MAH~NOOR🌹

By AfricanQueen300

87.1K 8.2K 1.3K

Free book I grew up with this, I had best friends became enemies and then best friends again. I love it now... More

Prologue
destinations
Welcome to Hamoud Boualem Company...
Meet Mr Hot Guy
She take my position
Hamoud Boualem Family
Promotion
Personal information
Sisterhood
Big Mistake
Dreams
Interview
MR Arrogant
hateatfirstsight
Courage
My Nikkab
The Name
hypocrisy
Kidnapped
Escape
Injured
Exclusively
Approched
Mine
My Favorite
Silent
You are my Destiny
i'm in luv
Contract Marriage
Confessing
Bonus page
Tracking
stupidly
Chased Game
The Game is Over..
My wife...
Hopefully
Am sorry
Other side
Faruq
Happy end.... Mr And Mrs Mahir Hamoud Boualem
Lover

The Family

1.6K 173 23
By AfricanQueen300


https://www.wattpad.com/1011360729?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=MrsUsman400&wp_originator=mMrIqcxdapq%2FSE7USZjGsb%2FFB1MBG%2Fu4vRbhIbJT5ilQsppeHl47%2FrAaYr311ST49cjr6g20uEIISILnMabOLa4cfYyXh4JH%2F5zPAmCw7u06ldoVSzISbMMN%2FFR4QX8x

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣8️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

        Cikin tsananin tausayi ya kalli Driven, ya shiga gaban motar driven zai magana ya mishi wani irin kallo, dole yayi shiru ya dawo gefen shi, da gudu ya nufi Dr Abdullahi keluarga Memorial hospital.  Kamar zai tashi sama, jin yadda take kananun magana tana kuma tab'a shirmen, Allah kadai ya kai su Asibiti.

                        Allah ya kai su asibitin cikin ikon shi, yana shiga ko parking me kyau bai yi ba, driven ya rigashi fita, tare da kiran a kawo abin daukar mara lafiya.

   Sanin waye yake maganar yasa duk kusan nurse din asibitin suka shiga gaggawan kawo gadon, sabida sanin darajar driven a gurin masu asibitin, duk wanda yake aiki da Familyn Dr Abdullahi keluarga toh ko a cikin gari ne haka zaka samu yana da daraja, sakamakon familyn sun kasance mutane masu zuciyar zinari, masu taimakon na kasa dasu.

      Basu dauki duniya da fadi ba, shi yasa duk wani gwamnati idan aka kafa shi toh sai ya janyo daya daga cikin gidan yayi tafiya da shi.

         Dan haka driven ma ganin ake mishi kamar jinin gidan ne shima, da sauri suka fito da gadon, lokacin yafito da ita a hannun shi yana tafiya irinta asalin jarumai,  kwantar da ita yayi yana kallon Dr Habib.

        "Faruq!"
"Please! Bana son damuwa!" Zurawa gadon da Noorh ido yayi, cikin damuwa da jin wani irin motsi da ran shi yake, wani irin yaja, tare da jin zuciyar shi yana bugawa da sauri da sauri, dauke kai yayi daga kallonta.

     "Ka kira min Ita!"
Wani juya ido Habib yayi sannan yace.
"Wacce kenan?"
Zaro idanu Faruq yayi cikin takaici, sannan ya dauke kan shi tare da juyawa ya bar gurin, yana jin dariyar mugunta da Habib yake Mishi,

Ya fahimci Naaz yake nufi, dake takan shigo asibitin aikin gaggawa.

    Kiranta yayi tare da gaya mata, tazo ana nimanta, sannan ya koma kan Noorh da ake duba,

    Nufar Office din Dr Raliyah yayi,.Yayar shi ce, yana shiga ya gansu tsaye da mijinta suna soyewa ya juyo da sauri, dariya tayi sannan tace.
"Ruq! Ka shigo yanzun Baby zai koma gida"
Buge mata hannu Mijin yayi shima likita ne,.yace mata.
"Liyah! Yau zanje duba Nanah da da daren nan ciwon kafa na damunta."
"Kace mata ta rage shan coffee."
Jan kumatunta  yayi sannan ya sumbaci goshin ta, ya fita.
Gaisawa suka yi da Faruq, sannan ya shigo Office din ta.
"Liyah!"
"Ruq!"
"Liyah!"
"Ruq!"
"I found my heart!"
"Kamar ya?"
"Wallahi daga ganinta nake jin bugun zuciyata ya nunku!"
"Kai Ruq!"
Tayi maganar tana zaro ido, zama yayi tare da mika kafar shi saman table din ta.
"Raliyah, Wallahi ita nake so! Zan iya rushe wancan tsohuwar al'adar auren zumuntan nan domin yarinyar tayi min!"

"Faruq kai da aka maka baiko da Naaz!"
Kamar wani shine zama da ita ya mike kamar zai buge ta,
"Ba zan yi auren zumunta ba! Nace miki Yanzun na tsinci abinda Zuciyata ta jima tana nima Ni bana son Naaz yarinyar bata min ba, dan haka karki dame ni da wata naaz"

     Sake baki tayi sake tana kallon shi.
"Amma kasan Nana da Dadah sun gama magana, yanzun ka bijiro da wata shirme, sannan ita wacce kake so yar uban waye!"
Dafe goshin sa yayi tare da lumshe idanun shi, sannan yace.
"Bugeta muka yi."
"Ruq! Dama daga muje na ganta."
Ta fito a fusace, a bakin kofar suka gamu da Naaz da idanunta yayi jajjur, cikin fushi ta juya fuuuuu.
"Wallahi kika bar asibitin nan baki duba min mara lafiya na ba, sai na baki mamaki a dare nan."
Cak ta tsaya, sannan ta juya tana kallon shi, cikin wani irin takaici.
"Kai waye? Ce maka aka yi ina son wannan yanayin naka ne?

Ina da wanda nake so yafi ka kome."
"Muje naga mara lafiyan?"
Dole ta hakura da masifar ko kallonta bai yi ba, kasa kasa yace mata.
"Abi wani sarkin ba dai ni ba."
Kamar ta fashe aka take ji, dan haka taje dakin da Noorh take daga nesa ta hango fuskarta.
"Laaaa!"
Da sauri ta ciro wayar ta, ta shiga kiran Number Dadah, ta gaya mata, ai ga Noorh. Tuni ta manta da fadar da take ji a ranta.

     Abin mamaki, su kansu tsayawa suka yi suna jin sai kiran  iyayen su take tana gaya musu ta samu Noorh, kafin minti talatin asibitin ya cika makil, Dadah na shigowa, daga nesa ta shiga gyada kai kamar kalangariya,.
"Na fada! Aka ce min wai ta mutu! Dube ta don Allah duk wanda yaga Fuskar Salha yaga fuskar yarinyar nan ya san nata ne, kamar ce ta Likita."

   Haka take kiran mijinta likita, kafin kuma ta fashe da kuka, ta matsa kusa da Noorh, tana shafa kanta, kuka anyi juyin duniyar nan tayi shiru taki, wai tana kukan mutuwar iyayen Noorh.

"Idan baki yi mana shiru ba! Zaki  bar asibitin nan!"

"Toh ja'iri mara kunya da idanu kamar na kifi, banza da uwar kai kamar uwar yaki, rankwal rankwal. Idan ka fasa kai Ni gida ka rena Ubayenka nan, dan banza da fuska kamar burodi, dama ina cike da kai rashin mutuncin da kayiwa Naaz wancan lokacin kasaka min yarinya a daki ka gama kwashe mata albarkacin jikinta dake kai din tantirin mara kunya ne kake gaya mata me zaka yi da ita?

               Ummaru kafita idanuna ko kaci kan Ubanka, aure da naaz kamar anyi an gama dan kan Uban a gurin kana zuru zuru da idanu kamar, wanda ya had'iye kunama."

      "Dadah Asibiti ne ba a son hayaniya."
"Gafara can, sakarai mijin tace. Dan banza mara kunya kai ma ina jiran na kama ka, wato har nice wancan matar taka me kugu kamar an sawa katako riga, shine ta ganni ta dauke kai Habibu Ni, Rafi'a taci mutuncina wannan yarinyar Allah sai na ci mutuncin ta a gaban Nana. Yar banza da idanu kamar tsitaka. Yar banza da dogon baki kamar shantu."

           "Hajiya Dada.."
"Rahila kike ki Rahiya, Raliya. Ke ohonku ko taliya kike ba zaki hanani magana ba, yau naga shegentaka, kai ba asibiti nake ba a mutuware nake, kar wani yayi min rashin kunya na ci mutuncin shi."

   Babu wanda yayi magana, Dr da sunga ana fama da Noorh, ana ta gyara mata ciwon dake jikinta, bai hana Dadah yatsina fuska ba tace.
"Kai Likita, haba wannan wani irin rashin Imani ne haka da rashin mutunci? Ka sami kafar yarinya sai darja mishi magani take, dan banza da fuska kamar fanke."

            Shiru tayi tana kallon, suna gurin wata Noorh ta fito da hanzari zata lab amso jini. Kallonta Dada tayi sannan tace.
"Ke zo nan! Nurse din ta tsaya.
"Na'am Hajiya gani!"
"Kinga yarinyar da take kwance! Toh jika na ce, yanzun shekaru goma sha kenan rabona da ita, kinsan me yasa na tsayar dake?"

Girgiza kai Nurse tayi,
"Ba sai kin girgiza min kai ko gyada min kai ba, domin naga kalangaru, idan kuma rantalelliyar kai ce baki kai wancan Jikar nawa ba, dube shi da kyau!  Toh abinda yasa na tsayar dake da Magana!"

    Gabaki daya gurin babu wanda bakin ciki bai kama shi ba, domin ji suke kamar su mata mugun duka,
"Toh ba kome bane sai dan naga kin fito da sauri, karki yarda rawan kanki ya kwashe ki, ki tab'a min jika, domin zan saka a kwab'e min na miki shegen duka!  Ko kuma nasaka wancan me k'ugun kamar anyiwa sauro zanzaro!

              Yayi miki shegen duka, dan haka kiyi tafiya jantil, no pas."

      Dake taga duk familyn Dr Hisham Abdullahi keluarga, sai ta shiga gyad'a kai kawai.

          Har kusan asuba, babu wanda ya bar asibitin, wasu daga cikin familyn ma da suka ji labarin suma likitoci ne duk suka zo, Dada nakan abin sallah dake mace ce mai yawan ibada ce, dan haka ta raba daren tana kai kukanta gurin Ubangiji.

           Har suka tafi Sallah asuba suka dawo.
Suna shigowa, Naaz da sauran likitocin suna fitowa.
"Alhamdulillahi, tana barci yanzun haka."

Inji Naaz,
"Ke yar nan! Ya jikin nata?"
"Dadah da sauki fa, kuma ma cikin jikinta shima lafiya yake. Karkiga yadda yake juyawa."

               "Alhamdulillahi! Kai Jama'a yau gani ga Yar Umar dina." Jikin shi ne ya kuma sanyi dan tun jiya bai Fahimci me yasa suka tawo da wayar da aka yi da Dadah ba, sai ya kuma tambayar su.aka gaya mishi Noorh yar takwaran shine Kawun shi Omar da ya rasu da Aunty Kanwar Maman shi,.Salha, wani irin murmushin jin dadi yayi, zubawa kofar da aka fito da Noorh yayi yana murmushi tare da shafa kanshi.
"Toh cikin jikinta fa?"
"Tayu da aurenta!"
      "Eh domin ranar da zata bar asibitin naji kamar tana cewa. Sun dauke mata shi. Sun rabata dashi ta hakura dashi kawai"
Wani irin murmushi Dadah tayi cikin jin dadi,
"Kunga yarda aka haifa tsiya na barci bai rab'e ta ba, balle tayi mutuwar zuciya. Irin naso ooo namijin na miki tsiya ajiye mishi abincin shiki tawo abinki, babu dole shima dan banza zai zo ya same Ni......
Please And Please... Kuyi min Uzuri, naso sai monday  zaku ji ni,toh ga wannan ku tab'a babu yawa, muna hidimar sauka ne, gashi dole zaku yi min hakuri gaskiya sabida wallahi babban lalura ya tawo min ba zaku naji na na sai.bayan kwana biyu

Continue Reading

You'll Also Like

375K 39K 21
انا العاصفة الحمراء ألتي تراهن وتربح انا القوة العظيمة الذي سوف تنهك كُل الارواح الجنون والتلاعب بحد ذاته هنا أستطيع ان اتلاعب بعقلك حَد الجنون امر...
85.2K 6.7K 60
ရယ်စေ၊ မောစေ အသက်ရှည်စေ ဟာသနှော၍ ရယ်မောပျော်ရွှင်စေရန်အလို့ငှာ လုလင်မောင်မောင်(ပစ်တိုင်းထောင်) နေမင်းပုည(ရွှေဒင်္ဂါး) (Own Creation) Starting Date...
71.1K 3.4K 39
An arranged marriage between two contrasting yet similar people. Will it work? Urwa Shah A nineteen year old girl filled with dreams. A strict...
217K 17K 22
On Hold Wanna visit rajasthan than read this special book about my love Rajasthan 💗