MAH~NOOR🌹

By AfricanQueen300

87.2K 8.2K 1.3K

Free book I grew up with this, I had best friends became enemies and then best friends again. I love it now... More

Prologue
destinations
Welcome to Hamoud Boualem Company...
Meet Mr Hot Guy
She take my position
Hamoud Boualem Family
Promotion
Personal information
Sisterhood
Big Mistake
Dreams
Interview
MR Arrogant
hateatfirstsight
Courage
My Nikkab
The Name
hypocrisy
Kidnapped
Escape
Injured
Exclusively
Approched
Mine
My Favorite
Silent
You are my Destiny
i'm in luv
Contract Marriage
Confessing
Bonus page
Tracking
stupidly
Chased Game
The Game is Over..
My wife...
Hopefully
Am sorry
Other side
The Family
Happy end.... Mr And Mrs Mahir Hamoud Boualem
Lover

Faruq

1.6K 179 42
By AfricanQueen300

https://www.wattpad.com/1012619907?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=MrsUsman400&wp_originator=%2F3Psbc8CzWLIt7nhOc%2Fefbq6TGO%2FoqXkdLl3tWqojpTg2slpkg41f2y3BNyNBTybBTJuuTrS0AdI0DareqPNPHmvNiA4X%2BuxvowSA2Z7n4iZx0w6%2BJj7HrArcFk40LE%2F

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣9️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

   Zama tayi a gaban Noorh cikin tsananin kaunar Jikarta, ji take kamar tana barin gurin zata samu mugun labarin an sace ta,shi yasa da Yaranta suka nemi ta koma gida wani irin kallo tayi musu cikin balokoko take kallon su, tab'e baki tayi sannan tace.
"Wato nayi saki reshe ku kama min ganye? Na tafi ku aiko min da cewa ƙaddara ce ta sani tafiya shine tafi ta baku sani ba, ko ba haka ba?"

   Duk suka yi shiru, kafin ta gyada kai sannan yace musu.
"Toh bani zuwa ko ina sai naga yanayin jikin nata, idan kuma a kanku nake zaku iya dauka ta cak ku kai ni gida."

     Shiru suka yi, tare da sunkuyar da kansu, dan sun san tunda Dadah tace babu inda zata ko zasu mutu su dawo ba zata je ko ina ba.

     .....
Allah ya azurtata da yara bakwai, maza hudu mata uku.
Dr Hisham, Dr Ubaidullahi, Dr Abubakar, sannan Baban Noorh, Asiyah, Mariya, sai Ma'idah tana aure a gidan su Maman Noorh, tana auren General Adam Yaqub Wazir,

      Wato asalin familyn baki daya auren zumunta ne, Dr Hisham.

Yana auren Babbar Yayar Maman Noorh, wato Maisarah mahaifiyar Faruq, sannan  Ubaidullahi yana auren Yar Kanwar Hajiya Kakar Mahir, Su'adat.

            Ita kuma Mariyah tana auren Kawun Mahir kanin Baban shi, da suke Uba daya, Asiyah tana auren, Controller custom, Mr Abdul Fatah. Cousins Brother Maman Noorh ne, Kanwar shi me suna Siyamah ita Abubakar yake aure, Salha Maman Noorh kuma baban Noorh aka hada su, ita yar Nana ce, domin da ita da Maman Faruq da Maman Naaz Su'adat, duk Nana ce ta haife su. Su hudu Allah ya bata yaran.

Dan haka suma kuma yaran su auren zumunta aka musu. A halin yanzun kuma wanda yake kawo musu matsala a cikin gidan Shine Faruq dan.tunda aka mishi baiko da Naaz yace baya sonta kuma da suna mutunci sosai.

Tunda batun aure ya shigo ne, duk suka tsani junan su, sannan itama Naaz akwai wanda take so, mahaifin shi yana daya daga cikin manyan yan kasuwan ƙasar.

           ----
A hankali take bude idanunta, tare da bin ko ina da kallo, wani dan banzan juyi da cikinta yayi yasata ware idanun ta, akan matar da take sallah.
"Masha Allah! Sannu yar nan? Yunwa kike ji ko?"
Tashi tayi daga abin sallah, sannan ta juya zuwa ban daki ta haɗa mata ruwan wanka, tazo ta cire mata karin ruwan (☹️🤔)

     Ta rike ta, ita Noorh ta mata kallon tausayi dan taga ta manyanta, ita kuma tana wa Noorh kallon tausayin ba zata iya kome ba. Dan haka suka shiga ban dakin da kanta, ta shiga taimakawa Noorh ta cire kayanta, tayi mata wanka sosai. Sannan ta fito da wata ƙatuwar towel ta kawo mata, da hijab kanta kuwa ta wanke shi kamar ba shine a curkude ba, sannan suka fito bayan ta duba kafarta, ta gyara mata zaman bandajin.

       Tunda suka fito, ta shimfid'a mata abin sallah, ta bata doguwar riga ta saka, sannan tace mata.
"Zaki yi sallar ko zaki fara cin abincin?"

Wani irin kuka ne yazo mata, ta zauna a bakin gadon.
"Duk abinda akace nayi zanyi."
Bata ruwan zafi tayi ta fara sha, tana idarwa ta koma ta dauko kwano a cikin ban daki ta bawa Noorh ruwa ta wanke bakinta, sannan ta umarce ta, da tayi sallah.
......
A hankali dakin ya fara cika, tana idar da Sallah ta juya tana kallon su, a hankali ta koma bayan Dadah ta kifa kanta, tana share kwalla.
"Beauty! Fito babu abinda zamu miki, ga Nanah ma tana shigowa."
Inji Faruq, tana kallon su baki daya kamar ta sansu amma ba zata ce ga inda ta tab'a ganin su ba,  shigowar kakanta da kuma Maman Naaz, tare da Maman Faruq, yasata kafe su da ido. A hankali ta mike tare da mika musu hannu, kafin su isa inda take ta nime zubewa a gurin. Da kiran.
"Ammyna!"

                Sai da Faruq ya tare ta, ya mai data gado aka shiga dubata, dake abinka da zuri'ar Abdullahi keluarga duk ba a musu gorin likitanci, Faruq ne yaki aikin baki daya, shi masanin computer ne, kuma babban dan kasuwa (irin Mahir din 😉😂😜🤨)

               Bata wuce awa daya ba, ta farka tare da kiran sunan Mamanta tana kuka. Maman Faruq ce ta zauna kusa da ita.
"Kiyi hakuri! Amma yanzun kina cikin danginki ne!"

          Kokarin tashi take son yi, suka d'aga ta, kukan da take bawai dan rashin lafiya ko wani abu bane, she is cry akan mijinta ne, tana jin ina ma da zata sake ganin ko yan uwan shi ta gaya musu, ita yar babban family ne.

            "Ya aureta? Kome sai sun sani na sadaukar musu, she take him forever, ni bana son kome kawai ku nimo min shi, ni zan zauna dashi ba zan bar mata shi ba. Wallahi ba zan bar mata shi ba, Ni nasan halin shi. Na gama shan wahala dashi"

Jikin Faruq ne yayi sanyi, matsowa yayi tare da cewa.
"Beauty! Ki manta dashi, Allah zai baki wanda yafi shi."

Kamar wacce ya watsa mata ruwan zafi.
"Ba zan hakura dashi ba, ba zan iya."
"Ke A'isha! Zan zage ki daga kanki har kafarki zanci mutuncinki dan kaniyarki, ke hungo naki. Waye shi da yake saki zubda kwalla, su waye suka kwace miki shi dan Ubansu na saka wando naje naci kwalar rigarsu."

     Cikin kuka ta fara basu labarin, tun tasowarta, har zuwa lokacin da suka shiga takun saka da Shi akan kamfanin shi, har zuwa auren da suka yi, shiru Iyayenta maza suka yi.
"Aikuwa dole ki rabu dashi!"
"Ka kawo shawara Faruq!" Inji Habib,

          Shiru Dadah da Nanah  sukayi basu ce kome ba, kuma fuskarsu ba yabo ba fallasa, tana jin Habib da Faruq suna ta zagin Mahir..
"Kika ce shima Jinin Hamoud Boualem ne?"
Gyada kai tayi, sannan Dadah ta mike daga gadon, tace.
"Ku kai ni gida, Asma'u tawo muje ki Barsu a kanta, ina son magana dake."

              A hankali Nanah ta tashi suka fita.
Tun a mota suka shiga tattaunawa, har suka isa gida. Tare da dauko tsuhuwar wasiyyar mazajen su, suna kuma kara tattaunawa akai. Sannan suka wuni abinsu.

       Bayan tafiyar su, Maman Faruq, rankwashin kanshi tayi tare da cewa.
"Bana son rashin hankali, taya mace da mijinta kace a kashe auren!"
"Mum! Auren fa baki ji ba ayi shi bisa ka'ida ba,.ai kawai ya sake mana yar uwa, yaje can yan uwan shi su bashi yar dangi."
"Wallahi kuwa!"
"Habibullah! Karku yi abinda Noorh zata ji haushinku."
Ita kan bata ce kome ba, sai ma daura kanta da tayi akan cinyar Maman Naaz, tana jin kewar Iyayenta,

               •••
Lagos.
Shiru yayi kallon kullin sharrin da Aysar Haladu da Manager suke mishi.
"Yanzun ya zamu yi da mutane nan?"

      "Babu abinda kudi baya yi! Ka zubawa Manager kudi yanzun zai ƙaryata kanshi."

         Aikuwa haka ce ta faru, bayan awa daya sai ga sabon karya ya fito, inda yaƙe cewa Ai Aysar Haladu da Nazzir sune suka sashi aikata kome akan Noorh,dan haka shi yanzun kwanciyar hankali yake nima,sannan mutuwar agent na NAN. Aysar Haladu da Nazzir ne, suka kashe shi ba iya shi ba,hatta wasu yan jaridun. Sosai ya Bankad'a ashirin su.

       Kallon talabijin din Mahir bai yi ba, ya mikawa Usman Kamfut hannu, tare da juyawa ya bar Office din shi. Daga nan ya nufi Airport. Bai saurari kashedin Ummi ba. Ya gama zarta da abinda ranshi yake so. Ba zai kuma kara koda awa daya ne a kasar ba tare da ya zubawa matar shi idanu ba.

       ......
Washi gari.
Ya isa lafiya, gidan Mr Abdul Fatah Boualem ya sauka, ya sami Mamar Habib tana shiryawa zata asibiti dake bai sami Mr Abdul Fatah Boualem din ba, nan take gaya mishi zata asibiti amma bari tasaka mishi kome, haka ta bada umarni aka mishi duk abinda yake bukata, ita kuma ta tafi.
             Bayan yaci abinci ya huta ne, ya fita zuwa main Family house din su, da yake garin. Duk gidan ya kare kamar babu manyan, kowa ya kama gaban shi.
Nannah ya samu ita da jikokin ta, ya gaida ita, sannan suka d'an tab'a hira har take tambayar shi Hajiya da Maman shi, yace suna lafiya.

      Daga nan ya kira Daya daga cikin jikokinta me suna Mehd, suka fita Mota ya saya, sannan ya bada ita aka mata service.

  Sannan suka tafi a motar Mehd, suna hira a hankali yake tambayar shi about family Abdullahi keluarga, nan yake gaya mishi abinda ya sani da kuma labarin da yaji na Jikar su ta dawo, da irin halin da Noorh ta shiga.

          A birkice ya mishi magana maza ya kai shi asibitin, haka suka nufi asibitin, suna isa.  A bakin kofar shiga asibitin suka bangaje juna da Faruq.
"Sannu!"
Mahir yace mishi tare da shiga cikin asibitin, haka kawai ran Faruq ya b'aci, juyawa yayi ta hango fuskar shi, dake Noorh na fadar musu sunan shi, ya faɗa internet niman shi.

   Cikin murtukekken kishi ya juya, tare da riko kwalar rigarshi, ya shiga jan shi zai fita dashi waje.
"Kai waye da zaka shigo mana asibitin Uban waye kake nima?"
Ran Mahir yayi mugun b'aci, dan haka cikin fushi ya juyar da hannun Faruq, tare da hada shi da Bango, ya bude muryan shi yace.
"Babu abinda ya haɗa Ni da kai, dan haka ka shiga hankalin ka."

Kafin ya kalli yadda mutane suka musu kawanya, juyawa yayi ya takarkace ya kwala mata kira,
Tana amsar abinci ne, amma sai da tayi wani shegen zillo, gabanta yana faduwa.

Da sauri ta sauko daga gadon, yana jin muryan shi yana kara cika asibitin, tana fita ta leka kasa, ta ganshi ya matse Faruq, wanda yake kokarin kwatar kanshi. Hawaye ne yake zuba daga idanun ta.
"Toh ka sake shi!"
Ture shi yayi da sauri ya nufi hanyar da zai sada shi inda take.
"Security ku kama min dan iska."
Kota kansu bai bi ba, ya haura da mugun gudu, haka suka yi ta bin shi. Yana isa gabanta ya tsaya cak yana hakki.
"Idan babu ke rayuwata bata da amfani"
Hawayen da yake zuba daga idanun ta, kawai ya tabbatar mishi tayi kewar shi amma taurin kai irin nata ba zai sanya ta faɗa ba. Hannunta ya kamo ya daura a kirjin shi.
"Kinji yadda yake bugawa!"
A hankali ta zare hannunta, ta juya zata koma ya riko hannunta.
"Me yasa?"
Kwace hannun tayi tare da isa gaban shi.
"Ka tafi! Bana son ganinka, kaje ka karata da Tasleem, kaje na bar mata kai"
"Noorh!"
"Just go!"
"Kinga ni babu wani abinda ya haɗa Ni da."
"Kama aureta kenan, zaka gaya min babu abinda ya haɗa ka da ita."
"Ku tafi dashi."
Inji Faruq,
Ya juyo ta gaban Mahir cikin Izza.
"Noorh hakkina ce na zab'a mata abinda take so, kuma kai kayi expire a gurinta, dan haka ku fitar min dashi."

Dariya ne ya zowa Mahir sannan yace.
"Bari kaga yadda ake gudanar da yaki akan so!"
Ta karkarewa yayi ya zubgawa Faruq naushi, shi kuma bai fahimci dalilin haka ba, ya rama.
"Noorh!"
Yadda yayi kiran araunane kafin ta fito ya kuma naushin Faruq, aikuwa Mahaukacin ku ya rufe Mahir da dukka, duk da Mahir yafi shi, amma ya kyale shi yake jibgar shi.

    Aikuwa jin ana ta ƙoƙarin raba su yasa suka fito.
"Ya Faruq!"
Ta faɗa bakinta na rawa, hango bakin Mahir da yake fitar da jini....🤨🤣😹 Shegen gora me zubda nonon sautu.... Ku sanya Mahaifina a cikin addu'o'in ku bayi da lafiya 🙏🏼

Continue Reading

You'll Also Like

262K 4.4K 62
This is an unofficial fan-made English translation of We are...คือเรารักกัน (We are... we are in love). Please do not re-translate to any other langu...
2.5M 187K 71
RATHOD In a broken family, every person suffers from his insecurities and guilt. Successful in every field but a big failure when it comes to emotio...
86.8K 2.4K 24
Isabella Rose Ivy Valencia-Moretti, the only girl born in Italian Mafia family after so many generations. Not only she is the princess of Italian Maf...
170K 7K 34
အဖိုး လက်ထပ်ပေးခဲ့တဲ့ အိမ်ထောင်ရေးက တည်မြဲပါ့မလား ဂျစ်ကန်ကန် ကောင်မလေးနဲ့ ဆရာ၀န်မမတို့ရဲ့ အလွဲများစွာ....