MAH~NOOR🌹

By AfricanQueen300

85.4K 8.1K 1.3K

Free book I grew up with this, I had best friends became enemies and then best friends again. I love it now... More

Prologue
destinations
Welcome to Hamoud Boualem Company...
Meet Mr Hot Guy
She take my position
Hamoud Boualem Family
Promotion
Personal information
Sisterhood
Big Mistake
Dreams
Interview
MR Arrogant
hateatfirstsight
Courage
My Nikkab
The Name
hypocrisy
Kidnapped
Escape
Injured
Exclusively
Approched
Mine
My Favorite
Silent
You are my Destiny
i'm in luv
Contract Marriage
Confessing
Bonus page
Tracking
stupidly
Chased Game
The Game is Over..
Hopefully
Am sorry
Other side
The Family
Faruq
Happy end.... Mr And Mrs Mahir Hamoud Boualem
Lover

My wife...

1.8K 167 28
By AfricanQueen300

https://my.w.tt/S20XewskWcb
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣5️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

      Zuɓewa yayi a kasa, ranshi na kara dugunzuma, wayar cajin laptop din shi ya ja da ƙarfi.

Ya nufi gidan Ummi cikin tafasasshen zuciya, yana shiga cikin gidan, sun zauna suna mai da yadda suka kori Noorh, ya shiga dukar su kamar hauka, ya gigice. Ya fita hankalin shi dukar su yake Hajiya da take d'akinta sai da ta fito, bai kulata ba.

Yana cikin wannan lamari, Allah ya kawo Ummi, rike Hannun shi tayi.
"Me yasa ba zaka nutsu ba!"
Bakin shi cike da iska, ya rasa yadda zai yi yace.
"Sun koreta? Ummi wallahi idan ban gan mata ta ba, Ummi tab'a kirjina, zuciyata kamar zata buga. Ji yadda yake bugawa.

      Ummi daga ranar da ta fara min rashin kunya naji Allah ya kawo min matar da nake so ne! Ummi Duk cikin matan da nake gani kowacce shakkar gaya min magana take, Ummi Har yau Noorh bata bude bakinta tace ina sonka ba Mahir. Ummi yaushe zan sami mace irinta? Macen da ta kalli idanunka ta gaya maka abinda yayi mata.

    .wasu suna son mace me kunya hakuri kawaici, Ni mace me zafi nake bukata, macen da zafin kanmu zai zama daya. Macen da babu wanda ya isa takata. Ummi yau sun koran mun mata na da cikin jikin ta, Ina laifin su bari ta haihu, amma basu yi wannan tunanin ba! Suka shirya min karya tare da kore min matar da nake so. Ummi bayn yarinyar da muka gamu a jirgin kasa, Ummi har yau ban kuma ganin me kama da ita ba, sai Noorh.

           Ummi dubu sau dubu, na kome da na mallaka, idan za a ce na zab'a dashi da Noorh zan zabi Noorh na bar kome, Ummi ba zan iya rabuwa da Noorh ba dan su, Amma Ummi idan kika ce na rabu da ita, zan iya hakuri da ita."
  Bata ce mishi kome ba, ta amshi bulalan ta wullar sannan ta wuce kitchen ta debi ruwa ta mika mishi ya sha, wani irin ajiyar zuciya yake saukewa a kai akai.

Da gudu ya nufi dakin Noorh na gidan, bai sami kome ba. Sai awarwaron Zinarin Ummi, jikin shi a sanyayye ya sauko,  kallon hannun shi Ummi tayi.
"Baba na,.a ina kasami wannan awarwaron?"
"Na mahaifiyar Noorh ce?"
Amsa tayi tare da juyawa zuwa sama, kallon inda take ajiye nata tayi, ta ciro su.. guda biyu,

A hankali abinda ya faru, shekaru goma sha biyu suka shiga dawo mata, da lokacin da ta cire a hannunta, ta mikawa Mahaifiyar Aisha. Wani irin sanyin tausayin yaran guda biyu ne ya dira a zuciyarta, yau itace ta rike! Toh ya batun wancan Aishan? Lokaci guda lissafin ya dagule mata.

      A hankali ta fito, tana kallon shi.
"A ina kasami Noorh har ta baka wannan awarwaron?"
A hankali gaya mata, kome jikin yan uwan shi mata, ya mutu.

Zuɓewa yayi akan gwiwar shi, kukan da yake tarewa ne, ya fashe da shi, cikin muryan kuka ya d'ago kai yana bata labarin matsalar Noorh,
"Zata tafi kasar da bata san kowa ba, idan yawan jama'a ya cika mata idanu, ciwonta niman tashi yake, har kuna da bakin zaginta Mahaukaciya?

         Kunsan wacece Noorh? Toh ita din Jinin abdullah keluarga ce, itama jinin mu daya, mu jinin  Boualem ne ita kuma abdullah keluarga."
Yadda yake fadar asalin Noorh, sannan yace musu.
"Yayan Mahaifiyar ta, shine Shugaban sojojin ƙasar Algeria.  Noorh kaddarar muce ya kawo iyayenta. Amma Noorh mata ta ce! Jikar Sheikh Bin Abu Turab, ce fa"
    Yadda yake bayanin alaƙar su da nasabarsu da Noorh abin tausayi ne, tashi yayi cikin tashin hankali.
Ummi! Yau zan raba dukiyar mu kowa ya dauki nashi, amma bazan iya cigaba da kallon wadannan mutanen a matsayin yan uwana ba, sabida su na rasa mata na da cikin jikinta."
.daga haka ya saka kai zai fita.
"Kul! Naji ko na gani ka tab'a wani abu na amanar da Allah ya baka, babu yadda ka iya dasu. Amma idan ka barni da su Zan hukunta su dai dai da laifin su.

         Tun kafin kasan Noorh nasan daga inda ta fito, domin itace matar ka ta farko! A'isha da muka daura maka aure da ita, Noorh dinka ce, wannan shine sadakin ta na farko, da nice na bawa Mahaifiyar ta, ban tab'a jin zafin abu idan aka yi kamar yadda naji zafin abinda suka yiwa A'isha Omar Abdullahi keluarga, Allah ya gani naso ta, kuma ina mata son y'a da uwa ce,.dan haka ba zaka bi bayanta ba.

      Sai ka gurfanar su Mutanen da  suka shirya hatsarin jirgin kasa, sabida kai da Mahaifinka.

        Saboda alƙawarin Cigaba da hada zuri'a tsakanin  Hamoud Boualem da zuri'ar Abdullahi keluarga, aka shirya babban hatsarin jirgin kasa, duk dukda lokacin ban san kome akan haka ba, sai zuwan mahaifinku Algeria, yake gaya min familyn  sunyi fushin auren yar wata ƙasa da yayi, dukda kowa yasan yadda suke hada auren dangin su.

    Dan haka, suka ce suna da yara mata a cikin zuri'arsu, ya zab'a maka wacce ta dace da kai, bai yi kasa a gwiwa ba, yace duk wacce ka zab'a tayi mishi, amma ayi hakuri idan kazo da kanka zai fi.

         Dan haka lokacin da muka je da kai bayan gama secondry school dinka, kace baka ga wacce tayi maka ba, dan haka Tsoho Abdullahi keluarga, yace ya zab'a mata wacce yake da yakinin duk rigimarka dole ka tayi maka,  dan haka, yake cewa akwai yar Dan shi Umar a Nigeria, kuma suna zama a lagos, Noorh. Yana ganin zata  dace kai. A lokacin mahaifinka ya bata kyautar kamfanin ka na garin Yola,.duk da bamu ganta ba, sai gashi ƙaddara ta kuma hadamu duk da bamu san ita bace,muka daura auren ku da wasa. Bakin cikin bata kamfanin shi ya sanya akayi ta sanadin da zai lalata sunan mahaifinka sakamakon ba ayi hadin auren da Zoolfah ba, jin zafin haka yasa aka shirya hatsarin jirgin kasan, sai kana raye za ayi auren ku da ita. Haka kuma mahaifinka sai yana raye zai tabbatar da kamfanin Hamoud Boualem ya zama na Noorh.

       Na jima ina addu'a Allah ya bayyana min wanda zai ruguza zalincin da ake a kamfanin, Sannan wasan Chased da kuka yi, an shirya kashe mu ne, na samu labarin haka ne, ta bakin abokinka Usman Kamfut, sannan muna maganar Noorh ta tabbataar min da haka,ta hanyar amfani da wata na'urar da ta saka a jikin zoben yatsar shi."
.haka tayi ta bashi labarin. Abubuwan da suka gabata, wanda banda karfin Ikon Allah babu wanda ya isa ya tabbatar da haka. Sai Allah, kenan dama can tuntuni akwai maganar aure a tsakanin su. Shi yasa ya mayyance mata. Ashe shi din mayyenta ne.

            Dan haka ya mike tare da barin gidan, su kuma Ummi cin mutuncin su tayi tare da musu gori da shiga tsakanin su da Tasleem, dan sai bayan sun zo Lagos ta sami labarin waye su. Dan haka take kokarin sallamar su, tunda ga yar masu gida, ina zata zauna da bare. Kuma dama Hajiya ta gaya mata Noorh tana kama da d'an uwan ta, da matar shi labibah. Domin kwayar idanun Noorh sak na yayan Hajiya ne.

      (Toh anya familyn su nan toh muje zuwa)

         ---
Tasleem tana makale, da Nazzir dan iska, sai gurgureta yake iyayen ta suna gidan Nazzir. Ita kuma Tasleem tana tare dashi ana kuma shirya yadda zasu gama da Ahalin Mahir idan akan aura mishi Tasleem. Dake dakikai ne, take suka bada haɗin tare da amsar tulin dukiyar da aka basu.

         Mahir yana can tare da hada shaidu, ya kuma dawowa gidan ya gayawa Mahaifiyar shi abinda zasu yi, tare da saka ranar da za ayi baikon su akan lokaci. Duk da haka zuciyar shi yana ga yar matar shi, gaba daya yana jin kamar tana cikin tashin hankali da matsala.
    •••
Ta isa tripoli lafiya, sanan ta wuce kasar Libya lafiya, inda gizo ke saka, sai a kasar Algeria.

     Inda screening farko, aka sami bindiga da hodar iblis a cikin jakarta, wani irin zufa ne ya shiga karyo mata, ta fara zare ido. Cikin tashin hankalin da bugun zuciya tace.
"Wallahi ban san da su ba, wallahi ban tab'a aikata laifin haka ba."

Haka suka kira yan sanda aka fitar da ita, tare da wuccewa da ita Office din yan sanda, ana kaita suka rufeta da mugun dukkan, tare da lallai sai ta amince da ta aikata laifin, sun dake ta ainun tare da azabtar da ita, sannan suka ce lallai sai ta amsa laifin da ake zargin ta dashi. Taki amsawa, karshe cikin ne ya fara zubda jini. Haka ya sanya ciwonta tashi fiyye da baya ma.

      Ganin yadda take zubda jini ne ya sa suka mikata asibitin kula da irin su. Ihun da take tare da hauka tuburan sai da ya tab'a zukatar mutanen da suke kula da lafiyar su, musamman da take kukan kar wani abu ta sami babyn ta,  idan ka ta Noorh sai ta baka tausayin sabida yadda ta haukace sama da baya, dakyar ake kula da lafiyar ta, cikin kuwa wata Dr Naaz ita ce take iya kula da lafiyar ta, domin tunda ta amshi ragamar kula da ita, take bincike akan ta. Kuma itama tunda ta likitar take sakewa da ita. Amma idan haukar ta motsa fa, sai tayi Mata alluran barcin suke mata aikin kula da lafiyar cikin jikinta.

    Da farko kun zata cikin ya zube a can asibitin, dan haka suka shiga bata kulawar matsalar haukarta, cikin kwarin gwiwar samun lafiyarta.

    Amma cikin kwana biyu kacal suka fahimci cikin yana nan, dan haka suka shiga mata alluran barci sabida cikin ya koma mahaifar ya zauna..
     ---
Zama tai tana kallon iyayen ta, da suke tattaunawa akan case din shigowa da makamai tare da miyagun kwayoyi.
"Yanzun kaga wanda aka kama yarinyar mana, sun tabbatar saka mata aka yi, sannan kuma sunce tana fama da tab'in hankalin "

     "Eh aikuwa Ammah yarinyar tana gurina, domin nice ke kula da lafiyar ta!"
"Me kika fahimta da ita Yarinyar?"
"Abbu! Yarinyar bata san kome ba, sai tana yawan magana da harshen Afrika da kuma English, gaskiya babu alamar tasan abinda yake faruwa ma, sabida tana fama da cutar hauka!"

     "Naaz! Kuma kika ce bata san kome ba?" Cikin gajiya da tambayar da su tace.
"Ammah yarinyar ba tana cikin hauka amma bata kaunar taga jini a jikinta, tayi ta kuka tana kiran Mahir! Babyn su yazo kar ya bari ya zube kuma ya mata hukumar kare hakkin dan Adam, suyi magana akan cin zarafin mata, dukarta suka yi sai da cikin wata. Uku ya koma baya sosai yanzun haka ya dawo wata daya, gashi haukar ta irin me jijjigar nan ce, shima haka ya isa ya tab'a lafiyar cikin, sam Yan sanda suna abinda suka gadama."

Haka tayi ta masifa tare da fadar sai ta turawa Commanden yan sandan kasar tunda shi yana cikin familyn Boualem kuma tasan zai share mata kuka, dan gaskiya dukar da akawa wacce ake zargin babu inda dokar kasar yace a ci zarafin mata.
          Kai jama'a.....na cika alkawarin jiyaa....

Continue Reading

You'll Also Like

65.7K 3.4K 54
The Rajputs well known as the most powerful and devil's for the people who tries to messed up with them people got goosebumps just by listening to th...
59.9K 1.4K 40
standalone ~ mafia siblings series "You can't make me stay here! I will get an emancipation." I yell. Flashbacks of the gun in my hand, the almost-de...
492K 17.3K 195
(Fan TL) Won Yoo-ha, a trainee unfairly deprived of the opportunity to appear on a survival program scheduled to hit the jackpot, became a failure of...
1.7M 55.7K 75
Alexander, James and Skye were triplets. They were stolen from their family at the age of 4. The family searched for them day and night never giving...