne tare da su Hajiya Babba....

Koda ya shigo ina kwance muna hira da Kausar,Yaya Rashid na rike da Baby,Abbaty yayi mun winking i blushed sai Kausar ta juya ta ganshi tace ai fa dai.....

Yaya Rashid yace kaga yaji kamshin Yaya Abbaty sai motsi yake zai bude ido,na saka dariya yazo ya zauna kusa dani yace Baby ina kwana?

I smiled Lafiya kalau Yayana,yace nayi missing dinki kaman raina zai fita wallahi kasa bacci nayi,nace ko Yayana?

He smiled sosai ma gashi komai banci ba ma,na zare ido sai ga Fateemah da abinci tazo ta zuba ma Yaya Rashid,Nace yauwa ki zubowa Yaya Abbaty....

Ta harareni tace kawai dan ki hadamu fada dama zan zuba masa ne mana,yace hana Ayana har da hararanta ko daga kafa babu?

Tace lah Yaya wasa nake mata nayi shiru Kausar ta fara ai Yaya Abbaty duk ka shagwaba Andeeja kai da Hajiya amma zanyi maganinta ne zamu karo maka Amarya.....

Nace Kausar kinsan bana son rashin Mutunci ko ai nima Yayana ne kuma bazan bari ba,Yaya Rashid yace gaskia Kausar zan saka ki jirgi yanzu kawai tun dazu kina takurawa Deejama haka nan kawai ko na ciro belt ne....

Fateemah ta karba Babyn ta kawowa Yaya Abbaty ya saka shi a cradle ya fara cin abincin sa yana ci yana bani,Yaya. Abdulrauf ma ya shigo shima yaci abincin......

Aunty Saima tace to dukanku 3 kun zama Gauraye ai kuwa Hajiya nada aiki,wai Abdulrauf ya zancen auren ne?

Yace hmm!Aunty Saima kinsan this week ne yakamata aje a saka date to Daddy yace sai an yi sunan Kubransa kinga bani da ja aiko?

Tace hakane Allah ya nuna mana ina zancen ita mahaifiyar yaran nan ne,yace kai Aunty Saima ni bana fatar wani abu ya kara hadamu na gaji ne nayi iya hakuri na da ita......

Aunty Saima tace to sai hakuri saboda yaran ne ai nace nima Aunty nayi ta bashi hakuri yaki yaji......

Aunty Saima tace kaji Andeeja kaman da gaske bari dai muzo mu kawowa Abdulrazak amarya kafin ki gama jego sai na bata fuska na kalle shi.....

Duka aka saka dariya yace Aunty Saima na tuba bana so rufa man asiri kafin Khadijatu ta suma......

Duka suna ta dariya Aunty Saima ta barmu ta fita,Yaya Abbaty ya shiga wurin Daddy shida Yaya Abdulrauf da Rashid ma suka same shi yana breakfast.....

Yace au Hussain dina aka kawo mun Rashid dake dauke da Babyn ya bashi Babyn.....

Ya kara ma Abbaty godiya da ya saka sunan danuwansa yace abun ya masa dadi sosai wallahi.....

Abdulrauf yace ai Daddy gaskia Abbaty yayi nazari Allah dai ya kara hada kawunansu.....

Daddy yace Ameen yace yauwa Abdulrauf nace wai date dinda kace a saka jiya ina kwance Hajiya ke cewa yayi sauri....

Yace haba Daddy wanne sauri kuma nan fa da 3 months ne dan Allah....

Abbaty yace Abdulrauf meye na sauri haka ka bari nan da 6 months dika suka saka dariya....

Daddy yace kaga Abbaty ka fita batun Abbaty nan da Khadijatu nace a kara sati kafin ta koma ai har hawaye sai da ya mun amma yanzu shine ke cewa kana sauri shifa a garin take ma....

Rashid yana dariya har da rike ciki,nan na shigo sanye da hijab na duka daga can bakin kofa nace Daddy ina kwana?

Yace hana Yar gidan Daddy muna fada ne meye na tsayawa can bakin kofa?

Ni kuma kunyar Daddy nake ji,Hajiya dake shigowa tace ai Alhaji ni kaina yanzu Khadijatu bata sakewa dani bansan dalili ba.....

Abdulrauf yace wai kaji fa haba Andeeja wanne kunya ne yanzu haka kikeyi hmm an manta lokacin da ake kwanciya kan kafar Hajiya....

I pouted,Abbaty da duk attention dinsa na wurina kowa ma wurin ya kula sai Daddy yayi gyaran murya yace daga yau ki dinga zaman ki a daki zan dinga zuwa nu gaisa.....

Nace to Daddy na tashi na tafi suna man dariya,Fateemah tace a'ah Yaya Kausar wai kinga Bestie dinki da Hijab suka kwashe da dariya....

Kausar tace ta ji dashi kina nan zata yaye shi,nace uhm na dauko waya na kira Mamana nace haba Mamana nafa zata koda zan bude ido da safe na ganki.....

Tace tunda nafi kowa rashin kunya ko ita Hajiyan ai sai taga bata kokari kenan....

A shagwabe nace haba Mamana dan Allah?Tace ke bafa zanzo ba sai bayan suna,nace Mamam dan Allah kizo mana kafin suna nayi missing naki ni bansan me yasa kika daina sona ba.....

Ina yi kaman zanyi kuka nace idan Ayana ce Mamana ita da kika fi so ai zaki zo mata haba Mamana  kawai sai na saka kuka.....

Koda Yayan ya shigo ina mata kuka su Kausar na kallona suna dariya yace haba Kausar wanne irin rainin hankali ne kika ga Babyn na kuka ba zaki bata hakuri ba......

Tace hmm!Yaya Andeeja ce da shagwaba dadin kukan take ji ne,Fateemah tace wai Yaya baka san shagwabar Aunty Khady ba ne?

Ya matso dai dai Mamana na bani hakuri,ya kalleni zai tike mun hannu na ture hannunsa,ya karbe wayan ya fita parlour yana waya.....

Wayanshi dake kusa dani ta fara ringing naga Dr Fa'iz ne na dauka muka gaisa mukai magana.....

Kausar tace munafinci yanzu bari kiga Fateemah yana shigowa Andeeja zata yi kaman ba ita ke waya tana dariya ba....

Nace ke kika sani Kausar a haka na mallake Yayan naki suka saka dariya Kausar tace ba nace bana son ganinki da samari ba muka saka dariya.....

Ashe shi ke ma kansa ajiyan Kanwar tasa,yana kuwa shigowa na kwantar da kaina kaman ba niba....

Ya zauna a kusa dani na matsa yace Baby wai meye nayi miki?Nace bakomai bakaga su Fateemah ba ?

Yace oh sorry meye basu gani ba amma,shikenan dai me da me kike so ne ki gaya mun....

Nace bakomai Yayana bana son komai,Kausar tace au kin gama kukan kenan?

Nace eh meye ruwanki a ciki kinga Kausar bana so zan gayawa Faizal dinnan....

Ya masto dab da kunne na yace ki daina kula Kausar dinnan yanzu ba inda yake miki ciwo ko?Nace Yaya can kasan na mun ciwo wallahi kuma bayana ma yana ciwo ga ciwon kai ga bleeding dinnan ga bani da appetite.....

Yace duka dai Babyna ya fara rikicewa nace ka samo man magani wannan da aka bani sunyi girma kuma ba dadi,yace to Babyna an gama sannu amma ki kwanta ki huta.....

Kausar ta kalle shi yace Kausar da Fateemah kada ku mata surutu fa bacci zatayi nan ya lallabani ya bani magani nasha harda na bacci ya bani saboda Hajiya ta gaya masa ban huta ba.....

Nan bayan ya fita ba jimawa na kwanta sai bacci,can cikin bacci naji ana tsotsona na bude ido naga Daddy junior Kausar dan wulakanci ta rikeshi yana shan nono.....

Nace haba Bestie meye haka ki bashi naki mana sai a hanani bacci bayan Yayana yace nayi bacci?

Tace to tun dazu yake tsala ihu 2 hours kina wannan baccin yan barka ma nata zuwa kawayena dana Hajiya sai f dai suga Babyn shi kansa mijin naki sau biyu yana kira.....

Nace dan Allah janye mun shi bana so,tace to nidai ki ma daina kunyana Farha dake shigowa na buga salati nace ke meye haka?

Duk madara a jikinta,Kausar tace kinsan dan ubanki a kanki zan sauke haushin ubanki sai kije ki bata kaya wannan na nawa kenan duka karfe 3 fa.....

Nace kina taba ta zan miki duka Kausar daka nice babba kema haka kikayi Hajiya bata miki duka ba kuma....

Aunty Saima tazo ta kama Farha tace kingani ko to ku muje na miki wanka a canja kaya ko?

Farha tace Mami wai zata mun duka ne, Aunty Saima tace tama isa ki kyaleta taje tayi wa Yarta mai gwigwiyayyen gashi dai suka saka dariya.....

Nan muka wuni da su Aunty Maryama matan Yaya Abdulrahman shi yazo daukansu suka tafi bayan ishah Ruth ma da mukai waya ta shigo taga Baby tace yaron likitoci.....

The next day tun safe da yazo suka fita shida Kausar da Aunty Saima ban kara jin duriyarsu ba....

Ni saboda ma stitch din bana son tashi Daddy ma ya shigo ya dade zaune yace Kubra me kike so ki fada a siyo miki,nace Daddy bana son komai wallahi duka Yaya ya siyo mun....

Yace to ga wannan 500 thousand ne kiyi sha'anin biki dashi,nace Daddy dan Allah ka rage wallahi sunyi yawa ina ma fa da kudi ba abunda nakeyi dashi ga hidimar gida kuma kace ka bani abun ya maka yawa.....

Yace  Khadijatu idan ban miki ba wa zan mawa me yasa kullum sai kin nuna bakya son abu ne....

Nace to Daddy na gode sosai na taugunna na karba,yace ba abund akw miki ciwo ko?nace eh Daddy duka naji sauki ne.....

Yace shikenan idan kina son wani abu ki gaya mun,nace to Daddyna nagode sosai Allah ta kara budi Allah ya bar mana ku....

Yace Ameen Allah ya miki albarka,inace ba wani matsala ko?Nace eh Daddy bakomai na dukar da kaina yace dan Allah ki daina kunyar Daddynki mana haba Mamana....

Hajiya tayi sallama tazo ta dire cofood flask nasan farfesun kajin nan ne 4 ake kawo shi ta ce Daddy da Khadijansa nace Hajiya ki mun godia kinga Daddy ya bani kudi har sunyi yawa....

Tace haba dai keda Daddynki din ai ba abunda ke yawa Baby Alhaji an gode Allah ya saka da alkhairi....

Yace wai ina sarkin surutun can ne,Hajiya tace ai yau Kausar da Saima sun fita amma nasan yanzu zasu dawo yace to shikenan....

Rahama ta kasa zuwa taga Miji?Hajiya tace ai abun na Rahama ne ya fara yawa sai ka mata magana ace yau kwana 3 ba ta zo ba kuma tace ba zata zo mana suna ba.....

Alhaji yace gaskia bata kyauta ba nidai nasan tsakanin Khadija da Rahama ba kunya bansan yaushe abun ya fara ba amma karki damu zata zo ne....

Nace nagode Daddy nan muka ta hira sai da yan barka suka zo mutanen gidansu Aunty Maryam Daddy ya shige dan ranar sunday ne bai fita aiki ba.....

Abbaty be kirani ba kuma bai zo ba,sai after magrib suka shigo niki nimi da kaya a can dakin kasa suka ajiye saboda kada na gani da manya manya akwatinansu dozen biyu....

Nace haba Kausar dina kinsan yanda nai missing naki?Tace ki bari nima nayi missing naki ance yan gidansu Aunty Maryam sunzo ko?

Nace eh suna ta tambayarki ma fa,tace ayya ai na dawo nace ina Yarki ne tace au naba Innah a mata wanka ta gaji nima bara nayi wankan nazo muyi dinner nace to har oxtail peppersoup na ajiye miki.....

Ana gama sallahn Ishan ya shigo muna zaune dirshan nni da Kausar muna cin abinci,yace Baby ko waya babu yau?

Na harareshi nace uhm Yaya kenan wanne waya kuma bayan kaki ka kirani ka jefar dani tun yau.....

Kausar tace uhm kin zama katuwa dole ya nemi yar shila,na juya na duba mirror nace bakya tsoron Allah wannan Baban nawa da ya tsotseni tun yanzu....

Yazo ya zauna kusa dani ya saka hannu nace,bari na baka kada ka bata hannunka,ina bashi a baki har muka karasa ci......

Yace ina Daddy junior?Kausar tace ai yana can Jamila ta goyashi idan ba haka ba sai kwanciya ya masa yawa gashi da kukan dare....

Yace Baby baki gaya mun yana kuka ba,na tura baki nace Yaya na manta ne ya saki baki yana kallona...

Ya girgiza kai yace lallai ma Baby abunki ya fara wuce tunani na,ya tashibya fita Kausar ta kwashe kayan abincin su Fateemah da suka fita suma sai lokacin suka dawo tare da Yaya Rashid.....

Ta ce au Yaya Khady yau ke kadai nace eh Kausar ta je kasa,tace to ke yar gata ce Yaya Khady kinga uban kayan da aka siya miki surveniers ne fa mukaje muka siyo .....

Nace oh ni Hajiya bazata yi shawara dani ba ni dai zan kirata muyi magana ai kinga Daddy fa 500k ya bani duk me zanyi dasu Abbatyn ya bani 200 jiya wai koda zan nemi wani abu to meye zan nema Fateemah?

Tace to kiyi shawara da Yaya Kausar kiji amma kinga dakin kasa duka cike yake da surveniers ance gobe ma zamu karo bags dinan masu kyau sosai plates ne cups ne komai fa .....

Hmm!Wai Fateemah ni ina ma naga mutane idan ba dangin Mamana ba banida kowa fa kawata biyu a kano sai kawayen Kausar ne kuma ji bana son biki bansan me zance musu bane ......

Tace kiyi hakuri ai inace irin waliman Yaya Kausar ne za'ayi?Nace to ji ina na sani amma zan mashi magana anjima naji me zai ce....

Kausar ta shigo nace wai Kausar a tayani godia Daddy ya bani kudi masu yawa shine nace to tunda gaki me kikaga yakamata a siyo?

Tace tab Daddyn ne ko Abbatyn zasu bari a karba kudi hanunki a siyo abu ko Hajiya?

Nace a'ah kinga i need to contribute ai na zauna haka,tace to idan kina so suyi fushi dake kenan nidai ba ruwana....

Nace to Kausar meye abunyi,tace to ga advice ke Fateemah me kika ga yakamata ayi ne?

Fateemah tace to ni Yaya Kausar bani da idea wallahi,Kausar tace to sai fa idan zaki kara wani surveniers ne wanda kike ra'ayi bazan hana ba amma banma san me zaki siya ba wanda basu riga sun bayar ba......

Nace to bari zan ma Yayana magana,Kausar tace kaji wani Yayana kaman da gaske.....

Na jiyo muryarsa amma bai shigo ba nace Asmah ta kira mun shi,tukunna ya shigo yace Yadai Yammata?

Nace Yaya laifin me nayi maka ayi hakuri mana,yace ba wani laifi fa Baby naga akwai baki ne na zata a anan dakin suke....

Na kalle shi nima raina ya gama baci nace dama naso muyi magana ne amma barshi kawai nagode....

Na mike na shige bathroom na duka ina ta kuka ita Mamana bata zo ba ga Yayan daga magana ya wani yi fushi dani......

Nayi kukana mai isana na watsa ruwa na fito baya nan lalai ma ni akan me ma yake fushi na manta abunda nace....

Na shareshi Hajiyana ta zo muka zauna nace Hajiya ga wannan na ciro 300k na bata nace a kara a sayi wani abun tace Kubra dont insult me mana haba dai.....

Duk abunda yakamata a siyo an siya kuma wannan kudin ki rike idan ma kina son kari zan kara maki ne haba mana,duk naji kunya nace nagode.....

Jikina a sanyaye tace ne ya sameki ni yau gabadaya na ganki wani iri ina ta so na tambaya nace bakomai Hajiyana....

Amma yau kuka kikayi Andeeja ga idonki nan sunyi ja sosai,nace Hajiya da gaske banyi ba...

Tace wani abun ake miki da bakya so ne?Nace no Hajiya bakomai sai kawai na kasa dauriya na fashe da kuka.....

Tace yau na shiga 3 Kausar na shigowa taga ina ta kuka Hajiya ta rungumeni tana shafa man baya tace me ya sameta ne Kausar,waya bata mata rai?

Tace ina ganin ita da Yayan ne dan lafiya kalau muka barta nida Fateemah to sai naga Asmah ta kirashi dan bai fa leko dakin nan ba kwata kwata....

Hajiya tace bani wayana yana parlour,ta kirashi tace yazo maza tana neman shi ina ta so na tsayar da kukan na kasa.....

Yana shigowa Hajiya ta rufeshi da fada ta inda take shiga bata nan take fita ba,wa yace ya bata mun rai yanzun nan sai ta hada shi da Daddy ai kasan yanda aka yi aka baka ita sai kazo kana misbehaving.....

Yace Hajiya me na mata dan Allah?Shikenan bazan mata fada ba bata son breast feeding haka zamu barta yaro yana jin yinwa haba Hajiya mana....

Tace au ina magana kana magana Abbaty?Yace yi hakuri Hajiya yi hakuri dan Allah.....

Sai sheshekar kuka nakeyi,Hajiya tace to ka shiga taitayinka mu muna sonta duk abunda take so dole shi zamu mata dama yaro dole a siyo mishi madarar a hada yara maza tsotso ne dasu......

Yace haba Hajiya madara kuma tace ba ruwana da wani likitoci kuma kunsha madarar.....

Yace to dan Allah zan siyo yanzu da daren nan wacce za'a dinga bashi ba NAN ko SMA ba tace ka ji dashi dai.....

Yace Khadijatu kiyi hakuri ki daina kukan kinji?Bance komai ba Ya tashi ya fita......

Ya shiga mota jiki a sanyaye wanne madara kuma mtsww yaje store ya siyo Aptamin itace best tana yanayi da breastmilk ma.....

Ya zo ya aika Jamila ta kai ciki ransa a bace yake,ya juya ya je gidan Suraj dama sunyi zasu hadu....

Yana shiga ya zauna,Suraj yace Dr lafiya dai?Yace hmm!kaga fada da Hajiya ta mani yau dinnan Suraj wai kawai Khadijatu daga na mata magana sai ta dinga kuka....

Bani da halin tayi ba daidai ba na mata fada kenan?Suraj ya numfasa yace Abbaty kayi hakuri mana yanzu har ka fara fushi da Babynka?Ka manta wahalar da kasha kafin ta dawo?

A cikin wasa da hikima zaka mata magana mana yanzu haba basai an kai wurin Hajiya ba.....

Yace hmm!Ni wallahi Suraj abun yana daure man kai,nifa kawai fushin wasa nayi saboda ta gyara......

Yace dama Ayshatu ta ce mun tun safw take kuka wai Mamanta taki tazo taga Baby....

Yace kaji fa nayi ta bata hakuri ko jiya amma taki taji,yace to kai Dr ne kasan zata iya samun mood swings ai perhaps shi ne......

Kuyi hakuri ka kirata mana Abbaty,yace ka kyale ta tana can kwance a jikin Hajiyarta.....

Yace to ai nasan ba zaka mayar da hankali ba idan ba hakura tayi ba,nan Suraj ya daga waya ya kira ni....

Na share hawayena na dauka,yace ya muryanki kasa kasa haka?Nace Yaya bacci na tashi ina wuni ina gajiya?

Yace lafiya kalau,dama dai na kira naji me dame ake so na walima mijin naki yace na tambayeki....

Nace ayya Yaya Suraj kada ka damu duka Kausar ta gama komai dama ba wani babban taro bane ni kaga ko friends bani da idan ba dangin Mamana ba.....

So abubuwan da Hajiya ta saka ayi are morethan enough ma,naku ma duka anyi taking care of it......

Yace to Khadijan Abbanta idan an tuna wani abun a gaya mana nace to Yaya Suraj insha Allah zan gaya maka....

Ina ajiye wayan Kausar ta shigo nace yauwa Kausara su Yaya Suraj ba ina so ki saka ayi musu Memo irin wanan na nuna mata kinga sai a kara a cikin bag dinsu tunda da akwai pen a jikin memo din......

Tace an gama Matar Yaya insha Allah bari na dauko wayana na kira,nace Kausar tace na'am please ko nawa yace kudin ki gaya mun dan Allah nagode da kokari.....

Tayi murmushi ta fita,da safe bayan na yi breakfast na saka kayana peplum da skirt na kashe dauri,ina jin ciwon ciki amma ina dauriya......

Kawai sai ga Aunty Saima su Kausar da su Fatee ana ta shigo da akwatuna na saki baki ina kallo,wannan akwatinan sune Yaya ya nuna mun na zaba yace mun abokinsa zai hada lefe tun kafin na haihu......

Dozen biyu daya nawa daya na Baby,aka bude kaya nida Hajiya muna kallo,Baby bed babba haka suka shigo dashi,Baby vibrator meye ma babu.....

Haka dai kaya har kaya Hajiya tace to an gode Allah ya kara budi da yakw dakin Hajiya akwai girma aka jere kayan a nan......

Hajiya tace to ga tukuicinku Aunty Saima nai murmushi suka karba suka fita,Hajiya ta zauna ta kama hannuna tace Khadijatu na kula tun ranar da kuka samu matsala da Yayan naki duka kin canja bakya sakewa.....

Nayi murmushi nace a'ah Hajiya ai na sake tun ranar tace to shikenan ai ki saki jikinki ki fita harkarsa kinji ko?

Kada abunda ya daga miki hankali,nace to insha Allah Hajiya tace au Mamanki ma tana hanya nasan yakamata su karaso yanzu....

Nace da gaske Hajiyana tace eh sosai au bata gaya miki bane?Nace bata kara man waya bama,na kira Jamila ta kwashe plates da komai aka ma dakin turaren wuta Jamila na cewa Aunty kamshin dakin bazai ma Boy yawa ba?

Nace kedai saka ko'ina kinji?Tace anyi fa da safe nace ki dai kara,tayi har kasa,ai kuwa ina nan na kasa zaune na kasa tsaye sai ga sallamar ta naji.....

Kada ace nayi rashin kunya shi yasa ban fita daga dakin ba sai da suka gaisa da Daddy tukunna suka shigo ita da Aunty Nafee......

Na ruga na rungumeta,Aunty Nafee tace wai ni Andeeja yaushe zaki natsu ne,na saki mamana na rungumo Aunty Nafee itama.....

Nace naji dadin zuwanku sosai,sannunku da zuwa suka zauna muka gaisa,su Hajiya suka shigo....

Suka kara gaisawa aka dauko Baby daga Baby bed aka basu na zauna kusa da Mamana ina kallonta ina murmushi....

Sai da Hajiya ta fita Mamana tace ashe Andee bakya da kunya gaban Hajiya?Nace Mama wallahi nayi kewarki sosai sosai kaman nayi ihu.....

Aunty Nafee da larabci tace amma dakin nan an gyara shi ne kaman sabo,nace eh an yi painting gidan ne ai sati kafin na haihu......

Tace gaske yayi kyau sosai,nace kinga kayan barka da Yaya ya kawo suka dudduba suka gani Aunty Nafee tace to ko ke fa yanzu......

Nan su Kausar keta shigo da abinci suka ci sukai sallah kasaru,Ina kwance a jikin Mamana sai ga sallamar Yaya Abbaty.....

Tace to ki daga na gaisa da mijinki ko?Nace to na zaunaya shigo ya yi crouching suka gaisa na kalle shi ya kalle ni......

Na kau da kai Mamana nata godia ita da Aunty Nafee,Yace Su Ammin Abuja ba su zo ba?

Tace eh kaga ai ni yau zan koma su kuma zasu zo gobe idan anyi suna da kwana daya su koma......

Nace Mamana wai da gaske ba zaki kwana ba dan Allah,na rike mata hannu tace a'ah ni ba dan Abbatyn ya matsa ba ai ba zanzo ba sai bayan suna....

Na harareshi ashe ya kamani,Suna ta hira da Ammi sai da aka masa waya yace zaije ne ya dawo....

Yaya Rashid kuwa sarkin kunya suna gaisawa ya gudu Mamana tace shidai Rashid yanzu ya daina yi da ita akan Fateemah.......

Yaya Abdulrauf ma yazo suka sha hira da Mamana Abdulrahman duka kowa yazo aka gaisa jirgintq 6 zai tashi.....

Ta kawo akwati daya na kayan Baby da sarkar zinari ta siya mun nace nagode,nace Maman kinga Yaya ya bani 200k Daddy 500k kuma kna da enough money....

Tace to ki kara surveniers ai nace ai na kara dama ina da wasu kudi daban Yaya Abdul ma su duka sun bani 100 100k kinga 200k....

Rashid ma ya bani da kayan Baby,tace to ai ke yar gata ce,nace kinga dress din da zan saka na walima da komai nashi na turawa Ayana kudin dama su ina da su daban dinkunan da na yi anan Duka na biya....

Kuma almost 10 set na bama Ayana dama aka kai Abuja ita dress nayi order,yanzu me zanyi da kudin....

Tace ina ce zaki hada masa walima Abbatyn?Nace eh duka Hajiya ta bayar da kudin tace to ki kara wani abu akai sai ki siya zinari da kudin ki rage wasu ki siya sarkar Gold ki siya zobe dama zobe biyu ne dake ko ta kalla hannuna nace eh....

Amma ina da wasu da na siya tun ina Riyadh su bana saka su,tace to ki siyo ki masa rich walima fa nace to....

Nace to Mamana ga wannan 200k na baki ki saka mun albarka tace ko kadan bazan karba ba gashi ma wannan 100k baban naki na kaduna yace a baki....

Nace nagode Amma Mamana dan Allah kiji tausayina ki karba ki saka albarka tace to ta karba.....

Su Fateemah suka dawo aka taru fa ana ta hira,Ammi tace Asmah ana gama suna ki koma kin barni ni kadai....

Aunty Nafee mijinta akwai kudi sosai itama kayan yara daga USA ta kawo mun masu masifar kyau.....

Karfe 6 suka tafi na raka su har kasa suka shiga mota ina musu waving driver ya kai su airport.....

Na koma na kwanta na kira Asmah da Fateemah na basu 100k nace suje suyi dinkin biki suka ce sun gode sosai amma Daddy ya ma basu kudi kuma Yaya Abbaty ya basu.......

Nace ai kuwa kun gode sosai,ina kwance ni kadai ina chatting Babyn na can wurinsu Kausar sai ga shi ya shigo....

Banko kalle shi ba na ci gaba da chatting nayi rub da ciki,ya ce Baby ana hutawa ne?

Na kyaleshi yace kiyi hakuri mana Khadijatu,nace nayi shikenan ai bacci nake ji......

Yace sannu ga wannan na kawo miki ance kina fama da ciwon ciki it will help,nace ajiye nan nagode.....

Ai sai ya kama hannuna yace ki kalleni mana,na juyo na kalle shi yace tashi zaune ina zama sai wayanshi ta fara ringing ya daga yayi magana hankali na bai kwanta ba.....

Nace wayw kake waya da ita ne?Yace bakowa kiyi hakuri nidai yanzu,nace zan duba yace ko missing dina bakyayi?

Na tura baki kawai sai ya rungumoni zan janye ya fi karfina nace Yaya bana so dan Allah....

Yace bakomai zan miki ba nace na ji na hakura shikenan,yace naga alama tunda kika haihu ko hannunki bakya si na taba.....

I blushed ashe ya kula,kawai wayarshi dake kan gadon ta fara vibrating dakkowa da zanyi na bashi naga Dr Asiya.....

Nace Asiya me take so me yasa take kiranka kuma Yaya?Yace nima banfa sani ba may be emergency ne na duba nace ina emergency line din?

Yace ai gaya na ya duba ba missed call yayi tsaki ya daga,na tashi na shige bandaki ban kara kulashi ba yayi ta knocking na yi banza dashi shi yasa zata dameni da cewa tana son halayyarsa tun ranar ban yarda da ita ba.........

Ina fitowa na same shi zaune a kasa ya dago da sauri yazo zai yi hugging nawa na zame,yace wallahi Khadijatu ba komai tsakanina da ita duk kiran da take mun cewa take tana gaishe ku ko ta kira taji ya kuka kwana....

Bansan lokacin da nace uwata ce ita da zata dinga kira taji?Yayi shiru yace calm down Baby nasan bakya so jikina ya taba naki amma kiyi hakuri kinji?

Nace dama nasan kana cin amana na kawai ta daka man wata tsawa sai da na shiga taitayina,Yace ya kullum kike zargina ne wai Khadijatu.....

Na fara kwalla na yi kneel down kawai ya juya ya fice duk na rasa me ke man dadi banma san Hajiya ta shigo taga ina kuka ba ta kamani da sauri tace yau dole na gaya wa Alhaji wannan cin kashin da yawa yake.....

Kukan yaci karfina sai ga Kausar da Boy ta shigo shima yana ta tsala ihu,Hajiya ta tashi ta fita na karbeshi....

Kausar ta dafa ni tace Andee menene?Yayanki yayi fushi sosai da ke ki dinga kwantar da hankalinki Abbaty yana sonki sosai ku daina fada da juna bansan me ya hada ku ba amma kuyi hakuri dan Allah.....

Ta goge man hawaye na,Rashid ma ya shigo ya kara bani hakuri yace zai bi Yayan ne sabod ayanda ya fita ransa a bace komai ma zia iya faruwa nan fa hankalina ya tashi matuka.....

Hajiya ta samu Daddy a dakinsa yana kwance tace Daddy akwai matsala fa ni na kasa gane kan Yaran nan ne ka ja ma danka kunne bazai yiwu kullum ya dinga saka Kubra kuka ba bansan kan me yake hada su ba amma wannan ne na karahe bazan lamunta ba.....

Daddy yace Maryama calm down mana menene?Ta ce to kaji ranar haka na ganta tana kuka yau ya fita a fusace na ganta tana kuka nafa gaji wallahi....

Yace ki bari zan dauki mataki Khadijan ce akwai zurfin ciki wallahi,bari i will talk to him naji yarinya da danyen haihuwa zai dinga bata mata rai...

Daddy yace ayi hakuri ranki ya dade kinga yau bana jin dadi zaki kara mun ciwon ne?

Tace a'a ga wayanka ka kirashi ka ja masa kunne ta tashi ta fita,Daddy ya girgiza kai yace oh madalla d son da Hajiya take ma Khadijatu a kullum yana mai gode ma Allah da Khadijatu ta samu suruka kuma uwa ta gari kaman Hajiya Maryama.......

Daddy ya daga waya yace Abbaty duk inda kake kazo ina son ganinka yanzun nan,ya kashe wayan.....

Read,vote and comment

💞💞💞💞💞💞FOREVER YOURS. 💞💞💞💞💞💞💞💞AYSHASAMIRA💞💞💞💞💞💞

Continue Reading

You'll Also Like

712 183 20
Nabeela Muhammad kabeer ....crazy,beautiful,lovely, caring,kind hearted....daughter of Alhaji Sani Muhammad Kabeer.... Some how ending up with Hand...
KASHI By stuckinatale

General Fiction

390K 19.5K 42
"So, Mrs. Kashi Abhay Pratap Singh..chalte hai. Goodbye..". Saying this, he left her broken in this world of betrayal. ~~~~~~~~~~ Kashi, a simple gir...
Ice Cold By m

General Fiction

2.2M 83K 49
[boyxboy] Wren Ridley is always two steps ahead of everyone, or so he thinks. His life seems out of his control when he starts having feelings for so...
185K 22.1K 34
(Editing in process) Salmah, is a normal girl from a normal family with nothing extraordinary about her. She happens to fall in love with Ammar. The...