FOREVER YOURS

By Ayshasamira

54.1K 3.4K 1.3K

Khadijama Is half Shuwa Arab,a Gentle and simple lady in her mid twenties,follow us as we peak through the li... More

Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35

Chapter 26

1.2K 83 35
By Ayshasamira

💞💞💞💞FOREVER YOURS 💞💞💞💞By AyshaSamira💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞
Chapter 26.......
Wattpad@Ayshasamira
Twitter @Scarlet_Samie....

Abbaty yama rasa mai zaiyi ne,Matar aure matar ma matarsa innalillahi,yana zaune Yaron da bazai kai Rashid ba ya sauko yana labe labe ya fice da gudu....

Sai gata da bedsheet din ma ya yane jikinta tazo ta durkusa,Kafin ma tace komai ya fice ya tada mota yabar gidan......

Yama rasa Ina zaije me yake masa dadi,Ga Babynsa tana ta kiransa,Ya kifa kansa a jikin sitiyari yafi minti talatin a hakan,ya kira Rashid yaji ko in a key din farm house dinsa......

Yaje can ya yi parking ya guda gidan ya zauna Khadijatu tana ta kira sai ga text dinta ma duk sai tausayinta ya kama shi baiwar Allah.....

Shi yasa aka ce abunda babba ya hango Yaro bazai hango ba lokacin da aka bashi Khadijatu da yayi hakuri ya zauna da ita kadai da yanzu bazai ga wannan tashin hankali ba....

Kai Saboda rudewa Abbaty har kuka sai da yayi,yana nan bai ma san karfe Gina tayi ba sallah kawai ke dagashi daga Inda yake zaune....

Can sai ya tashi ya rufe gidan ya tafi gidansa,Yana bude kofa ta taso da saurinta duk sai ta bashi tausayi....

Ta taso da saurinta tana tambaya Yayana lafiya dai Ina ta kiranka?Har Yaya Suraj na kira lafiya Yayana?

Kawai sai ya rungumoni gaba daya,Ina jin zafin hawayensa a jikina,Yayana kuka kakeyi?

Daddy ne ko Hajiya me ya same su?Na shiga 3,Abunda nake maimaitawa kenan,Munfi minti him a haka....

Sai nayi karfin Hali na rba jikinmu na jashi zuwa dakinsa,na zaunar dashi Kn gado idonshi a kasa....

Na rasa me zanyi,na kama hannunsa na rika,Yayana baka da lafiya ne?He nodded eh kaina ke ciwo....

Yayana zaka watsa ruwa kaci abinci sai na dauko maka magani duk idonka sunyi ja sosai sannu Yayana.....

Shikenan bara n shiga wankan hakanan na taimaka masa ya cire kayan sa ya shiga wanka nan nayi zaune Ina tunani to wai me yasa Yaya zai mun karya nasan akwai abunda ke damunsa......

Bazan kara tambayar sa ba,Na kai masa abinci na ajiye,na dauko mashi pajamas na ajiye Ina ta tunani me ya same shi bai taba kai time dinnan nauyi checking on me ba....

He didn't even comment on my endless calls,I sight Allah kasa lafiya,I picked my phone na kira Rashid mukai magana naga baice komai ba na kashe nasan gida lafiya....

Na kira mama na ma naji lafiya,Ina duba time to ai Yaya Abbaty baya dadewa har haka a bathroom,na ajiye kayan ka kwankwasa na ji shiru....

Na tura kofar na ganshi a cikin bathtub ya cika ruwa yayi kwance ne ko zamansa zance....

Bansan me yake tunani ba sai infant girgiza kai da sauri,naje na zauna a bakin bathtub din.....

Herbeebiena dan Allah ka ajiye duk damuwar da kake tare da ita ka samu natsuwa ba wai Ina son nasan meke damunka ba ne,a'ah ganin ka a haka zai jefani a matsanananciyar damuwa dan Allah Yayana......

Na taimaka masa yayi wanka muka fito,ya sanya kayansa muka zauna Dakyar na samu yayi spoon 5 bansan me yake tunawa ba ya yi sauri ya girgiza kai Kaman wanda ke tsorata......

Nidai Ina ta karanto duk Addu'an da tazo bakina bansan wanda ya bata masa rai har haka ba nasan shi yana da fada Amma ba mutum bane mai yawan fushi....

Haka dai yana gama ci ya hau kan bed ya kwanta na kwashe komai nakai kitchen na rufe gida na zo na kashe wuta.....

Na dora kansa kan chest dina nidai har bacci ya kwasheni bansan meke faruwa ba a cikin zuciyarsa....

Abbaty kuwa har safe bai runtsa ba Idan ya tuna rayuwan aurensa da Fareedah ya tuna duk kenan abunda yake mata wani ma yana mata kuma duk abunda take masa tana ma wani sai hankalinsa ya tashi wata kyamar ta ta kamashi....

Mata ba gaba daya yaji ya tsane su Amma Yana son Khadijatu Kim yasan b a zata aikata hakan ba,haka dai y dinga saka wannan ya kwance....

Ai dole first thing tomorrow yaje ayi masa ma HIV test shida Khadijansa to Ina ma yasan ko maza nawa taje kwanciya dasu...

Haka yai ta Addu'a da ya tabbatar bacci ya dauke Khadijatu ya samu ya zame jikinsa ai ya dauro alwala yana ta sallah yana rokon Allah ya kawo masa sasaauci da mafita Saboda baima dan me yake masa dadi ba.....

Har n farka da Naji Assalatu na hango shi akan sallaya,na dauro alwala nayi Fajr Ina jira inji yace muyi jam'i naga yayi sallarsa min anayi tawa na kara kwantawa.....

Can cikin bacci I was feeling nauseous na tashi Ai kuwa sai Amai Ina bathroom Ina ta kwara amai na gama na wanko jikina nayi wanka gabadaya....

Lokacin na kula baya dakin,na fito nan na ganshi parlour dinsa kwance kam couch,na duka na gaisheshi baima amsa ba na tafi dakina.....

Na hada masa breakfast na kai masa,na koma dakina nayi bacci na bayan na gayawa Jamil abunda zata girka mana for lunch......

Ina bacci Naji kiran sallah azahar na tashi nayi sallah,Ina nan Ina gayawa Allah matsalana Ina rokon Allah ya yayewa Yayana duk abunda yake damunsa.......

Na jira sai 2:30 naje na kai masa Lunch yana nan kwance dai yanda na barshi,naje dining naga breakfast dina yanda na barshi raina ya fara baci .....

Na kwashe na ajiye lunch na fita,nan kara komawa ba sai past 5 na sameshi kam sallaya fuskarsa ba Yabo ba fallasa......

Na kwashe abincin bai ma taba ba,na yi masa gulab jamun na kai masa ko kallona bai yi ba,gashi this days saurin fushi nake da shi raina yayi matukar baci Amma kawai nayi tunani kila fa operation yayi patient bai yi making ba .....

Na bashi uzuri akai dinner haka na kai masa na tura masa text masu dadi,Ina nan zaune parlour Muna kallo nida Jamila Amma ni hankali na sam baya kam movie din......

Sai ga call din Suraj,muka gaisa sai yake tambayana Ina mijina,Nace ai baya jin dadi ya kwanta ne,sai yayi ajiyan zuciya yace to kice dashi ya kunna wayarsa mana nace to na ajiye....

Da na tashi kwanciya nan neme da da ba nace Jamil tayi shimfida a dakina mukayi baccin mu ni bacci mai nauyi ke daukana this days ma Bana sanin me akeyi dana samu bacci......

Da safe na tashi asuba na shiga wurin da nan na sameshi dai kam sallayarsa bai taba dinner ba haka gulab jamun....

Nayi ajiyan zuciya mai karfi sai da ya waigo ya kalleni na kwashe kwanukan,nayi sallah na nemi wuri na kwanta nayi bacci na....

Dana farka ne na fara damuwa Wai me ke faruwa ne kofa abinci baya ci ko zan kira su Hajiya ne....

Ina wannan tunani Ina ta to and fro a parlour saiga wayan Suraj,Ina dagawa yace mun gashi a waje da sauri na naje parlour dinsa na bude kofar.....

Yaya Suraj ya kalleni ya girgiza kai muka gaisa na barshi na fita,Ina ta tunani to meke faruwa nidai ko na kira Daddy ne na gaya masa kawai nima sai na fara hawaye bansna dalili ba.....

To ya zanyi da raina ace ni ban kai matsayin da Yaya zai Gaya mun damuwarsa ba,Ina ta tunani Bayan Kaman hour 1 sai ga call din Yaya Suraj....

Can naje na sameshi,yace mun zai tafi na bishi a waje nace Yaya dan Allah me ya sameshi Ina ga zan kira Daddy da Hajiya ne kawai kwana biyu ko kallon abinci baya yi bansan ko me yake damunsa ba.....

Yayi murmushi yace Khadijama kada ki damu akwai abunda ke damunsa ki taimaka ki fitar dashi wannan damuwa yace baya so a sani kada ki kira su Hajiya ki barshi zuwa gobe mu gani kinji?

To Yaya Dr na fada ina share kwalla,duk tausayina ya kama Dr Suraj ya buga motarsa ya tafi.....

Duk yanda Bana so abun ya dameni sai ya dinga damuna,har zan shiga wurinsa sai nayi tunani nace kai Kila space yake so kada na takura shi ya tafi ne gurin Fareedah....

Ina nan har aka gama lunch abinci kawai nake kai masa koda na shiga baya nan na duba koina nan gansa ba to sai kuma na dawo nace Jamila ta dubo man ko motarsa na nan tace bata nan.....

Yana shiga da boy Yan dauko wasu abubuwansa ya rufe gidan Saboda baya son tuna abun da ya gani,duk tunaninsa ai Fareedah ta tafi gidansu.....

Ai kuwa ya sameta zaune ita da Mamanta da kanwar ta,suna gaishe shi ko amsawa bai yi ba ya kalleta yace ke meye kike yi a gidannan Kafin na dauki ki kwashe duk wani abu da yake maki ne a gidannan ki tafi na sakeki saki 2 ya zama 3 kenan maza ki fita da ke da koma waye kike tare dasu......

Allah Idan na sameki anan zan kira miki police aure ne ya kare ki dauki kayanki ki fita yanzun nan....

Maman ta nisa haba Abbaty kaddara ce ta hau kanta hakuri ake yi mana,Ya kalli Maman yace Mama da kin bata tarbiyya ta gari da hakan bai faru ba Ina tunanin bata gaya miki abunda tayi bane na baku minti 10.....

Ya haura sama bai kara kallonsu ba,yana kwashe sauran abubuwansa ya zuba a portfolio.....

Sai ga Fareedah a durkushe tana kuka dan Allah Abbaty kayi hakuri sharrin shaidan ne Wallahi Ina sonka sosai ai da yayi wani kwallo da ita sai Mamanta ce ta kamata ya kira gateman yace ayi waje dasu kada na bude idona na gansu a gidannan.....

Ai kuwa Koran kare aka masu ita da Yan aikinta duka ya dates gidansa yace Idan na gansu ko kusa da gidannan kai aikinka ya kare ya buga motarsa ya tafi.....

Ya dawo gida baiga Khadijansa ba,ya ajiye kayansa yana ta son ganinta ya shiga side dinsu ya sameta tana bacci a kan carpet ma kasa......

Jamila tana tausa mata kafa,suka gaisa da Jamila baya son ya tashe ta ya koma ya hada tea dinsa ya sha,baya jin zai iya cin komai Saboda takaici mun Fareedah itama Khadijatu Kaman tayi fushi ne baiwar Allah......

Nan yake ta sallah yana rokon Allah,can ya tuna ya lalubo number wanda Ke test a Hospital dinsu yace mai yana son HIV da Hepatitis test yazo yanzu gidansa.....

Ai kuwa ya lallaba ya je Jamila ta tashi yana so ya diba jinin Khadijatu ya saka abun nan da take magana wanda ake sakawa a yatsa ya guda jinin ya fito sai ya ga ta zaburo ta bude ido sai ya hade bakinsu ya fara kissing nata......

Bayan some minutes ya kyaleta ya tashi ya tafi ita kuma wani azababben bacci ne yake damunta bata ko iya daga ido ta kara kwantawa.....

Yazo ya diba nashi blood din ya tafi dasu yace in a day zai dawo da result,Yana nan zaune kan sallaya can ya kashe wayarsa ma.....

Nan shima bacci yayi awon gaba dashi,nidai Sai Bayan asr na farka Ina tunani ko mafarki nakeyi da Abbatyn yayi kissing dina can na duba hannu na inda nake jin ciwo to kuma jinin menene ake diba yau.....

Haka dai muka wuni Muna gida daya ba wanda yace da wani komai,na kai dinner na dauko lunch dina muka aikawa gateman ya kara dashi ko yayi sadaka......

Haka na kwana a dakina tare da Jamila,Safe na tashi nayi asuba kenan sai Jamila take tambayana me za'a girka for breakfast,nace to bara naje naga ko yaci lunch Idan bai ci ba kawai musha tea and bread dinmu......

Na dubo naga suna nan yanda suke na ce ta kwanta abunta musha tea and bread,nan ma nace ta bani ruwan zafi Yanzu zan karya yunwa nake ji.....

Ai kuwa ta ajiye mun Ina hada tea sai tace Aunty Khady kada nayi kaudi dan Allah Kiyi hakuri mana ki shirya da Yayan.....

Nace Jamila Ina fada dashi ne?Tace to Kiyi hakuri Aunty Khady bafa ina saka ido bane naga kwana biyun nan da dare duk sai ya shigo dakin nan jiya yafi hour daya yana kallonki har tashi nayi Zan fita yace na yi zamana.....

Da gaske Jamila?Eh Wallahi Aunty shekaranjia ma sai da na fita na barshi Ina kwance Naji rufe kofarsa na dawo.....

Ai bansan Ana yi ba ni wannan ciwon ya isheni ji nake kaman a cire mun jinin jikina a canja wani....

Ai kina ma kokari Aunty Khadijama naga bakya kwanta wa ciwo Alalh dai ya baki lafiya Amma har wani fari kinyi sosai fa....

Bari kedai nan nasha tea dina na kwanta Muna ta hira ta gyara gida na fita parlour na muka fara kallon nan Namu.....

Ai kuwa sai Naji Ina so nayi fitsari,Ina shiga toilet Naji duk wani jiri ke taso mun,Ina fitowa Ina dafa abubuwa na samu na kawo parlour din daga nan sai naga wani duhu sai nayi ihu Jamila shi kuma Yayan shigowanshi kenan sai yayi sauri ya rungumeni.....

Ni ai daga nan bansan Inda kaina yake ba ya kwantar dani kan couch a living room dinsa ya ce Jamila ta bashi bowl sabo da ruwa,ya bude closet ya dakko sabon towel....

Temperature na yayi high sosai,ya matse towel din ya daura mun akai,ya rubuta wasu medications yace taje zumunta pharmacy yanzu ta karbo ya mashi waya......

Dama yasan za'ayi haka PCV yayi low sosai,Khadijatun ce bata son jin magana game da health issues.....

Haka aka kawo drip din ya daura mun guda 3 za'a saka Saboda bata da karfin jiki......

Ya kira Jamila yace akwai Ugwu a gidannan ta ce eh akwai yace taje tayi ma Auntynta source ki dafa white spaghetti nasan zata ci ki saka Hanta sosai a source din ki kuma matse shi ki hada da Maltina Kafin ta tashi.....

Ta tafi yana nan rike da hannuna yana kallon fuskata wannan kyau haka sai shagwaba duk yayi missing shagwabar kai bazai yarda laifin wata ya shafi kanwarsa ba Amma kawai he wanted to be alone ne abun na dawo masa....

Bayan hour daya na bude ido naganni a Inda nake na tuna abunda ya faru,Ya kalleni Sannu kin tashi?Ban ce dashi kala ba.....

Ya kira Jamila ta kawo abincin yayi serving dina ya ci sa'a yunwa nake ji na ci source din da Spaghetti to ruwan kam na kasa sha nikam.....

Baby please,Yaya I chimed in dan Allah karka ce mun komai Bana so ka mun magana if dai after 3 days sai yanzu Bana so,dama ka bari na mutu Ka huta kawai.....

Haba Babyna baki fa san irin damuwar da nake ciki ba ko tausayina bakya ji this is unlike you my Baby I missed you so much kinsan da Bana so na kulaki bazan zo nan gidan ba ko?

I kept quiet nasan Babyna da hakuri Kiyi hakuri,ka kira su Hajiya da Daddyna?

Lokacin ya tuna bara ya kira Hajiya ita kadai zata saka Khadijatu ta sha magani duk injections ya saka a drip din,nan ya kira Hajiya ya gaya mata....

Ko minti goma baa kara ba sai ga Hajiya da Daddy sunzo,Hajiya nata fada me yasa bai kaita gida ba.....

Nan dai Hajiya ta saka nasha wannan abun mara dadi,Daddy duk hankalinsa a tashe me ya sameta ne Abbaty?

Wallahi jiri ya kwashe ta bata cin abinci,Khadijatu na gaya mata PCV dinta is low Amma taki taci wai ba dadi maltina ma bata sha to bansan ya zanyi da ita ba.....

Yana magana Ina harararsa kawai Bana so Daddy yaga rashin kunya na Shi yasa na kyaleshi.....

Amma na cika Fam,Sannu Kubra Hajiya ta fada yanzu ai ba zan barki a nan ba dole da ita zan tafi Alhaji can a karasa saka drip din....

Abbaty ya sosa kansa Hajiya ai total bed rest take so ki barta zan kula da ita dan Allah Hajiya....

Hajiya ta tashi Khadijatu me da me like so na daukar miki mu tafi,Yauwa Hajiya akwai karamar traveling bag dina tana nan Jamila ta nuna miki komai nawa yana ciki dazu da safe kawai na hada jakar.....

Sai hankalin Abbaty ya tashi nan take idonsa yayi ja,kenan Khadijatu yau dama niyyan tayi ta tafi gida ya shiga 3....

Daddy dai na waya hankalinsa baya nan yama juya baya,sai Abbaty ya matsu kusa dani Baby kada muyi haka mana kinsan Ina sonki sosai ko....

I eyed him Ka kyaleni fa Bana so,I frowned my face,Hajiya na dawowa tace a bari Jamila ta kamkamta kitchen mu tafi Ina zan bar Yar tawa ba kula ai ko kwana biyu ne sai tayi Idan naga ta murmure sai na maido maka da ita.....

Daddy yayi murmushi yace to Hajiya ai nasan su duka ne zaki mayar Amma nima na goyi Bayan zuwa da ita gara Inda akwai Babba......

Haka yana kallo muka shige motar Daddy da driver da Daddy a gaba ni Jamila da Hajiya a baya an cire drip din wai zai samemu a can ya mayar mun .....

Muna shiga muka samu Rashid da Fateemah Ana soyayya a parlour,Subhanallah!Hajiya baki gaya mun Deejama ba lafiya ba,Rashid uttered....

Ai Ni Yaya Rashid ka daina damuwa dani tunda yarinyar nan tazo Amma ai zata tafi ne dole nice zaka samu anan....

Na hau sama dakin Hajiya nayi alwala nayi sallah zuhr Ina nan zaune akayi asr,Sai ga Yaya din ya shigo da drips din nashi .....

Yazo zai saka na tsala ihu wayyo Bana so,Hajiya ta rugo da gudu menene?Me ya sameta me kayi mata?

Hajiya me zan mata Wai fa drip dinne bata so,dama suma tayi shine na saka mata ai bata sani ba....

Kayi mata a hankali mana dama hannun Likitoci yafi na nurses zafi ai haba ,he looked at me I was still eyeing him.....

Nidai saka mata a hankali dan Allah,Hajiya kuwa tayi zaune Ina ta zuba shagwabana dole yanayi Ina ihu....

Rashid da Fateemah suna mun dariya,Fateema na basu labarin yanda nake tsoron injection da girmana....

Nan Hajiya ta barmu ta sauka kasa ta duba abunda zaa girka mun......

Fateemah tana da evening lectures suka fita tare da Rashid sai ni da shi kadai.....

Ya matsu kusa dani Baby Kiyi hakuri mana,na daure ai dai Yaya koma patient dinka ya Mutu yakamata ka yarda da kaddara ai shi bawa Allah yana jarrabarsa.....

Amma baka nuna mun cewa ni matarka bace shine Kaki kati confiding in me abun ya mun zafi ba hanyar da ban bi ba ka ki to me zan maka sai yanzu ka zo ka dameni Bana son hakanan.....

Haba Babyna na cancanci ki tausaya mun mana wani Hali ne na shiga wanda Bana so na gaya miki Saboda baki da lafiya nasan abun zai girgiza ki Shi yasa Amma dan Allah Kiyi hakuri mana ko sai nayi kuka ne nima he copied me....

He then hugged me,kwantawa zanyi Yaya,kuma ka cire mun wannan drip din masifar ni bacci zanyi Bana so....

Bansan Babyna da fushi haka ba Allah Saboda kawai bakya da lafiya ne na ksa gaya miki abunda ke damuna kinji ki yafe wa Yayanki mana.....

Nadanyi nazari kadan na tureshi Bana so Yayana dan Allah ka bari Kaje Idan ka gama fushi da rashin cin abinci tukunna ka dawo muyi magana.....

He smiled Babyna na shiga Yanayin da abinci baya Ka burgeni Wallahi kawai duniyan ce abubuwa suka mun yawa Kiyi hakuri....

Me yasa ka diba mun jini Bada permission ba?I thought your body is mine Baby har sai na nemi permission.....

He started kissing me I am sorry Baby please forgive your husband nasan fushi ba halinki bane....

Nasan kina da understanding Babyna uhm kodai ciwon nan da ke sakaki bacci ne ke saka ki fushi,he ticked me I smiled....

Yayana zan yafe maka a condition daya,granted koma menene he chimed in....

To Yayana kayi promise zaka Gaya mun abunda yakw damunka shine kadai zai da na hakura....

I promise Amma Sai kin samu sauki ko zuwa gobe ko jibi Wallahi zan Gaya maki Babyna he hugged me....

Ana kiran Magrib drip na karewa nayi sallah muka zauna muka ci abinci tare nayi Ishah shine aka saka na biyu...

Yaya yaushe zai kare nikam,I pouted to Baby ke Kiyi baccinki mana menene na damuwa?

11:30 zan cire maki sai na tafi gida tunda kin gujeni,I pushed my mouth nice na gujeka?

He nodded yes Kubran Hajiyanta,uhm ko Ina nan Yayana ba tare muke kwana ba,kuma kafi 10 daya baka kulani koda muke kwana tare.....

Baby kinsan fa ba kaurace miki nayi ba Saboda baki da lafiya ne na baki bed rest ne....

Kinyi missing dina Sosai ko Babyna?I pouted nidai bance ba kawai magana nayi....

Wai Baby in tambayeki?I nodded baki san meke damunki ba da gaske?I smiled Ina ga harda ulcer ke damuna saboda na cika cin abinci yanzu...

Ulcer da me?He asked malaria David a Wallahi Yaya duk symptoms din malaria da typhoid nake da....

He smiled ya zawo paper daga pocket dinsa ya bani,Ina duba wa na fara Shillong kan gado yayi sauri ya rikeni kina so ya fita ne?

I nodded no stay still ai tunda har na hakura na 10 days ba zan bari Kiyi wasa  ki janyo mun miscarriage ba....

I smiled after 3 years Allah na gode maka,Yayana I said swiftly yanzu kwana nawa ya rage...

He looked at me na me kenan Baby?Wancan abun mana,munyi 10 days yanzu ai ko....

He looked at me yana murmushi Babyna kinyi missing dina da yawa ne?Da nasan baki cika damuwa ba....

Nidai Yaya ba wai missing dinka nayi ba Ina so na sani ne Saboda na kara kiyaye wa.....

5 days ya rage ko 6 ma,I pushed my mouth to shikenan bazan koma ba sai after a week....

With his gaped mouth he looked at me,dama Saboda abun kike zaune can ne?

I smiled then closed my eyes da hannu daya a'ah Yayana shikenan kwana biyu zanyi yayi maka?

Kice dai nima na dawo nan din mu zauna tare duka,kinga I want to kiss you Kafin mamanki tazo nasan yanzu zata zo ta tsare mu....

I smiled he kissed me passionately,he smiled then pecked me Ina sonki sosai Khadijatu muna gida daya ma tunaninki nake yi inaga an dauke mun ke .....

Yayana nima Ina sonka sosai wallahi kawai abunda ka mun ne ya bata mun rai badan shi ba bazan biyo Hajiyana ba....

Ha smiled Baby kin yarda kina da juna biyu ko?I nodded shyly kin yarda kin canja da bakya mita bakya fushi mai tsanani ga baccin nan naki mai yawa....

I pouted Yaya ka daina mana,Muna ta soyayyarmu sai ga Hajiya da miyar ugwu dinta da taji kifi nidai na koshi tace dole sai kinci ai ko zaki samu karfi.....

Yayan da kanshi ya dinga bani sai da na koshi sosai,Hajiya ta shigo tare da Jamila da su Innah suka mun ya jiki suka kwashe kayan....

Daddy ya shigo yaga Yayan,wai Abbaty baka tafi ba?Daddy ai naga dare bai yi ba just 10pm ne....

Daddy yayi murmushi muka zauna Ana ta hira,Bayan Daddy ya fita ne Hajiya ta bishi kawai Kaman wanda ke jiransu yayi hugging dina.....

Babyna yanzu ki kwanta nasan kina jin bacci kinga zan miki injection kuma zata sakaki bacci....

Wai Yayana dole kai zaka mun ka sa a mun mana,Babyna kinsan irin kishin ki da nakeyi kuwa?

I nodded sai gasu Rashid sun shigo,haka Ina ihu ya dauko syringe din sai yayi hugging dina yana gaya mun magana mai dadi har yayi injection din shiga ya hana ni ihu......

Nan kara 20 minutes ba na kwanta sai bacci,bansan lokacin da ya tafi ba su Rashid ma suna ta hiransu har Hajiya ta dawo suka tafi suka kwanta Muma Hajiya ta kashe wuta nida Jamila da Hajiya muka kwana a dakin......

The next day na tashi nayi wanka na shirya nasan d a yazo zai saka drip dinnan hannuna har yayi ciwo dadin abun saura Daya,.......

Ina ta dokim ganinsa,gashi nan ga wayana ba Yaya Rashid na shigowa na karba wayarsa na kirashi sai na jiyo muryarshi a parlour....

Yana shigowa ya zauna a kusa dani,he whispered Babyna kinyi missing dina ko?Sorry benzoyl da sauri ba gashi har past 9 bacci yaso ya daukeni.....

Ya dauko kayan aikinsa wai sai anyi flushing wurin ya cushe,haka dai ya mun wayo lokacin su Rashid sun fita,ya saka syringe din Inda zaiyi flushin sai ya fara kissing dina da hakan ne zafin ya dan mun sauki Amma Naji zafin flushing dinnan.....

Aka dora drip din Muna nan mance da juna ita kanta Hajiya ta kula da irin kallon da Yaya yake mun na irin I want you......

Ana Azahar har cikin raina naji Sanyi ya cire mun Kafin ya tafi masallaci Ina gama Sallah sai ga su Ayshatu.....

I hugged her I missed you Ayshatu,ba wani missing ki ka kasa kirana baki da lafiya kina da wanda ya fi miki nine agarinnan ta fada da arabic....

Nima da arabic nake magana nace Kiyi hakuri Ayshe mana Wallahi Yanzu haka wayana yana hannun Yaya yaki ya bani wai bedrest nake kiji fa.....

Shikenan ai tunda nazo na huce Sannu ya jikin?Nace Lafiya kalau sai ga Fateemah ta shigo Muna ta hira mu duka 3....

Ya shigo yace nazo na gaishe da Yaya Suraj a parlour na shiga yana rike da hannuna muka gaisa ya mun ya jiki tukunna ya tafi....

Nan Ayshe ta wuni kuwa sai dare yazo suka tafi,har abinci Hajiya ta saka mata suka tafi da shi wai zata iya jin yunwa da dare......

Ai kuwa Abbaty na shigowa nace Yaya wayana mana,ya zauna yana copying dina ba zan baki ba sai gobe Ina sonki huta yanzu Idan na baki nasan chatting zaki tayi......

Yayana jiya Ina ta so na kiraka Naji muryarka Wallahi na rasa ya zanyi,he smiled da gaske Babyna?

I nodded to lokacin ya fito wayar ya bani,zan iya kiranki ai Hajiya bata nan da dare?I nodded eh sai Idan kuma baccin nan ne ya daukeni.....

Da haka akai mun injection nayi bacci can cikin dare daga ni sai Jamila shine na kirashi muka sha soyayyar mu....

The next day an gama saka drip injection kawai zai mun da safe da dare,shine yazo da safe Bayan munyi breakfast yaje office.....

Ko hour daya baiyi ba ya dawo,Muna kissing juna a dakin Hajiya dan ya hanani fita ko parlour ne sai ga sallamar Aunty Saima......

Tana shigowa muka gaisheta,ya zauna tace ni fushi nake da ku ace ba zaku iya zuwa nan da katsina ba tunda kukayi aure sau daya fa kuka zo....

Nace Aunty Kiyi hakuri laifin Yaya ne shine baya barina kinsan bazan ki zuwa ba,she smiled ai na sani Kubran Hajiya ko nan din ai Hajiya na complain baya so Kiyi nisa dashi ni ai gani nazo to Abbaty.....

Ayi hakuri Aunty Saima Ina ta going through abubuwa ne tace eh ai Naji na maka murnar rabuwa da wannan Fareedar yanzu ai ba aure tsakaninku ko Hajiya tace saki 3 kenan ko Idan aka hada dana farkon?

Allah ya taimakeka bansan kam abunda ta maka ba ta kule hakurinka Amma Khadijamar ka ta isheka Abbaty kuyi zamanku lafiya kai da Yar uwarka....

Ya jikin Khadijama Ina ta surutu,kinji sauki ko?Nace eh Aunty,Allah ya baki lafiya matar Doctor naga shi da kansa yake jinya ba nurse shine komai we both laughed......

Sai kaina ya kulle saki 3?Bayan Aunty Saima ta fita na kalli Yaya,Yayana ka saki Fareedah?

He smiled eh Khadijatu yanzu ke kadai ce hankalinki ya kwanta ko?No I nodded me yayi zafi Yayana har saki biyu at once aka hado dayan can 3 haba Yayana....

He smiled ai I promised to tell you abunda ta mun ko?So don't worry kiji sauki dai Babyna kinji I pouted I am sorry bansan me kake going through ba all this days....

Amma Yayana you can confide in me ba wai in dinga jin abu a gida ba Bayan Ina tare dakai baka Gaya mun nasan Bana son zancenta Amma irin this is important na sani ko?

Kiyi hakuri My Love insha Allah daga yau bazan kara boye miki komai ba,Abbatyn ma naki ne to me zan boye miki we both smiled.....

I hugged him I can't wait a cire mun wannan Canular duk ta bi da dameni,Allah sarki Babyna ji nake kaman na cire ciwon na mayar a jikina ki huta.....

Ita kuwa Fareedah suna can ita da mamarta hankali tashe Ina zasu Ai kuwa sai gidan gobe da nisa.....

Aka gama bayani yace ai solution daya ne sai ya kwana da Fareedah ne kadai asirin zaiyi Abbaty ya mayar da ita....

Ta kalla gobe da nisa duk sai taji amai yake ji tace haba Malam ya zan kwana dakai ai kawai na hakura dashi....

Mamanta ta kalleta haba Fareedah shikenan kinyi giving up?Tace eh Mummy da na kwana da wannan kam nayi giving up,nan dai suka ci gaba da shawara ita da Mamanta.......

Read,vote and comment...

💞💞💞💞💞FOREVER YOURS 💞💞💞💞💞💞AYSHASAMIRA 💞💞💞💞💞

Continue Reading

You'll Also Like

214K 2.3K 9
An English Hausa novel. Aisha, a girl with dreams and ambition. She wants to further her education and become an independent woman. But what will...
185K 22.1K 34
(Editing in process) Salmah, is a normal girl from a normal family with nothing extraordinary about her. She happens to fall in love with Ammar. The...
38.9K 4.4K 26
It all comes down to LOVE and SACRIFICE. Follow me on this voyage and I guarantee you'll find it fascinating. Note: The pictures you will see here a...
39.2K 506 3
When Khalil and Abdul clash over the affections of Minal, tensions rise and sparks fly. With a wedding hanging in the balance, it's a battle of love...