MAH~NOOR🌹

By AfricanQueen300

87.2K 8.2K 1.3K

Free book I grew up with this, I had best friends became enemies and then best friends again. I love it now... More

Prologue
destinations
Welcome to Hamoud Boualem Company...
Meet Mr Hot Guy
She take my position
Hamoud Boualem Family
Promotion
Personal information
Sisterhood
Big Mistake
Dreams
Interview
MR Arrogant
hateatfirstsight
Courage
My Nikkab
The Name
hypocrisy
Kidnapped
Escape
Injured
Exclusively
Approched
Mine
My Favorite
Silent
You are my Destiny
i'm in luv
Contract Marriage
Confessing
Bonus page
Tracking
stupidly
Chased Game
The Game is Over..
My wife...
Hopefully
Am sorry
The Family
Faruq
Happy end.... Mr And Mrs Mahir Hamoud Boualem
Lover

Other side

1.8K 200 42
By AfricanQueen300

https://www.wattpad.com/1010638382?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=MrsUsman400&wp_originator=t2vwVWQ6R91YNEa2KNee5i420PyN1JrEhumbRRqCRdz5YTOoQL1ZJLcrISZd7lMQcvWlnV4CA9a9pOvRLjzx5TfDagW0gPV2qQkotFhqHb6BOKq1Bu9MEnMI16fJUADn

MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣7️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

_Alhamdulillahi nagode sosai, daga duk inda kuke ina mikawa Fans din Mahnoor gaisuwa na Nagode da addu'o'in ku_

  *Ina mika sakon ta'aziya ga Aunty Mami wacce tayi rashin yar uwarta, tare da Maman Sultan wanda ta rasa mahaifinta, Allah ya jikan rai ya kuma gafarta musu, ya kyautatta namu bayan su*
"Ummi don Allah ki rufa min asiri, wallahi zuciyata zata buga, nayi iya hakurin da zanyin please i need my wife" banza tayi dashi, ta cigaba da aikin ta,kamar bata san da abinda yake rokonta ba.

    "Amma Maryam!"
"Hajiya don Allah karki saka baki akan wannan al'amarin, Ki kyale ni da MUH'D!" Ummi ta katse Hajiya,
Shiru tayi tana kallon yadda Mahir ya tara kasumba da uwar gemu.
"Kai dalla can, tashi kaje ka gyara kanka, ka wani zauna buzu buzu da kai sai kace me cutar hauka!"
Inji Hajiya, "Hajiya nifa ba zanje ko ina ba, kawai Ummi ta gaya min meye nufinta da aurena da Noor?"

Cak ta tsaya da aikin da take a kan laptop, ta juya tana kallon shi, bata ce mishi kome ba, ta juya tare da wurga mishi takardan.
"Ka aureta ba bisa son ranta ba, kayi ta amfani da ita ba bisa ka'ida ba."
"Yanzun Ummi Noorh dince ta gaya miki haka?"
Dakuwa tayi mishi, da hannu bibbiyu, tare da mishi alamar da yana kusa sai ta watsa mishi mari.
"Kaniyarka, da zaka zo kusadani sai na maka shegen duka, meye ba zata fada ba, kasan irin kukan da take yi idan ta tuna ta rasa duk wani abinda akewa yar gata sabida rashin hankalin da kayi mata?

           Kasan dalilin da yasa tayi ta maka borin bata son zaman nan, tunda taji labarin wacce aka yi aurenku tun farko, tuni kishin ka ya gama turmusheta, mara kirkin mutum kawai, yarinyar nan haka ka aureta ko dan irin abubuwan al'ada babu, ka gama rena mata hankali, da cewa mafarki take, toh Wallahi ta gaya min rabuwa zaka yi da ita na gaya maka."

       Mikewa yayi cikin jin haushi da b'acin rai ya ki kula takardan da zai saka hannu, ya saki Noorh.
"Wallahi indai ana daura igiyar aure sau dubu, toh na kuma damke auren Noorh akaina, naga wanda zai yi wannan aikin amma ba dai ni ba!"

Ya juya fuuuuu, kamar zai yi hauka sabida yana matukar son matar shi, kuma baya jin zai iya sake ta.

    Kallon ta Hajiya tayi, tare da cewa.
"Nasan yadda yarinyar ta koma gurin yan uwanmu, toh wallahi ina tausaya mishi, domin matukar ta isa hannun Hajiya Dadah toh wallahi ina tausaya MUH'D don kuwa."

    "Hajiya na fahimci haka shi yasa nake kokarin na koya mishi, yadda zai jure abinda zai biyo baya, domin bana manta lokacin da Ubaidullah yayi faɗa da Su'ada, yadda kowa ya juya mishi baya, gasu yanzun har da Yarinyar da ake shirin aurar da ita Dr Naaz, kuma ban san Baban Noorh ba sai shi kawai na sani da Abubakar da Dr Hisham Abdullahi keluarga."

    "Kin san Umar yaki zaman algeria ne, aiki da china da kuma turawa ya hana shi zama, rabon Noorh da yan uwanta ya dawo dashi daga china koda aka yi auren haka ya tafi ya barta, sai da yayi shekara biyu ya dawo ya tafi da ita,  ita tanka zo duba dangi, Kinga yaje algeria kenan yazo nigeria, dan shi Dr Abdullahi keluarga yaki ya bar yaran shi anan Nigeria, itama Dada da take yar Nigeria yaki barinta zuwa akai akai, kakan wancan Yarinyar masu shegen son abun duniya suka zauna anan din." Ta wani bi gefenta da harara, zaka zata Tasleem din tana gurin ne zunzurutun tsanar da tayiwa Tasleem din ne kawai.

        "Amma Amma Hajiya wacce irin dangantaka ce a tsakanin ku dasu Noorh?"
Ajiyar zuciya tayi sannan tace.
" Boualem Da Dr  keluarga, ya'yan mace da namiji ne kamar dan Mahir da Dan Hidaya, Ni bana son Boualem, aka bani shi domin Keluarga yaya nane uwa daya Uba daya, shima an bashi Kanwar Boualem Mai suna Hafsat amma ita basu jima ba Allah yayi mata rasuwa, dan haka yana cikin jimamin mutuwar ya sami aiki da gombe, ya anan ya hadu da A'isha, kasancewar yayi auren gidan yasa ba a mishi iyaka da auren A'isha ba, amma dukkan mu dangin juna ne, kuma Bama cika auren bare daga farko sai yan gidan, nima da zamana yaki da Boualem shine aka raba auren, daga baya shima Hamoud zaman cikin gidan su, ya hana shi sukuni ya tattara ya dawo nan kasar da zama, dan ya fahimci hankalin shi zai fi kwanciya, lokacin da ya gaya min ban hana shi ba, dan nasan babu mamaki Arzikin shi ne yake kiran shi, ashe har da rabon haduwa da mutuniyar Arziki irinki"

    Shiru Ummi tayi, sannan tace.
"Ikon Allah, kiga yadda Ubangiji yake alamarin shi, gashi kuma Allah ya hada wannan al'amarin cikin sauki"
Murmushi Hajiya tayi sannan tace.
"Tace eh mana, kuma Kinga abinda Noorh take haka Yayana yake yi akan gaskiyar shi, shi yasa yaki zaman Nigeria domin bai iya boye abu ba, asalima mutanen Unguwar mu shakkar shi suke."
  
  Gyara zama Ummi tayi tare da kallon hajiya, sannan tace.
"Toh takwaran Muh'd ga"
Shiru tayi sannan tace..
"Mutum ne me waddatar zuci, yana da hakuri sosai, sannan yana da matukar kokari wajen ganin ya bawa kowa damar yin abinda yake so, mutum ne me ra'ayin kowa yayi abin da yake so, shi yasa mutane suka yi ta mishi abinda zai b'ata mishi rai. Mutumin nan zan iya cewa bakin cikin mutane ya kashe shi domin ba iya yan uwan shi ka dai suka dauki alhakin shi ba!"

           Yadda take bada labarin Kakan Mahir sai ya baka tausayi,. Dukda kuwa auren kiyayya ce, amma ta fadi Quality na halayyar shi, mutum ne me matukar kirki da hakuri da jama'a, ta fadi abubuwa dayawa wanda tace kafin ya rasa yasa an kirata ya gaya mata fushin da Baban Mahir yake dashi dan ya gaza mishi adalci, yarinyar da zai aura, Dan uwan shi Hamid ya dauke ta ranar auren shi da  Safoor. Kuma mahaifin bai magana ba, shi yasa ya bar musu gidan gab mahaifin shi zai rasu ya koma gida.  Ta gaya mata abubuwa da yawa akan Familyn ta dana su kakan Mahir. Kafin suna tashi.
    •••
Yallabai mai kan mint kuwa da uwar kai kamar kusan yaki, yana barin gidan Ummi, gurin Usman Abokin shi ya nufa anan yake gaya mishi abinda Ummi tayi mishi, sai masifa yake, tare da cewa matukar ta raba shi da Noorh toh tabbas mutuwa zai yi.

Shan soda drink Usman yayi sannan yace.
"Don Allah akwai wani guba, idan zaka mutu kazo na baka yana taimakon kashe mutum da wuri kaji"
Cikin masifa ya juya yana kallon shi baki sake yana faɗin.
"Meye nayi maka na rashin mutunci haka? Nazo da damuwa na kana gaya min maganar banza"

      Yadda yake magana zaka san zuciyar shi a harzuke yake da abinda Ummi tayi mishi, ya zo gurin shi domin ya fahimci abinda yake ji, ya kuma kara tunzura shi, mikewa yayi cikin fushi ya kuma fita daga Office din Kamfut, har ya kusan fita waje Kamfut yace mishi.
"Mijin Indo Indo! A kai zuciya nesa shugaban yan zafin rai, a sha ruwan sanyi don Allah kar ace."

"Wallahi zan danna maka ashari'a!"
"Toh jinin maguzawa, ALLAH ya kare ka don Allah ayi tuki a hankali, Noorh kan idan ka sheka lahira aure zata kuma yi miji gangariya wanda kunamar shi yake harbawa."

A fusace ya kuma dawowa ya shake wuyar Kamfut, jikin shi sai rawa yake, idanun shi yana cika da kwalla.
"Lion Man sauke ni, wallahi wasa nake maka, bana fatar ka mutu ma balle ka rasa Noorh, don Allah sake min wuya na." Sake shi yayi tare da barin Office din shi baki daya.

Girgiza kai Kamfut yayi yana girmama soyayyar da Mahir yakewa Noorh.

         Yadda Ummi ta kafe, tare da nacewa Mahir sai ya sake Noorh sai ya baka tausayi, yayi juyin duniyar nan tayi hakuri fir taki, ta kuma mishi gargad'in karta ji karta gani  ace ya bar ƙasar. Duk inda Noorh take tasan tana hannun danginta. Haukar da yayi ta mata babu iyaka. Tana sane dashi tayi banza dashi.

       Yan uwan shi kuwa, baya ta su, Shibha yake kulawa itace ke mishi hirar Noorh, itama ranar da Ummi ta kamata sai da taja kunnenta kamar zata cire mata shi. Dan haka ya kuma kowa cikin kaɗaici sosai. Tausayin kanshi da irin rayuwar da Noorh tayi ne ya kama shi, zai ci zai sha sai dai bai da nutsuwar zuciya.

             •••
Algers..
A bakin wani gindin gada take kwana, da zaran taji karar motar yan sanda zata shige kasar gadar ta boya jikinta wani lokaci har rawa yake, zunzurutun tsoron karsu kuma kaita gidan mahaukata.
Tana kwance aka fara ruwan sama, dan haka ta tashi zaune tare da kallon gyambon kafatarta. A hankali taja wani tsuma ta shiga daure kafar, jin motsin a cikin ta yasata sake wani irin ajiyar zuciya, tare da dafe cikin da ya taso, sake motsawa cikin yayi ta kuma dafe shi tare da sake murmushin jin dadi.
  Cikin harshen larabci tacewa cikin.
              "Marhaab!"
      (Barka dai)
Sake motsawa yayi,
      "Kaifa anti?" (Ya kike)
Sake juyi cikin yayi tare da wani katon kutufu, aikuwa ta sake dariya tace.
"Lastu bikhair"
(Bani da lafiya)
   Ta faɗa cikin zubda kwalla, tana kallon ciwon kafarta,
Juyin da cikin yayi tace.
"Wa'anti?" (Kefa)
Juyi ya kuma tace.
"Alhamdulillahi!"
Dan karamin juyi yayi tace mishi.
"Laa Shukrah laki?"
(Ba sai kinyi min godiya ba)
Shiru cikin yayi bai kuma motsawa ba, ta tab'a cikin tare da dafe shi taji yaki motsi,
"Bint! Bint! Bint!!!" Ta faɗa da karfi amma cikin bai ko motsa ba, da sauri ta fito daga inda take ta nufi hanyar cikin gari tana ihu duk da dare ne, ita lallai sai Bint tayi magana.
  Dakyar ta tsaya a gurin wata mai sayar da abinci, ta isa gurinta cikin kuka tace mata.
"A yumkinunil julusa huna?"
(Zan iya zama a nan?)
Gyada mata kai tayi cikin tsoro, tare da niman hanyar arcewa.
"Bint!" Ta cigaba da kiran babyn cikin ta da kuma girgiza ta.
"Ma'usmiki?"
(Me sunanki) matar ta tambayeta?
"Ismi Noorh?"
(Suna na Noorh?"
   "Min aina anyi?"
(Daga ina kike?)
Kallon matar tayi cikin wani irin tsoro,
"Ana min...?"
Mikewa tayi da sauri ta bar shagon Matar, wacce take kokarin kiran yan sanda, ta bazama da gudu, ko gabanta bata gani, yadda take gudu akan titi ga uban ruwan saman da ake, ko gaban. Bata gani bata kuma san waye yake zuwa daga bayanta ba. Babban burinta ta koma maboyinta. Sai dai kash, taka birkin da kuma duke bayanta da driven shi yayi ya tsayar mishi da aikin da yake yi lokacin gudu, ya sanya shi d'ago kai.
Cikin sansanyar muryan shi yace.
"Fa'iz!"
"Ya sayid!"
"Ka kula me ya faru?"
"Sayid ina gani kamar hatsari ne muka yi!"
"Shi yasa bana son kana wannan gudun. Ka fita ka duba mana wa ka buge"
Lema ya dauka cikin sauri ya fita, hangota yayi tana ja da cikinta, da sauri ya juya cikin motar yana fadin.
"Na shiga uku na lalace, Ya sayid na na buge mahaukaciya ne"
Dafe goshin sa yayi tare da bude motar ya sauko da kafar shi daya sannan ya fito baki daya, hango yadda take ja da cikin ya matukar girgiza shi, cikin sassarfa ya isa gurinta, tare da ɗaukar ta, bakin shi kunshi da addu'a, driven ya bude mishi motar ya sakata, yarda kai kawai take, amma tana mugun jin jiki.... Har yanzun jikin da saura so kuyi hakuri, karfin hali nayi kawai...

Continue Reading

You'll Also Like

2.1M 105K 56
Rehan's mother is a typical Indian mother, who wants to get her son married before he turns 28. And also she doesn't want him to marry his cunning au...
404K 41.6K 23
انا العاصفة الحمراء ألتي تراهن وتربح انا القوة العظيمة الذي سوف تنهك كُل الارواح الجنون والتلاعب بحد ذاته هنا أستطيع ان اتلاعب بعقلك حَد الجنون امر...
73.6K 3.6K 40
An arranged marriage between two contrasting yet similar people. Will it work? Urwa Shah A nineteen year old girl filled with dreams. A strict...
125K 8.9K 64
ရယ်စေ၊ မောစေ အသက်ရှည်စေ ဟာသနှော၍ ရယ်မောပျော်ရွှင်စေရန်အလို့ငှာ လုလင်မောင်မောင်(ပစ်တိုင်းထောင်) နေမင်းပုည(ရွှေဒင်္ဂါး) (Own Creation) Starting Date...