HAKKI NE

By ZahraSurbajo0

899 27 5

soyayya,azabtarwa,juriya hakuri,gamida darasi me zafi aciki ku shiga ku karantazekya More

HAKKI NE 1

899 27 5
By ZahraSurbajo0

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
       *HAKKI   NE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

_Zahra surbajo_

*Bissimillahirrahmanir rahim.*

_wannan littafi me suna asama k'irk'irarran labarine,ban yishi dan wani ko wata ba in kunji abun da yay dede da rayuwarku arashine_

_Abun da ze zamo alkhairi Allah ya bani ikon rubutawa,ya kaudani daga akasin hakan_

*Sadaukarwa ga Hauwa'u Muhamnad Danjuma Nbs keffi,Alherin Allah ya kai miki*

*1*

"Na rantse da girman Allah duk shegen da ya kuma dukarmin d'a a layin nan se yasan ya daka,uban wa ya haifamin yaran da zan zauna ay ta dukarmin"cewar hajiya inna dake ta faman zage zage atsakar layi,makwabta duk sun leko suna kallonta.

Seda tayi masifar ta iya masifa sannan ta kad'a kanta ta koma cikin gidanta dan ta rarrashi d'an nata da aka daka agurin wasa shi da yara yan uwansa.
      A zaune ta samu yaron yana wanke fuskarshi datasha kuka.karasawa kusa dashi tayi  ta dafashi tace,"kai ma ne modibbo ko kadan baka biyo halina ba,da ka biyo halina to wlh da kudi akace suyi ma haka bazasuyi ba,dan san da zakaci ubansu wasani"

Yaron d'an kimanin shekaru goma shabiyar,D'ago ido yayi yakalli mahaifiyar tashi yace cikin taushin murya,"inna to meye ribar yin fad'a da mutane kullum,be da wata fa'ida"ya fadi yana kokarin mik'ewa.

"Dalla can jani talau kawai,ay sekaje kaita bari ana jibgarka,"cewar inna cikin jin haushi.

Murmushi yayi sannan yace cikin ladabi"inna ta takaina Allah yabar min ke,batun gaskiya inna,gwanda daban rama ba sabida kinga su mada kowa yasan basa ji,in mukayi rigima cewa za'ayi tafiyata d'aya dasu shine kawai yasa na hakura"

Kwafa inna tayi sannan tace"can ta cakalkale maka,Shiyasa mutallib ke burgeni be barin ta kwana,ni b'ace min da gani sullutu kawai'"

D'an rusinawa yayi yace"Allah ya huci zuciyarki inna ta"yana gama fad'i yasa kai ya wuce zuwa d'akinshi.

Muje zuwa.

Surbajo for life.

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
      *HAKKI NE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra surbajo

*Dedicated to Hauwau muhammad danjuma nbs keffi*

*2*

Modibbo tunda ya shige d'aki yake share kwalla dan inda sabo yasaba da fad'an na innar tasa.

Mutallib ne yashigo d'akin da saurinsa rai ab'ace ya k'arasa gun d'an uwan nasa yace yana huci"Dan uwa naji ance su mada sunma taron dangi sun dokeka agun wasa da gaske ne?"ya tambaya yana huci.

A hankali Midibbo ya kalli d"an uwan nasa yace"da gaske ne mutallib amma ay na barsu da Allah"be jira yagama jin meze ce ba ya juya da gudu zuwa waje yana fad'in"Wlh basu daki banza ba duk shegen daya kwana lafiya shiyaso"
   Inna na zaune taga shigewarshi da gudu,ay bata tsaya d'aukar mayafi ba ta biyo bayanshi da gudu tana gyara d'aurin zaninta tana fad'in"maza jarumi na,me share kuka na,karka barsu seka rama masa maza ka kwato kimar gidanku"

Shiko mutallib tunda ya falla dq gudu seda ya isa majalisar su mada,duk wanda ke gurin seda ya kwasheshi da mari,nan ko sukayo kansa,cikin ikon Allah basuyi galaba akanshi ba har aka rabasu,ya juyo ya dawo gida.

A k'ofar gidan yasamu inna tsaye tana masa abunnan da akewa k'auraye"chau chau nawa,Alkah de ya biya yan maza,"murmushi yayi yace"naci uwarsu inna"

Jan shi tayi zuwa cikin gida tana murna,modibbo koda suka shigo cikin gidan be fitoba zaman shi yayi.

*FARKON LABARI*

Malam Habu dattijone d'an kimanin shekaru sitti da biyar,bafulatannin jihar katsinane awani gari da ake kira Kaita.
    Matar shi d'aya me suna Fatima yaransu na ce mata inna, da  y"ay"ansu biyu maza,na farin sunanshi Muhammad,amma suna cemasa Midibbo sabuda sunan baban malam yake dashi,se me binsa mutallib,tun daga kan mutallib inna ko ta samu ciki sede ya zube,har daga karshe ma bata kara samu ba.

So na gidan duniya inna ta d'orashi akan y'ay'anta,k'uda akan dole yake tab'a mata su,amma dan wani mutum na layi binka zatai har gida taji baasin dukar mata d'a.

Shekarun madibbo goma aduniya shi kuma mutallib bakwai Allah yaywa mahaifinsu rasuwa.

Duk d'awainiyarsu seta dawo gun inna,dan taki ba kowa y'ay'an ta yarda ta fita tai aykatau ta kawo musu abin bukata.

Akan y'ay'anta,zata iya cin mutuncin kowa daya tab'a mata su.

Tun kan rasuwar malam yake jan kunnenta bisa mugun son da take nunawa y'ay'an amma tayi burus abunta.

Mutanen anguwa har sun ganota,shiyasa ko ina gulmarta sukeyi ita ko ko ajikinta.

Mutallib yaro ne me jini ajika dabe barin kota kwana,sha yqnzu mqgani yanzu,sab'anin Modibbi da kwata kwata beson damuwa bare yay hayaniya,rayuwarshi cike take da sanyin hali.

*wannan kenan*

*Cigaban labari.*

Surbajo for life.

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀
       *HAKKI NE*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra surbajo

*Dedicated to hauwau muhammad danjuma nbs keffi*

*3*

A kwai shak'uwa me k'arfi tsakanin modibbo da mutallib,shiyasa mutallib be jure a wulak'anta masa d'an uwa be d'auki mataki ba.
     A nata b'angaren inna tafi son mutallib sabida shi beda hak'uri,ko kad'an ga zafin zuciya,hakan yasa take kallonsa a matsayin jarumj.
  Shi ko modibbo kota kanshi bata bi dan tace sullutune shi wanda besan ciwon kanshi ba.

A b'angaren kulawa da iliminsu kuwa inna na iya bakin k'ok'arinta wajen ganin sun samu ilimi wadatacce,har zuwa yanzu da suke secondry school.

Inna ta tsaya tsayin daka,dan ganin y'ay'anta sun haska a duniyar ilimi,modibbo nada k'ok'ari sosai,yayin da mutallib kuma se anci kwakwa yake fahimtar abu.

Haka rayuwarsu ta kasance,suna matukar k'aunar junansu sede shi modibbo ba me son tashin hankali bane..

BAYAN SHEKARU GOMA SHA BIYAR.

Sanye yake da farar rigar ma'aikatan lafiya,hannunshi rik'e da wasu takardu,ya nufi wani office cikin sauri.

  Modibbo Habu Kaita kenan,matashin likita d'an kimanin shekaru talatin da haihuwa.

Koda shigar shi office d'in  mutanen dake ciki suka mik'e da sauri suka had'a baki gurin fad'in."likita ya ake ciki ta haihu?"

Goge gumi yayi sannan yace"Gaskiya sede kuyi hak'uri amma ayki za'ayi mata,dan d'an a gicciye yake munyi iya yinmu abun yaci tura,yanzu zaku bada kud'in ayki dubu shabiyar sannan ku kawo jini leda uku,"

Jiki asanyaye wani wanda nike kyautata zaton shine mijinta yace,"likita ataimaka mana don Allah,wallahi bamu da dubu sha biyar,amma za'a samu dubu biyar,agurinmu,ataimakemu jinin kuma adebi nawa"

D'an nazarinsa modibbo yayi sannan yace "ba damuwa,Allah ya bata lafiya"

Takarda ya rubuta musu suka sa hannu sannan suka je suka biya kud'in,shi ya cika musu dubu biyar din,suna ta masa godiya.

Minti talatin ya kwashe yayin gudanar da aykin sannan ya kammala,yaciro yaro namiji sankacece.

Seda ya tabbatar komai lafiya sannan ya fara shirin komawa garin su,wato Kaita.

A Dutsen safe yake ayki,a asibitin gomnati na garin,yana daukar albashin dubu hamsin duk wata,

Da albashinshi yaci gaba da d'aukar nauyin karatun muatallib sannan yaci gaba da kula da gida,sabida tun samun aykinshi inna ta dena neman kud'i,acewarta lokacin hutunta yazo.

Da la'asar ya iso gida,akan mashin d'inshi lifan.wanda da k'yar inna ta barshi ya siya acewarta lokacin siyan beyiba.

A tsakar gida yasameta,duk'awa yayi har k'asa yace"inna ta barka da gida na dawo, ya ayki?"
    Murmushi tayi sannan tace"sannu da zuwa modibbo,ina nan nayi tsuru ance hanyar dutsen safe an yanka wani,hankalina duk ya tashi nace to Allah dawo da modibbo lafiya"
  Murmushi yayi yace"eh inna nima ina gun ayki naji ana labarin Allah de yakawo kwanciyar hankali ak'asarmu baki d'aya"

"Ameen"cewar inna

Daga haka suka d'an tab'a hira,sannan ya mik'e yashige d'akin su shida mutallib domin yad'an kintsa.

Muje zuwa
.

Surbajo for life.

Continue Reading

You'll Also Like

1.5M 26K 53
What if Aaron Warner's sunshine daughter fell for Kenji Kishimoto's grumpy son? - This fanfic takes place almost 20 years after Believe me. Aaron and...
287K 13.8K 93
Riven Dixon, the youngest of the Dixon brothers, the half brother of Merle and Daryl dixon was a troubled young teen with lots of anger in his body...
81.6K 2.4K 38
Francesca Astor came to Love Island to find her soulmate, and once she sets her eyes on him, she's never letting go. Rob Rausch x Fem!oc #1 robertrau...
1.7M 61.8K 43
" Wtf is wrong with you, can't you sleep peacefully " " I-Its pain..ning d-down there, I can't...s-sleep " " JUST SLEEP QUIETLY & LET ME ALSO SLEEP...