MAH~NOOR🌹

By AfricanQueen300

87.1K 8.2K 1.3K

Free book I grew up with this, I had best friends became enemies and then best friends again. I love it now... More

Prologue
destinations
Welcome to Hamoud Boualem Company...
Meet Mr Hot Guy
She take my position
Hamoud Boualem Family
Promotion
Personal information
Sisterhood
Big Mistake
Dreams
Interview
MR Arrogant
hateatfirstsight
Courage
My Nikkab
The Name
hypocrisy
Kidnapped
Escape
Injured
Exclusively
Approched
Mine
My Favorite
Silent
You are my Destiny
i'm in luv
Contract Marriage
Confessing
Bonus page
Tracking
stupidly
Chased Game
My wife...
Hopefully
Am sorry
Other side
The Family
Faruq
Happy end.... Mr And Mrs Mahir Hamoud Boualem
Lover

The Game is Over..

1.9K 189 35
By AfricanQueen300

https://my.w.tt/DZSZL7gxVcb
MAH~NOOR✧✧
My First Wife♡
Chapter 3️⃣4️⃣
MrsUsman400

For You Jikar kulu

BISMILLAH RAHAMANI RAHEEM

   "Jimin wa za a zubda? Ba zaku gaya min ba?" Ya tambaye ta cikin tsawa da fada, yana rike da Arm ɗinta.
"Mahir! Ka bani haɗin kai nayi abinda ya dace da kai! Matukar ka rasa damar gobe toh wallahi ina gaya maka ba iya kai ba hatta mahaifiyarka zasu shafe tarihin k..."

   Kifa mata mari yayi, cikin b'acin rai.
"Yaushe Mahaifiyata ta zama tsinken sakace hakorinki?"
   
"Karka kuma mari na! Sabida ni Ƴa ce ba baiwa ba, yin haka zai iya zama abinda ba zan lamunta ba." Tana Magana tare da huci, wayar hannun shine yayi tsiwa, ya dauka tare da sakawa a kunnen shi.
"Zaki! Ya naji kana haushi kamar kare, ko dai zakanyar bata baka hadin kai bane?"

      "Idan na kama ka, sai na."
Fauce wayar tayi tare da kashewa.
"Waye ya gaya maka, ana mayyadar raddi? Kyale shi, wasa na gaba dole ka fad'i!"

"Idan naki fa?"
"Zaka ji labarin da ya wuce tunanin ka, sabida sun wuce yadda kake tsammanin su."

"Wai meye kika sani akan su!"
"Meye ban sani ba kuwa anan su? Kayi ƙoƙarin duba, bayan Nazzir? Akwai katon zanen Dragonfly idan ka samu kazo na gaya maka waye Ubanshi, wanda shi na shi zanen yake gefen wuyar shi, shi yasa baya saka riga mara kwala."

     "Yaushe kika san haka?" Ya tambaye ta cikin tashin hankali.
"A ranar da Badar ya turo min sakon shi, ya gaya min kome akan ka. Ban fahimta ba sai bayan da nayi backup din Email address dina. Anan ma fahimci abinda yake son na fahimta, Bayan mun dawo, na kuma duba laptop ɗina, amma ban sami abinda nake so ba..kayi hakuri kwai lokacin da zaka san meye faru.'"

.    "Ke jinki zaki min dadin baki ne na kyale abinda nake mishi kallon wasar mutuwa? Toh baki isa ba, duk abinda zai faru ba zan tab'a lamuntar faduwa ba!"
Daga haka ya barta a falon, taji haushi Sosai, dan haka tun da tayi sallah isha take kwance idanunta lumshe, har ya gama abinda ,ai yi tana jin shi yana taje kanshi alamar yayi wanka, dake mutum ne mai son gyara gashin kanshi.

       Yana tajewa ina ina jin saukar ruwan a fuskana, dan haka na juya mishi baya abuna, amma dan bakar naci da jaraba, haka ya juyar dani ya shiga min wasu Yaren da shi.kawai ya iya, sosai ya jefa ni cikin wani yanayi.

       Lumshe idanun nayi, tare da mika kamar zan shiɗe, haka ya cigaba da abinda yayi niyya, har dai da ya samun nasarar juye min bakin man shi, kafin ya koma yana sauke numfashi akaina, takaici ya bani nayi banza dashi ina jin shi yana kara matse min kirj, tare da saka yatsar hannuna a bakin shi, kamar wanda ya sami Lollipop.

   Banza nayi mishi tare da zare hannuna, a bakin shi haka yayi ta jagwalgwalani har na samu na tashi nayi wanka, sannan na dawo na kwanta, dake akwai barci a idanuna, ina kwanciya ya zo tare da haska kirjina da yake cke tam, a hankali ya saukar da hasken zuwa cikina yana kallon yan layin dake kasan mara na, yadda ya taso, sakamakon cikin da ya tasa Matana, lub'a hannun shi yayi nayi mishi kara tare da mik'ewa ina b'ata rai. Hararar shi nayi sannan nayi kwanciyata, tare da kumbura fuskana, amma mutumin nan bai fasa min wasan banza ba sai da yaga raina ya b'aci, sannan ya kyale ni yana murmushin mugunta.

          Dakyar nayi barci sabida mugun halin Mahir, ina jin shi lokacin da yake kokarin shigewa jikina.

      Da asuba, tare muka yi wanka, sannan ya ja mu, sallah bayan mun idar muka kuma bin lafiyar gado, bayan gari ya waye ne, ya sani muka sauka kasa muka ci abinci, sannan muka anan muka hadu da Nazzir, tare da wata yarinya dauke kai muka yi abin mu, muka Cigaba da karyawa. Bayan mun gama. Dake yarinyar tayi shigar banza ne.

    Sussuce min Mahir yayi, dole haka na hakura ya gurgure Ni, sannan ya kuma taimaka min muka yi wanka, tare muna fitowa muka shirya cikin kayan arewa Ni riga da zani da mayafi babba, shi kuma jamfa ce haf tare da hular da aya murza, muka dauka gurin game din.

    Anan ma banda na kai zuciya nesa, tabbas da mun bar abin kunya, domin tsakanin shi da Allah ya nace sai ya ci gasar, Ni kuma ina kallon yadda su Nazzir suke kallon shi, zagayen farko damar ya kai labari, kafin muka shiga zagaye na biyu, dakai na na fadar fashi. Kamar zai yi hauka, na karshen ne ya fadi sosai domin ga dawakan shi duk azube akan allon wasan.

            Tashi muka yi zamu fita, Nazzir yace.
"Karku kuma dawowa nan domin idan kuka dawo ina me baku hakurin abinda zai faru."

Dake yana da mugun kafiya shima, haka yayi ta gayawa Nazzir, magana marasa dad'in ji. Karshe haka naja hannun shi muka fita, kallon Juna muka yi rai mu a b'ace.
"Me yasa ba zaka Fahimta ba?"
"Akan me yasa zan fahimta? Bayan ina gani kuka zubda ni?"
       
Girgiza kai nayi na barshi a gurin aiki yana huci, sannan muna shiga cikin dakin mu, na janyo laptop dina,na kunna mishi.

     Dauke kai yayi tare da zubawa hannun shi idanu.
"Kalla!"
Kin d'ago kai yayi, sai da nayi magana da ƙarfi.
"Malam dube ni nace ma"
Cike da mamaki, ya zubawa Allon na'uran ido, hoton Ummi da kanen shi ne, an saka jar zane akan su.

    "Da ka kuskura ka kai labari, haka zaka sha mamaki abinda zai dawo daga baya,"
"A'isha! Me kika sani akan wannan al'amarin?"
Zama tayi a kusa dashi,sannan ta rike hannun shi, duk da bata kaunar Mahir, amma ba taji zata barshi a cikin duhu.

...
"Lokacin da Badar ya turo min sako, ya tabbatar min da cewa baka da hannu akan abinda yake faruwa, amma na kasa fahimtar ka. Sai dai a karshen Bayanin shi yace akwai gasar da Nazzir suke shiryawa duk wanda ya shiga takun tsaka dasu.

        Shima kafin su kashe shi, sai da yayi wasar, kuma ya cinye wasan baki daya, sannan suka kashe shi. Amma bai gaya min yadda wasan yake ba, yau sati daya kafin mu zo nan aka shiga turo min wannan sakon, da shirin da suke akanka, shi yasa naji ba zan iya barin ka, ka cinye ba domin Ummi da Kanenka!"

      Cike da mamaki yake kallonta.
"Toh dama kin san mutanen da suke zagaye dani ne?"
Mikewa tayi tare da. Nufar ban daki, ya biyota.
Kallon shi tayi tare da fadawa jikin shi, daga nan ta kuncewa Mutumin kirki hankali, sai da ta tabbatar sun baje a gadon, sannan ta shiga gaya mishi abinda ta sani akan kamfanin shi, tare da yadda ta san kome a cikin kankanin lokaci, ya kasa aiwatar da kome, kwalla ne yake zuba daga idanun shi.

" Me yasa ba zaki zauna da ni ba?" Ya tambaye ta,
"Ba zan iya bane, nayi kokarin koyar soyayyarka amma na kasa, am sorry." Da sauri ta mike akan shi idan ta tuna yana da matar shi na fari sai taji babu dad'i, idan ta tuna yadda ta sake mishi jiki yayi yadda yaso da ita, sai ta ji ba dad'i.

Ban daki ta shiga tayi ta kuka,kamar ranta zai fita, bata san me yasa tun ranar da aka gaya mata maganar auren shi ba take yawan jin haka.

       Shigowa cikin ban dakin yayi ya shiga cikin ruwan, yana kallonta, sannan ya kai hannun kirjinta a zafaffe yake murzata. Dauke kai tayi kamar bata jin abin a ranta, nan kuwa mintsinta yake a ranta.
"Mahir!"
"Noorh!"
"Kasan cewa an kusan bikinka?"
"A ranar da aka kai min matar zan bata saki uku, domin kece abokiyar rayuwa ta! Kin zame min Bakuwar Fuska. Tun daga ranar da na ganki,.kina masifa akan mun tare muku hanya, na Fahimci Allah ya turo ni Yola ne domin samun abinda na rasa."

Yadda yake amayar min da zuciyar shi, sai da na kasa jurewa domin ya gama fadawa soyayyata, dan haka ya juya tare da kallon shi, a hankali na kai bakina saman nashi, hannun shi ya kai keya na..

•••
Washi gari
Muka bar Abuja, ban san me yake shiryawa ba, amma time to time, yana sake murmushin har muka iso, muna sauka Abokin shi Usman Kamfut yazo ya dauke mu.

    Muna isa gidan Ummi gabana ta fara faduwa, a hankali muka shiga gidan, cikin sallama.
Zubur Tasleem da Iyayenta suka mike.tare da kura min ido, dauke kai nayi domin ina tune da abinda ya gaya min, bin shi nayi ya shirya sannan muka sauko bayan ya gurje ni son ranshi, domin na fahimci yanayin shi mutum ne me bukatar kulawa.

      Na saka hand dries zan busar da gashina ya kwace, muna fito abin mu, muna sauka naga an shirya table din,.kallona yayi sannan ya ce min.
"Mu shiga ki nima min abinda zanci! Hajiya na Barka dai! Bari princess ta bani abinda zan taimakawa tumbina"

              "Allah ya shirye ka! Toh ka gama kazo ga Iyayen Matar ka sun zo batun baikon ku." Inji Hajiya.
"Da dai sun koma inda suka fito, domin Ni ina da wacce nake so."
Daga haka muka shige inda ake girkin, muna yi muna dariya, dake ana kallon duk abinda yake faruwa, zagayowa yayi tare da rungume ni.

     Muna aikin muna rungume da juna, kodan na bakantawa Tasleem da Iyayenta, har muka gama, sannan na shiga ba shi abincin yana ci muna hira. Muna gamawa muka nufi gidan shi, wai kar su min wani abu da babyn shi.

               Yadda naga Tasleem tana kuka sai da ya kashe min jikina. Tunda muka koma gidan, sai da muka yi kwana biyar ban fita ba.

  Bayan tafiyar mu ne, ta fadi wai ta suma,aka nufi asibiti da ita, tsawon kwanakin nan Mahir take ambata, sai da suka kwana shida sannan na samu labari bayan ya sani a gaba muka tawo, tunda muka shiga cikin dakin, take kallona.
             Hannun shi ya kai tare da rungume ni ta baya, kan shi akan kafad'ana. Wasu hawaye ne suka zuba.
"Princess bari na je na dawo, karki yarda wani ya baki wani abu ki ci, kinji."

   Yana fita, Hidaya da Samiha tare da Adeemah. Suka zuba min ido, tashi Adeemah tayi tare da rufe kofar, wata ƙatuwar bag suka wurgo min, bayan sun kira wayar Nazzir tare da Iyayen Tasleem.
   Had'iye yawu nayi ina kallon su.
"Nasan ba don shi kike ba, dan haka ga shi mun sayi duk wani soyayyar da yake miki, sannan cikin jikinki dan karki kuma dawowa akwai maganin zubdawa. Ance kema yar Algeria ce dauki kayanki, ki rabu da Mahir domin ba tsarin ki bane shi."

    Kallon su nayi, Nazzir ya tawo kamar zai shige jikina, matsawa nayi.
"Nasan kece kike juya mana hankalin shi, dan haka ki bar garin nan salin alim ko kuma na sab'a miki kaminki."

   Had'iye yawun nayi, ina kallon su. A hankali Tasleem ta sauko.
"Noorh! Me yasa? Me yasa kika dauke min hankalin shi, gashi har da cikin shi kike dashi, Noorh mutuwa zanyi idan baki bar min shi ba."
      Girgiza mata kai nayi, sannan nace mata.
"Da dai kin amince sai mu zauna tare dashi, tunda mijin mata hudu ne! Amma kice na bar miki shi, ba zai tab'a sabu..."

Yadda Nazzir ya janye ta a gaba na,.yace musu kowa ya juyar da kan shi. Aikuwa duk suka yi haka, kallon shi nayi ban san lokacin da nakaiwa gaban shi cafka ba, ihu ya saka. Na murɗa da karfin tsiya,.ya fasa kara karo na biyu.
"Zama da shi ya koya min yadda zan kwaci kaina, dan haka ka kuma kuskuren min wannan haukar sai na kashe dan isa irinka,", naja abar da karfi ya zube kasa. Duk suka razana. Kuka ne yazo min, sannan na had'iye kukan na kalle su.
"Ba zan rabu da shi ba sabida ke ba, dan haka ki shirya zama dani a matsayin kishiyarki ki."

"Baki son zuwa gurin danginki ne? Kiyi kokarin fara niman danginki kafin kiyi iko da Namijin da gobe zai miki gorin mara asali." Wani irin abu taji ya daki kirjinta, ta zuba musu ido.
"Kiyi kokarin ganin kin samu danginki sai ki zo a gwabza kishin da kike jin shi mahaukaciya. Me cutar hauka."

Aikuwa suka fashe da dariya, wanda sautin shi ke shiga har cikin kunnenta, cikin fushi da fusata, ta suri jkar kudin. Ta bar asibitin, cikin minti talatin ta isa tare da tattara kayan ta, ta bar gidan baki daya, ta nufi airport.

            Bata yi kuka ba, dan ciwonta kamar zai motsa, haka ta sami jirgin da zai ida tripoli na kasar Libya, daga nan kuma zata samu jirgin da zai shiga Algers.

Bata san ko ina ba, amma zunzurutun b'acin rai yasa ta, barin kasar da bana ta ba, idan akwai abinda ya fusata ba kome bane sai zunzurutun kishin mijinta, tana masifar Muhsin mijinta, shi yasa ta kasa boye b'acin ranta, kishi kuma yana haɗe da soyayya ne, daddin dadd'awa, gorin da aka ce zai mata shima ya taka rawan azo a gani.

   Dan haka bata tare da ta fahimci, me aka shirya mata ba, ta haura saman gadar zare. Ta kuma bi ta kai.

     ...  Bayan minti Talatin jirgin ya tashi, har zuwa lokacin bata iya kuka ba, dan ta fahimci itace ta ke cusa musu kanta su basa yinta. Bayan daga shi sai Ummi da Hajiya suke yinta..

      --- bayan awa daya, ya dawo kallon su yayi suna kuma kallon shi suke suna niman hanyar da zasu kare kansu.
"Ina Noorh?"
Nazzir wanda bai gama samun damar nutsuwa ba, ya bude baki zai magana Mahir ya kwashe shi da mari.
Mika mishi waya Adeemah tayi jikinta na rawa.
"Ni bana son shi! Amma zan amshi kudin dan haka Tasleem gashi nan na bar miki MAHIR"
Dariya yayi yana kallon  su, zunzurutun ya rena musu hankalin.
"Ku tattara mu koma gida, yadda zanci Ubanku a nutse."

    A tsora ce Baban Tasleem yace mishi.
"Zaka min shiru ko sai na hada da kai, yarinyar da ka iya rubda ciki akan Dukiyar ta, yarinyar da ka cilla rayuwarta domin ta kar tayi kyau gobe, Yarinyar da ka lalata lafiyarta, kace baka santa ba, shine kuka zo cin dudduniyarta. Toh ka tattara Yarka ku bar Mansion din mu, ki na baka mamaki."

Daga haka ya juya tare da barin d'akin, kallon su Nazzir yayi bayan fitar  kanen Mahir.
"Zan baku dama, kawai ki kafe akan abinda zan saka ku, sannan kuma zan kai ku gidan da Uwar shi ta baku."

    Sunyi na'am da abinda yace musu.
Lokacin da Mahir suka isa gida, bai kula su ba, ya nufi gidan shi, anan ya samu ta tattara kayan ta, ta bar shi, sai wata yar takarda da ya samu.
*Duk da nasan wacece ni! Amma bai hana ni maka rashin da'a ba, Am sorry ban san me naki ji a kanka ba, amma am so Happiness da nake dauke da cikin mutumin kirki irinka. Sai dai na tafi na bar baya da kura. Ka tuntube Ummi da Barrister Usman Kamfut, zasu iya gaya maka abinda ya faru shekaru goma sha biyu,naso na tsaya naji me ya faru, amma yanayin kaddarata ba zata bar ni ba, Bana son na cigaba da wahalar da kai, Tabbas ni Mahaukaciya ce, nayi hauka. Amma duk da haka na zabi sadaukarwa domin rama halaccin da iyayen Tasleem suka min, dan haka na bar mata kai. Kayi hakuri Little princess tana kewar Daddy King. Mahir ka mai dani mutum da yau ina yawo a titi karshe na mutu da cutar hauka. Nagode da min gata, don Allah karka sake ni, zanyi farin ciki idan na mutu da auren ka Assalamun Alaikum*
  
                       Da
                    Matar ka! Abar sonka....
Kowani marubuci da yadda yake tafiya da labarin shi 🙏🏼☺️

Continue Reading

You'll Also Like

2.5M 187K 71
RATHOD In a broken family, every person suffers from his insecurities and guilt. Successful in every field but a big failure when it comes to emotio...
397K 41.1K 22
انا العاصفة الحمراء ألتي تراهن وتربح انا القوة العظيمة الذي سوف تنهك كُل الارواح الجنون والتلاعب بحد ذاته هنا أستطيع ان اتلاعب بعقلك حَد الجنون امر...
117K 8.4K 64
ရယ်စေ၊ မောစေ အသက်ရှည်စေ ဟာသနှော၍ ရယ်မောပျော်ရွှင်စေရန်အလို့ငှာ လုလင်မောင်မောင်(ပစ်တိုင်းထောင်) နေမင်းပုည(ရွှေဒင်္ဂါး) (Own Creation) Starting Date...
PARIWAAR By

General Fiction

122K 13.1K 90
Arjun Shergill is a 28 years old, well renowned businessman, who has a big loving family and two kids. He is a caring and utmost loving man. This sto...