FOREVER YOURS

By Ayshasamira

54K 3.4K 1.3K

Khadijama Is half Shuwa Arab,a Gentle and simple lady in her mid twenties,follow us as we peak through the li... More

Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35

Chapter 32

1K 72 5
By Ayshasamira

💞💞💞💞FOREVER YOURS 💞💞💞💞By AyshaSamira💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
Chapter 32.......
Wattpad@Ayshasamira
Twitter @Scarlet_Samie

Can Kausar ta bude ido tace au Andeeja tare muka taho lahira,nace bana son iskanci ke kadai kika tafi lahiran bada ni ba ina jijjiga Baby.....

Ta tashi zaune na bata Babyn nace breastfeed her tace wallahi zan rama kinga ki fara bani tea tukunna....

Hajiya nata mana dariya na hada mata tea na bata tasha tukunna ta karba Babyn tana hararena.....

Nace Farha fa tana gidan Aunty Maryam taki ta dawo,nan muka wuni sai yamma aka sallameta after 6 hours kenan.....

Muka dawo gida nan fa yan barka suke ta zuwa bayan kwana biyu sai ga Gwaggo Shatu,ta fara habaicin ta ita dasu Yusrah wai wasu har yanzu dai basu haihu ba ita ko alamun ciki bata gani ba.....

Nidai nama bar wurin na koma parlour din Yaya Rashid na zauna muna hirarmu sai da naji sun tafi na dawo.....

Yaya Abbaty nayi nayi ya barni na kwana yace daga ganin sarkin faea dai miya tai zaki......

Ki jira naki mana ke idan ma kika matsa mun ba gidan da zaki koma fa ko kik haihu a'ah kedai gida gida wai bakya tausaya mun ne Khadijama.....

Nace Sorry Yayana gobe zaka kawo ji ko?Yace eh dole zan kawo ki tunda Daddy da kansa ya saka baki amma gaskia ba har ranar suna ba dole kizo yau gobe ki huta gida kinji Baby kema fa lafiyan bata isheki ba.........

Nace yarda Yayana duk abunda kace na yarda,ai kuwa Faisal ya turo makudan kudi na suna yace ranar sunan zai dawo,hakanan daren suna ya diro kano tare da Yan gidansu.....

Munsha hidima,Nida Aunty Maryam ne muke ta kokarin nan hakanan Ayshatu tana kama mana Mamana da Da Fateema d Asmah suka zo da yake Fateen na hutu akayi walima duk mun galabaita......

Ina zaune kasa dirshan kaman wacce ruwa ya cinye ina cin sinasir sai ga Jamila wai Yaya yace nazo mu tafi....

Nace oh ni baiwar Allah yanzu ma bazai bari na kwana anan ba,Mamana da suka zo ranar suna tace maza kafin na ci miki mutunci ki tafi.,
muka tashi na saka ma Ayshe kayan ta a mota suka tafi muma muka tafi......

Gajiya sosai nake ji nayi wanka na kwanta,banma san ya kwanta ba can cikin baccin nake jin yana kirana na frka firgigit......

Nace Yaya,he smiled calm down tashi kiyi sallah to,nace to na tashi nayi sallah yace kiyi wanka zamu fita ne nace to....

Bacci nake ji kaman me bana ma iya gardama ko tambayan ina zamuje,nan fa nayi wanka na zunduma jallabiya na...

Lokacin yake gaya mun Ayshatu ke labour da asuban nan aka kaita hospital,nace to Yayana banma karya ba kuma yunwa nakeji tunda yanzu aka kaita kuma su Hajiya na hanya bara na karya kadan.....

Ya girgiza kai ya matso daf da fuskata yace Baby amma bakya da lafiya yau ko?Nace eh Yaya wallahi sai a hankali ya akayi ka gane....

Yace hmm!wannan yau ba tambaya kuma very calm Khadijatu ai dole nasan da matsala.....

Nayi murmushi na hada mana tea muka sha da cake,na tashi su Jamila nace musu su shirya zan turo driver ya kaisu gida can zuwa 10......

Suka ce to muka fita sai hospital,yana ta mun dariya wai ni na zama Dr kullum ina hospital,nace nifa Yaya kasan menene?

Allah yasa ba zirga zirgan nan ta tado ma Ayshe labour ba saboda jiya mun jikatu.yace to Allah y tona maki asiri dama shine ko na ga alama.....

Nace Yaya wallahi kosai nan nake so na bakin hospital ka siyo mun,yana ta dariya yace to yau abun da ake so kenan da sauki tunda ba Rake kike so ba.....

Ya tsaya muka siya muka shiga hospital muka samu Suraj a tsaye yace Dr Fateemah ce zata karba haihuwan....

Nace ina su Hajiy yace suna office dina bana so su wahala a tsaye,nace to yace dama ganin su Hajiya ne ban shiga ba saboda kunya amma yanzu kam zan shiga...

Abbaty yana mishi dariya yace yau kai da kanka na zata ai baka da matsala Abbaty ne me kishi ya haka to....

Ya sosa keya yace kaga a gaban kanwata bazan yi magana ba,zan hadu dakai ne........

Nan ma dai ya kasa hakuri ya shiga ciki ya barmu a waje,minti kadan sai ga Yaya Suraj da Baby na karba ina ta murna iyyeh Allah nima ka bani Yar macce in bama Hajiyana mai cire mata kewana.....

Suraj yace Ameen,Abbaty ya zare ido yace au plan din kenan to ban yarda ba Allah ya bamu namiji,nace ai harda namijin duka Hajiyata zan ba....

Yace shikenan all the best,muka shiga dakin da aka ajiye Ayshe,ni da Hajiya da Mamana da su Fateemah kausar ce kawai bata zo ba.....

Nan Hajiyana tace maza na zauna yau in huta kada na taso da Nakuda nace to Hajiya.....

Iyayen Suraj ma suka zo,suka ce ai da Ayshatu zasu tafi sai an gama suna ne zasu bamu ita.....

Hakanan muka zauna muna bayan 6 hours aka sallameta tare dani dasu Asmah aka je gidan iyayen su Hajiya suka tafi gida.....

Kullum can nake wuni su Falmata suka zo kwana daya to buki da Aunty Yagana da Ayyanar Yaya Abdulrauf.....

Aka gama buki Ayyana ana ta shan soyayya da Yaya Abdulrauf,a gidana take kwana kullum yana can,anyi biki da kwana daya suka kama hanyar Abuja suka tafi.....

Mamana ma ta wuce Kaduna aka bar Fateemah da Asmah,Asmah ta dawo gidana Fateemah da Kausar na wurin Hajiya......

Kausar tace wai ke Andeeja dan ubanki a ina kike siyan laces kinga kinfi kowa kyau a pictures dinnan mutane santi leshinki suke na buki na amma wanda kika sa Bikin Ayshe yaci uban na bikina ai kin cinye bikin....

Nace wallahi Yayana ke siyo mun akwai friend dinsu ai dake ko thailand ne ko ina shi ke kawo musu ai kinga Na Ayshatu ma duk wurinsa aka siye na kai mana dinki.....

Tace iyyeh wallahi Daddy yaga abunda ya gani ya hada ki da Abbatyn gashi nan sai mu kuke kunyatawa nace kya ji dashi......

Na kwana biyu ban fita ba ina ta hutawa,Kausar da Babyn tayi 3 months zata tafi,tace Allah yasan ba inda zata tafi sai Matar Yayanta ta haihu....

Faisal ya kirani yana ta mun tsiya wai na hanashi matarsa,nace a mana hakuri dai Faisal.....

Cikina ya fito sosai wata 7 kenan na samu Yayana zaune a parlour yana kallo nace Yayana hijab nake so a dinka mun har kasa babba sosai....

Yace kai keda kanki kike son Hijab ikon Allah,to yanzu kuwa ya kira waya yace a dinka mun guda 5.....

Naki gaya masa dalilina shi da kansa yace wai Baby kwana biyu bakije gida ba lafiya,nace ka bari ai ina missing Arwa sosai da Farha nace ma Yaya Rashid ya kawo mun Farha....

Yace yanzu ta saki jiki dake kenan nace eh,yauwa Yaya ina hijabs din,yace au sorry goben nan zaa kawo maki su....

Nace yauwa ina ce dai Yadin nan dan katsina ne aka dinka mun yace eh sosai nima nafi son kisa saka shi yana miki kyau....

Nace to,da yamma aka kawo mun Farha sarkin rashin ji,muka chocolates dinmu tare sai da tai bacci na kwantar da ita tukunna na shiga wanka na shirya na sameshi....

Yace Maman Baby kinsan dai wallahi ba Farha kadai taci chocolate dinnan ba nace eh ai ita da Mamanta ne....

Yace anya dai Baby haka ranar da Marmie tazo kinma fita cin chocolate bana so ki wahala ne wurin haihuwa nace to na daina Ranka ya dade......

Hakanan na ki zuwa gida sai da aka kawo man hijabs dina tukunna na shirya na saka zumbulelen Hijab dina.....

Ina fitowa ya kwashe da dariya yace wai dama abunda ke hanaki zuwa gida kenan protruded stomach ashe kina da aiki shikenan na huta ma.....

Yanzu haka kina haihuwa zan miki wani kinga ba zaki dinga zuwa gida sosai ba ina dariya nace ai zanta dinka hijabs dinne.....

Muka tafi Kausar nata masifa Yayan naki ne ya hanaki zuwa gidannan na san ko,Asmah tace hmm!Aunty Kausar ba wani Yaya fa kunya takeji a ganta da ciki ai kinga tunda ya kara girma ta daina zuwa.....

Tace hana yo wa yaga Khadijatu da zumbulelen hijab,nan muka wuni har dare ban cire hijab ba har Daddy sai da yace Kubra tun safe fa kike da Hijab dinnan bakya jin zafi......

Nace a'ah Daddy bana ji Hajiya nata mun dariya,duk bayan kwana biyu nake zuwa gida har Marmie duka na dauko su suka dawo wurina saida sukai sati tukunna na mayar dasu....

Farha ma da kanta tace ba zata je ba shine na barta gida,Hajiyana tace ina bukatar hutu na bari na huta mana nace to.......

Ai kuwa ranar da ban tafi gida ba ina fama da ciwon kai ina zaune sai kawai ga Jamila tace Aunty ki taso da matsala nace ta me?

Asmah ta shigo tace Masifaffiyar gwaggon ki ce fa,na zare ido Asmah tace kinsan nifa bana daukan wannan iskancin....

Muka fita na same ta ita da Ramla da Yusrah tana ta kallon gida a kalla nan a kalla can kaman wasu yan kauye.....

Ina shigowa na duka na gaisheta bana so taga cikin jikina dama na zumbula hijab dina naki dagowa.....

Ramla tace munafuka ke ai a munafunci zaki kare Khadijatu,a hada baki dake a ci amana nan ina cousin dinki?

Yusrah tace ai har abunda yafi wannan idan dai wannan mai idon magen ne zata aikata yau dukan tsiya zan mata Mama kinsan na gaya miki dama....

Asmah tace duka a daki juna dai mu zamu zauna ki duketa ne?Ramla tace wannan marar kunyar daga kina tazo ne?

Yusra tace wai kanwar tane baki ga gata nan ruwan munafukan shuwa arabs ba waisu larabawa duk kamshin turarennan na asiri ne suke labawa dashi........

Nidai bance komai ba,nace kuyi hakuri,Asma tace lallai ma Yaya Khady suyi hakuri da akai me?

Yusra tace to Abdulrauf dai na Ramla ne ba wanda ya isa a aure shi yanda aka asirce Abbaty haka muma muka asirce Abdulrauf....

Gwaggo tace hmm!nifa abunda yake damuna daban ke Yusrah baki gaya mun haka gidannan yake ba ita Ramlatu aka barta can wannan mugun gida sai fili ji gida kaman Aljanna.....

Yusrah tace ai baki ga Aljanna ba sai kin shiga wannan parlour din da ciki ai Daddy mu sam baya sonmu....

Gwaggo ta tashi ta shiga koina ta zagaya,Asmah tace wai Yaya Khady ba zakiyi magana ba,Jamila tace ai haka zaki ganta idan dai Aunty Khady ce.....

Ramla da ke tsaye tace ai ke wannan yar aikin har bakinki ya hude haka?Lallai ma zan miki rashin mutunci ta daga hannu ta mari Jamila na rike nace komai ya tsaya a kaina bada su ba.....

Gwaggo na shigowa kenan ta ga na rike hannun Ramla tace kai Ramla kika barta Yusra yi mun kasa kasa da Khadijar nan ta doso kenan sai ga Yaya Abbaty da Abdulrauf din duka sun shigo......

Bansan waya kirasu ba,Yace Yusrah kada ki sake ki taba mun Mata wallahi tunda ku ba kirki ne daku ba zumuncin a daina me ya kawo ku gidana,?

Yaya Abdulrauf yace ke Ramla daka nan kada ki koma gidana ki je gidanku sai na neme ki ku ko kunya bakwaji.....

Gwaggo shatu ta saka salati yanzu Abdulrauf a gabana kake cewa taje gidanku kaga tsinanne wanda basu san ciwon kansu ba yar uwar taku kuna da yar uwa kaman su Ramla kunfi son dangin dangarere.........

Ba wanda yace wani abu cikinsu,Yaya Abbaty yace inzo muka wuce parlour dinsa can naji sun buga kofa sun fita.....

Ai kuwa da dare yace na shirya muje Daddy na neman mu,muka je muka samu Yaya Abdulrauf da Daddy ina ta boye cikin nawa a cikin hijab muka zauna Hajiya ta shigo aka zauna......

Daddy yace ashe abun da Shatu tayi muku kenan kuyi hakuri amma nayi shawara kai Abdulrauf zaka saki Ramlat ka kawo yaran nan wurin Hajiya idan kayi aure daga baya ka dauke su amma hada iri da Gwaggo Shatu da akwai matsala....

Ranar ance Ramla miliyan 3 ta sace maka ko?Kayi hakuri amma ka sake ta idan zaka iya ni a nawa ra'ayi.....

Yace wallahi Daddy da ya fi mani ni kaina bana jin dadin zama da Ramla kawai ina ladabi ne gwanda a rabu a huta......

Hajiya tace a'ah ya kuke magana kman hadin baki kada ayi haka sai a muku tabon masu sakin matan Farko kayi hakuri ta zauna tunda akwai yara amma rabuwan aure bashi da Dadi kaima Daddy bai kamata ba......

Abbaty yace Hajiya abun su ne da yawa fa kiga Gateman ne ya kira mu yace muyi sauri muzo danuwanka ya zama mugun abu nan duk lalurar gidannan ba wanda Ramla take zuwa haba.....

Hajiya tace a daiyi hakuri dan Allah bana son rabuwan aure Daddy ransa a bace yake sosai.....

Yace Hajiya ki bari kawai tun yaran basuyi yawa ba nan fa tazo ta gama zaginki jiya me yasa zata zauna tun jiya na yanke ba zata kara zama a matsayin matarsa ba ashe da ta gama nan sai suka kwasa yau suka je wurin Deeja a'ah bazan lamunta ba Alhaji ya fada yana girgiza kai........

Suna rife baki sai ga Gwaggon ta turo kofan tare da Yusrah da Ramla suna wani rike kugu,tace au taron munafunci ake yi a anan to kunyi kadan a kawo wata sadakar yalla a matsayin kishiyar Ramla......

Hajiya tace kuyi hakuri dan Allah ku zauna ayi sulhu ke Shatu,Ramla tace wanne sulhu za'ayi ke ai kece munafukar tsohuwar kina wani a zauna a ina....

Na mike ba shiri nama manta ina boye ciki nace Hajiyar tawa kike zagi to badai ita ba wallahi.....

Daddy dasu Yaya suka tashi Daddy yace Shatu ni kika zaga ba ita ba sai tari ya kama Daddy.....

Abdulrauf yace mu uwar mu tafi karfin a zageta ki je na sakeki Ramla,tace ni ka saka yace eh ke din wacece....

Abbaty ya kama Daddy ya zaunar ya samo masa ruwa ya bashi ya sha,Daddy yace Shatu maza ki fita ki barmun gida....

Ta saka ihu wai an rabata da danuwanta yace ko a lahira bana so na ganki Shatu ki fice mun daga gida.....

Suka fita,Hahiya taje ta dauko magani aka ba ma Alhaji muna nan zaune muna mishi sannu.....

Yaya Abdulrauf ya fita yaje ya dauko Yaransa ya dawo dasu duk gasu nan kaman ba Yayan yan gayu ba duk sun jeme kaya ba yabo ba fallasa......

Na jasu naba Jamila ta musu wanka ba su da wani kayan kirki,dole kayan Farha aka saka musu,Kausar tace kai Khadijatu ashe kin iya masifa ni ina bacci naji ana hayaniya me yasa baku kiranj ba inji dana musu duka......

Daddy yace gwanda da baccin ya kamaki ke kam Kausar akwai masifa wallahi tace sannu Daddy amma hmm!

Yace to daga yau a daina fadan hakanan ku fita harkar su na kira mijinta na gaya masa dama tun dazu nasan magana ya mata ta taso tazo taimako zan ci gaba yanda aka saba......

Abbaty yace Allah dai ya kyauta ace danuwanka baya sonka sai abun hannunka,Daddy yace to Abdulrauf yanzu sai ka rike matarka hannu bibbiyu san Allah ina nifin kanwar Kubra.....

Yace to,nan muka tashi muka wuce nace Kausar yau da Babyn nan zan tafi fa nikam tace gaki ga ta kuje da Innah Amma saboda mugun kukan nan.....

Nace kya ji dashi dai wallahi nidai wai sai ace sai na koma gida,tana ta dariya tace ke kika sani dai yana nan yana jiranki.....

Naje muka koma gida nace nifa Yayana banji dadin sakin Ramla ba dan zasu zata ko Ayyanah ce yace au kema kinbi side din Hajiya ai ni da 3 ma ya mata kowa ya huta ......

Nace haba Yayana 3 kayi m Fareedah ne na kara bude kafa,yace ko hauka nake zan kara kula Fareedah ne dan Allah?

Idan kika kara zancen Fareedah ba zaki fita gida ba gobe daga ANC zan maido ki nan nace ayi hakuri tuba nake dan Allah......

Yace ni da ke ne yau,nace wayyo Daddyna zo ka taimaka mun,ya saka dariya yace kinganki bakya jin magana......

Can bayan kwana biyu mun fita da dare sai ga wayanshi na ringing yana dagawa yace innalillahi wa inna ilaihi rajiun da gaske to Allah yaji kan musulmi Mamanta fa?

Kai hauka dai da gaske?To kagani ko karshen kenan Allah ya mana kyakkyawan karshe ni da tayi saboda ni ga abunda ta ja ma kanta gani lafiya da Matana........

Ya kashe Abdulrahman ya kirashi nace ka bani Yayan yace to wallahi kuwa eh kagani ko eh ai baka nan akayi wannan scene din har suka sa hawan jinin Daddy ya taso ai bazan hanaka ba kaje ka ci musu mutunci ka kara tsorata su.....

Ya bani wayan na karba nace Yayana ka gudu kaki zuwa ayi zumunci dan Allah?Yace to ai Marmie na nan ko?

Nace to ai Yayana nake son gani ai kuwa Abbaty ya dinga zungurina,na gama wayan na bashi.......

Yace Baby kinci sa'a ana ruwan sama da ajiye ki zanyi a nan ki taka zuwa gida,nace ne nayi ne Yayana?

Yace na zata Yayana in a romantic way ne ashe harda Abdulrahman haka ake ce masa,nace lala haba dai bakaji yanda nake fadan naka ba Yayana na lankwasa murya.......

Naka special ne sai ya tike zuciyansa yace indeed na yarda saboda yanda aka fada nawa daban ne....

I raised an eyebrow nace yauwa Habibina,yace yauwa ko ke fa Babyna,My wife the apple of my eyes.....

I blushed after few days ne Kausar kw gaya mun wai ai Fareedah ta rasu mamanta ta haukace nace kai ki bari dan Allah?

Tace au be gaya miki ba nace uhm kinga bamu cika maganar ba da shi fa shi yasa......

Allah sarki,Allah yaji kanta wayyo ita ko Maman Allah ya bara lafiya wannan masifa da me tayi kama........

Ina komawa gida muna kwance nace Yaya ashe Fareedah ta rasu?Yace au eh ta rasu fa,nace Allah sarki Allah yaji kanta yace Ameen.....

Da alama baya son maganar sai na kyaleshi kawai ina ta tuna ta Allah sarki akan namiji hmm!

Yace me kike ma ajiyan zuciya Baby?Nace bakomai Yayana wallahi cikin na mun nauyi ne......

Sannu Babyna wallahi kina kokari ma amma bakya son exercise kin daina ana gama asuba zan tadaki muje mu zagayo da yamma ma kina yi kinji?

Nace to Yaya insha Allah,zan daure na rika yi wai Yaya ya akw haihuwa ne?Ance da zafi sosai ya zanyi ne Allah yas ba mutuwa zanyi ba....

Ya dinga dariya yace yanda aka haifeki Ammi bata mutu ba insha Allah kema ba zaki mutu ba shikenan?Nace a'ah ba yanda zaayi zafin yayi subsiding?

He smiled akwai kar ki taba damuwa ke matar Dr da kanta kanwar Doctors su Suraj ai dole naki daban ne,he was laughing hysterically har sai da na fahimci he was teasing me......

I pouted and said haba Habibina,he smiled an daina yi hakuri Sarautar mata.....

Ai kuwa the next month aka dauko fasting(azumi)idan nayi yau gobe bazanyi ba haka nake yi amma lokacin Iftar idan na fara aiki ni kaina nake cewa su Jamila su karasa......

Shine first azumin da friends dinsa zasu dinga shan ruwa bayan 3 years shi da Dr Zaid,da Dr Shu'aibu......

Suma ba kullum ne suke zuwa ba,haka nan azumi nata tafiya duk ina ta wahala yace na daina har na haihu nace a'ah ni fa tunda bashi zai mun ramakon ba.......

Lokacin Tahajjud kuwa ba kullum nake tashi ba unlike wancan azumin da muke tahajjud tare,bacci nake yi kullum sai nayi mafarkin mai tsoro night mares.....

Har ya ce to bazai dinga fitan ba a gida zai yi Sallahn haka dai dinkin Sallah ma Maternity gowns na saka aka mun Kausar nata mun dariya........

Koda Akayi Sallah ai cikina ya zana wani irin Babba ko me zansa ai bzai boye shi ba sai kawai na rage fita ban fiye zuwa gida ba sai dai Kausar tazo....

Mamana ko sun kira video call sai dai na tura musu fuskana kawai,Fateemah tace sai ta dauki picture na.....

Batasan Asmah ta mun ba nima ban sani ba,haka nake zama idan ya fita na samo mango nayi ta sha bayan ya hanani.......

Ina kwance a parlour sai ga Jamila Aunty nace na'am wai kinyi bako yace yana waje,nace anya dai Jamila kodai Asma yake nifi?

Tace kedai yake nifi,nace waye ne to?Tace ban sanshi ba amma kila dan uwanku ne nace to Jamila waye zai zo bazai man waya ba......

Sai ga Call din Abbaty wai na bar Yaya Furqan a waje,Nace to Yayana bai ce mun ga suna ba kuma baifa kirani ba shi ya sa nace ta shiga dashi parlour din Yayan yace yana zuwa.....

Ina ta guna guni yanzu sai yaga Kataon cikin nan kenan yaka san me nayi oh ni me yasa bai bari sai nan da sati kadan ba haka dai har na shiga ina ba kaina dariya.....

Yace Khadijatu ce wannan da Hijab har kasa?Nace Yaya nice mana da bana sakawa yace to nidai nasan ko sallah da Jallab kike yi bansan yanda aka samu progress ba amma ai abunda kike boyewa bazai boyu ba.....

Na saka dariya nace sannu da zuwa shine ba zaka wani kira ba har kasa gabana nata faduwa ba dalili......

Yace ayi hakuri kinsan wani aiki nazo yi fa to na gama flight dina na yamma ne naje na gaishe da Hajiyanki da Daddy nace kar Kausar ko Rashid su fada miki nazo....

Yanzu na baki suprise visit ai kinji dadi ko?Nace sosai kawai dai tafiyan naka da an bari sai na haihu ko ranar dana haihu,yana ta dariya yace wai dama Andeeja haka kike da kunya suk da arab muke maganan.....

Nace ina Yaya Faruk ne to?Yace Faruk dinnan naku ya tafi Umrah aure ma fa yake so yayi anytime soon....

Nace eyyah ai na zata rana daya zakuyi ku hutar damu,amma ayi nashi ayi naka da yake kai Maiduguri zaka mayar damu,muka saka dariya..........

Yaya Abbaty ya shigo,muna ta hira na kawo musu lunch suka ci sai yamma ya kaishi airport oh danuwa mai dadi,Ammi sai da ta aiko mun da sakon turaruka da arabian face glows dinnan....

Nace ya gaya ma Ayshe ta dawo hakanan nayi missing dinta ni kadai a gari ba dadi,ya gaisa da Asmah kafin ya tafi.......

Bayan shagwaba ba abunda nake ma Abbaty wani lokacin ma sai ya tafi office nace ya dawo kamshinsa nake son naji..........

Yaya Abdulrauf kuwa haka su Ramla suka ta binshi yace ina har abasa bazai mayar da mugun iri ba suje a nemi wani ba shi ba.........

Ranar kuwa ina strolling wata tace kaman Khadijatu Turaki,na juya nace eh nice baiwar Allah....

Tace kai baki gane ni bane?Na danyi tunani nasan face din amma na manta,tace nice fa Ruth tare mukayi FGC Zaria class dinmu daya science class.....

Nace Ruthy ya akayi kika yi wannan kibar haka,tace kedai bari yarana 4 sun hurani sosai da hausanta a karkace,nace kai naji dadin ganinki a kano kike?

Tace eh a kano nake fa nan nayi aure na bar Minna dama a minna nake ai,Ranar ma na hadu da Shu'aib daidai wurin nan.....

Nace kai haba may be ma gidan mu ya fito nan ne Family house dinmu gidana amma ba nan unguwan bane zan baki adress mukayi exchanging number ta tafi....

Ina shiga nake ba Kausar labari tace ke na kuwa taba haduwa da ita da yake gidanta a nan unguwan ne take ce mun ya akayi sunana Turaki tana da kawa Turaki sam na manta na tambayeki amma an dade sosai fa.....

Allah sarki ashe nurse ce ma,ita Ruth tana da kirki ai har taso lokacin ta aura Shu'aib fa tana sonshi sosai kuma kuwa maganan shi ta fara yi mini......

Allah sarki ashe Shu'aib ma ba'a barshi a baya ba he was a player says Kausar,nace sosai kuwa yanmatansa 3 lokacin ayi ta ba su Ruth aiki saboda suna son saurayin seniours,muna ta dariya......

💞💞💞💞💞💞FOREVER YOURS 💞💞💞💞AYSHASAMIRA💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

Read,vote and comment......

Continue Reading

You'll Also Like

Gentle touch By K

General Fiction

46.9K 1.1K 32
It had been mere months after her eighteen birthday, when she was pulled from the safe haven of her life and forced into the fantasy the women had cr...
287K 20.8K 24
[#4 on Spiritual🔥🔥 On 24 September 2018] "Why is everybody avoiding me because of my voice? Was I the one that created myself? No. I was ridiculed...
57.3K 6.1K 23
Her crush. The guy she liked since her first day of school, he never looked her way, didn't care about her at all. She thought it was because he like...
185K 22.1K 34
(Editing in process) Salmah, is a normal girl from a normal family with nothing extraordinary about her. She happens to fall in love with Ammar. The...