MAH~NOOR🌹

By AfricanQueen300

85.4K 8.1K 1.3K

Free book I grew up with this, I had best friends became enemies and then best friends again. I love it now... More

Prologue
destinations
Welcome to Hamoud Boualem Company...
Meet Mr Hot Guy
She take my position
Hamoud Boualem Family
Promotion
Personal information
Sisterhood
Big Mistake
Dreams
Interview
MR Arrogant
hateatfirstsight
Courage
My Nikkab
The Name
hypocrisy
Kidnapped
Escape
Injured
Exclusively
Approched
Mine
My Favorite
You are my Destiny
i'm in luv
Contract Marriage
Confessing
Bonus page
Tracking
stupidly
Chased Game
The Game is Over..
My wife...
Hopefully
Am sorry
Other side
The Family
Faruq
Happy end.... Mr And Mrs Mahir Hamoud Boualem
Lover

Silent

1.9K 177 26
By AfricanQueen300

MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 2️⃣5️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

Idanun ta ne ya kuma komawa kan bindin shi, tana kallon shi kamar taga dodo, ta leka sai kuma ta rufe fuskar ta, tana kuma lek'awa zata rufe fuskar ta.
Wandon ya dauka ya saka tare da xora jallabiyar shi ya bar mata d'akin, dan ya fahimci haukata shi take son yi.

Ga yadda yake ganinta naked babu abinda zai hana shi bai farmata ba, kitchen ya nufa, har zai fara bada oda abinda za a girka mishi dan yasan Haroon zai iya zuwa da wuri, sai ya koma dan yasan ba karamin aikinta bane fitowa tsirara. Allah sarki tana can ta gaji har ta fara barci, rufeta yayi tare da gyara mata kwanciya. Sannan ya wuce daya dakin ya kwanta.
Washi gari da safe, ya rigata tashi, har ya gama zai fita sai ya tuna babu kaya a jikinta, dan haka ya dawo ya saka mata kaya, tana barci sannan ya tashe ta tayi wanka da karyawa kafin ta sata tayi sallah. Tana idarwa ta fara barci. Sannan ya fita ya barta.
Karfe sha biyu zata sha na rana, tun sha biyu saura ya dawo, ya bata sannan ya koma gurin aikin shi, haka ya bashi damar kulawa da ita, kuma sosai yake hakuri da kiriniyarta, domin wallahi bata jin magana.

Ga barna kamar bera, sau uku tana fasa mishi Center table, na farko wai ta hau zata zauna, tana cikin zama kawai taga ya canza channel din tv dake tana kallon Dora in Magic Land ne, kawai ta fasa ihu tare da tashi tsaye ta daka tsalle badan yana gurin ba da sai ta raunane, ya dauke ta, aikuwa ta shiga ya kushinsa tare da kai mishi duka, abin ya masifar b'ata mishi rai, dan haka yana sauke ta, ya dalla mata mari. Sai da ta dauke wuta a tsorace ta kalle shi.
"Uncle duka na! Ammyn Abbina."
Yadda tayi maganar shi kan shi sai da idanun shi ya cika da kwalla, wato abinda ya Fahimta duk da manta kome iyayenta suna makale a ranta rungumo ta yayi ta fashe da kuka.

Rungume ta yayi, ta k'amk'ame shi tana goge fuskarta a jikin shi, daukarta yayi ya kai ta d'akin dan haka kawai yaji kamar zai yi baki, yana sakata a daki ya bata maganin barcin ta, ko minti biyar bayi da ita ba, yaji muryan Nazzir.

Rufe kofar d'akin yayi, sannan ya fito kallon juna suka yi sannan ya koma ya shiga tattara Broking glass din falon, ya kai waje. Sannan ya dawo yana jin shirmen Nazzir, da ya gaji ya kwanta tare da daura daya akan daya, yace "mishi idan ka gama shirmen ka ina zaka iya rufe min kofar gidan."

Haka na biyu, ma ta fasa wai zata yi wasan sauka da hawa, shima faɗowa tayi daga Center table din, na uku ne tayi a gaban Haroon, bai san tana gidan ba, lokacin da yaji karar fashewar abu a falon,.sama ne ya zo da dubawa yaga wata cutie face.

.kamar ya zura da gudu, amma ya tsaya, tare da kallonta itama kallon tsoro ta mishi sannan ta gudu dakin ta, shiru yayi tare da cewa a ranshi yaushe tazo.
Dan haka da Mahir ya dawo bai san abinda ya faru ba, sai da tace mishi.
"Uncle! Wani yazo?"
Shiru yayi tare da kallonta kamar yana son tuna wani abu, kafin ya shiga dakin shi na aiki ya ga, ai Haroon ne bai kuma bin ta kanta ba, domin shiri yayi akanta a cikin gidan.

---
Yau asabar, wanda yayi dai dai da cikar su wata daya da dawowa ta tashi da ciwon mara, haka tayi ta birgima gashi harun ya tafi kwara, tun daga d'akinta take fama har ta fito falo, shi kuma yana can Gym room, haka ta yar yada mishi jiki tun daga falon farko na sama har falon kasa, kuma taki zama guri guda.

Sai kuka take tana niman Uncle, yana cikin daki yana faman d'aga karfe, jin sautin muryan ta yasa shi, fitowa, yana zuwa ya ganta zaune ji yayi zuciyar shi kamar zata fado kasa, domin daga ita sai pant da wata shimi, kamar ya fashe da kuka, yadda ta b'ata ko ina, da jini. Haka ya rikota suka nufi ban dakin falon kasa, ya cika da ruwa ya turata ciki, sannan ya koma kitchen ya nufi loundry ya dauko bokitin mopping ya ciko da ruwa, zunzurutun tashin zuciya, haka ya zuba hypo, Klin, izal da dettol, sannan ya zo ya fara goge falon yana yi yana yatsina fuska, yana jin da yau Noorh da hankalin ta zai tasha faɗa, dan ya tsani kazamta.

Haka ya gama goge gidan tass, sanan ya dauko turarukan wuta duk ya saka, ya dauko rum frsh ya fesa, sannan yaje yayi wanka dan ji yaƙe kamar yayi yawo cikin jinin, sannan ya nufi ban dakin yayi mata wanka tare da nuna mata yadda zata yi tsarki, yana gamawa ya dauke ta suka nufi dakin ta, ya ajiyeta sannan ya fito ya rasa me zai mata, kawai ya koma dakin shi domin bata da pad.

Wata riga ya saka mata tare da cewa yana zuwa, da sauri ya fita. Ganin ya fita ai kuwa ta fito daga inda ya ajiyeta ta fara barna, tana zuwa kitchen ta kunna gas, tare da cika ruwa a tunkuyar non stick ta fara kokarin daurawa a kan gas sai ga Shibha tana sallama. Sake tukunyar tayi akan kafarta, dan tunda yazo gidan bata tab'a ganin mace ta shigo ba, da gudu ta bangaje shibha, ta haura sama, tana lekota. Ita kanta Shibha tsoro ya kamata balle Noorh.
Akan lokaci ya dawo san bai jima ba, ya shigo gidan yayi turus.
"Waye yace kizo baki sanar min ba?"
Ya fada fuskar shi a tamke, da gudu Noorh ta sauko tare da buya a bayan shi yana sauke ajiyar zuciya, sai lokacin ya fara jin kamshin gas, a saba'in ya shige kitchen, yaga b'arnan da tayi tare ya rufe gas din ya fito ya rike kunnenta ihu take tare da yarfe hannunta, mikawa Shibha pad din yayi sannan yace mata.
"Wuce ki saka mata!"
Babu musu ta wuce, suna shiga dakin taga Noorh na mata wani irin kallo da gudu ta sauko abinta, ta gaya mishi da kanshi ya rakata ta, yana shiga dakin yaga zanin gadon duk sun b'aci da jini.
Kamar yayi ta zunduma ihu, haka yake ji, dakyat ya samu Kanwar shi ta gyara dakin, tana gamawa Noorh na b'atawa, cikin jin haushi tace.
"Wallahi ba zan zauna ba,guduwa gida zanyi ku Cigaba da kazamtar ku."

Haushi ya kama shi sosai, domin yana ji yana gani ta b'ata ko ina, dan Allah yaso ya saya pad din me panta ne da bai san ya zai yi da Noorh ba.

Kafin Shibha ta bar gidan, sai da tasha kashedi, sosai tare da jan kunne, aikuwa tana komawa gida,taja bakinta shiru, ta same su, suna jiran zuwan Azumi nan da wata biyar masu kyau.
•••
Nazzir yana yawan zuwa gidan Mahir, tare da saka idanun shi, akan Mahir abinda da ta kai har Mahir ya hada shi da mahaifin shi, ya ja mishi kunne baya son hayaniya, amma yaki. kamar ya san Mahir yana boye mishi wani abu, shi kuma ya nace sai ya nima.
... Baby Queen kuwa suna gama Service ta uzurawa Dad, ya shirya har da Mommy suka nufi Annaba, garin su dake ƙasar Algeria. Duk da Sun isa da dare, bai hanata ganin yadda garin ya hadu ba, a wani hotel suna kwana, washi gari. Suka nufi garin su yana cikin garuruwan masu dinbun tarihi, dan haka ta dauki haka a matsayin Destination place, haka tayi ta daukar shi a hotona.

Ba laifi Familyn baban ta suna da ƙarfin iko a garin, kuma suna rike, da madadin iko. Domin sune suke roling garin baki daya, haka ya saka mata wani irin izza, domin matsayin Mahaifinta ne, Kawun shi ya rike mishi, dake yana zuwa suka ce ba zai koma ba, dan haka suka bashi damar ya rike garin.

Karku ga yadda kan Tasleem yayi wani irin kato, tare da jin ita wata ce, Mom duniya sabuwa, amma dake Dad me wayo ne yaki amsar mulkin, yace sai ya dawo zai amsa, haka suka yi ta yawo a garin har na tsawon wata uku, sannan suka fara tattara nasu zasu dawo Naija, anan ne ta ji aranta taje taga Family Noorh.

Lokacin da aka kaita biskira, har cikin gidan Kakannin Noorh sai da taji kamar zuciyarta zata buga, me yasa kome na Noorh sai an nuna mata fifiko akanta, Kanin Baban Noorh Me suna Dr Dr hisham abdullah keluarga shine Ministan lafiya na kasar Algeria, D'aya kanin shi Dr Nahid Abdullahi' keluarga shine matsayin Governor Biskira, ga wasu manyan manyan mukamai da suke rike dashi, bata kuma rudewa ba, sai da aka gaya mata ai Maman Noorh Familyn ne, sau uku ta shiga ban daki Zunzurutun cikinta ya tsirga, kamar ranta zai fita lokacin da ta gama fahimtar itace tazo duniya a zero zata koma a empty. Bata yi kasa a gwiwa ba, ta gaya musu ay Noorh ta rasu. Sunyi kuka sosai domin a ranar aka fara zaman makokin Noorh. Kakar Noorh wacce suke kiranta Ummul Banun, tace ita bata yarda Noorh ta rasu ba, tana ji dai bata lafiya. Haka dai suka bar garin kwanan su daya, amma ba karamin shatara na arziki aka musu ba, domin sun san gaba da gabanta, duk sai ran Tasleem.ya fara b'aci, abinda bai kai faɗa bai sai fada da kuka. Ita me ya sa aka haifeta a karamin family, domin karamin me degree daya shine mata shi dan shekara ashirin da daya, daga masu degree biyu sai masu uku, kuka take tare da jin tsanar familyn ta.

A cikin wannan yanayin suka dawo Annaba, suka hada kayan su, suka dawo Naija. Tare da burin dole ta nimo mijin da zata burge kowa, domin a yanzun babu wanda yasha gaban ta, shine target din ta na gaba.

•••
Yau ma Shibha tazo gurin Noorh da katon teddy bear, sai kwalin chocolat, ai kuwa suka zauna a falo suka fara sha, suna gamawa,suka shiga kitchen. Akw shiga barna wai ana girki.
Flour da kayan miya sai da yaci uwar shi domin pancake suka watsa a kitchen ɗin, haka suka gama aka fito falo, aka kuma baje suna kallo ana cin pancake kafin kace kwabo an lalata falon an sauya mishi halitta launuka.

Jin ana alamar ruwan sama, yasa Noorh, fita da mugun gudu. Ta faɗa wasa da ruwa, nan tana wanka tare da wasa da ruwa. Ita kan Shibha gyara ko ina tayi domin tasan idan yayan su ya dawo zata sha fada, kuma sake yarinyar na da nutsuwa haka ta gyara ko ina tsaf, sannan ta fito bata ganta ba, ashe ta zaga can bakin swimming pool, tana wankar a can, har Mahir ya dawo, kallon ko ina yayi alamar anci Uban gidan sosai, yadda ya balbale Shibha da fada dai dai shigowar Noorh gidan, zata jata suje suyi wanka. Taga Yasaka Shekara Shibha da a gaba da fada.
Kuka tasaka mishi tare da ture hannun shi.
"Uncle daina fada!" Ta ture shi tana kuka, mutuwar tsaye yayi sakamakon Jikewar da tayi daga samar har kasa, kayan jikin ta ya lafe a jikin ta, gashi wani irin yanayi kome na Jikinta sai da ya fito, kallon kasa yayi yadda take zubda jini, idan ya Fahimta pad din Jikinta ne ya jike jagwab.
Dauko lema yayi ya mikawa Shibha.
"Kar na kuma ganinki cikin gidan nan!"
"Yaya ka barni muyi hira da Aunty Noorh don Allah ba zan kuma ba zan zo da abincin mu ma"
"Ni zaki janyowa fitina Ummi tasan ina ajiye da Yar mutane, maza ki tattara kar na kuma gani ki!"
"Ni wallahi zan kuma dawowa!". Ta faɗa kasa kasa, tana fita yayi ciki da Noorh yarinyar nan tana son Haukata shi, dubi yadda kome nata yafito, maketa yayi tare da kaita daki yasata dole ta cire kayanta ya haɗa mata ruwan zafi, tayi wanka tare da hada mata ruwan zafin da zata sha.

Sabida kar mura ya kamata, tana fitowa ya bata pant ta saka, wanan ya mika mata kayanta, ita nan fushi take dashi har da wani b'ata rai, tare da juya mishi baya.

Tana gama shiryawa ta fito tare da ɗaukar chocolat dinta ta fara ci, wasa wasa sai da ta cinye kusan rabi, yana fitowa ya samu ta cinye, buge mata baki yayi tare da cewa.
"Chocolat girl kawai!"
"Uncle bindinka kawai!"
Zaro idanu yayi waje, tare da rike bakin shi, wato tasan ta zage ka, itama. Make mata baki yayi ta bata magani tasha bayan ya bata abincin da yazo da shi, fir taki ci. Sabida sunci pancake.

•••
"Aysar! Ina jin kamar Noorh tana raye, domin ban ji ta mutu ba, wancan bad guy din yaƙi bani damar muyi magana, ban san meye project din shi na gaba ba,"

Gyara zama Aysar Haladu yayi tare da ɗaukar kwalbar ruwa yayi tare da sha, yana kallon Manager.
"Kuma kasan Mahaifiyarshi tana daga cikin manyan alkalan ƙasar nan, don haka bazamu tab'a lokaci guda ba. Dole sai mun san meye yake nufi da shirun da yayi"

"Why him kept quiet? Shirun shi yayi yawa, me yasa ba zai yi magana ba, toh mu zamu yi Analysis wani abu da zai saka dole yayi magana!" Inji Manager,

"Karku fara takalo shi! Nasan waye MAHIR! Idan aka takalo shi matukar ya fashe mune a ruwa, dan haka ku bari akwai lokuta da zamu tab'o shi kuma zai yi magana,"

"Ya kake abu kamar kana jin tsoron shi ne?" Inji Aysar Haladu,
"Ba tsoron shi nake ba, nima umarni ake bani, idan na sab'a zan iya samun matsala."

Shiru duk suka yi tare da mikewa, sannan suka bar gidan.
Ya jima yana kallon yadda zai karya Mahir amma har yanzun bai Samu damar ba, amma Insha Allah next target din shi, sai ya kure shi. Sai yaji tsoron fitowa media ya kare akan shi. Sai ya mishi abinda ba zai tab'a mantawa ba.

Dan haka ya ajiye abun a ranshi, tare da Cigaba da abinda yake gaban shi.
•••
Tsaye yake yana gabatar da project din da yake bukata, tana shigowa,ta kurawa abun ido, tayi kamar tana son tuna wani abu, kawai me zai faru, kawai ta juye mishi ruwan hannunta a samar project din, dama kan shi ya gama kuncewa tana zuwa ta kuma watsa mishi ruwa akai.

Cikin wani irin yanayi ya kalle ta, ya rasa yadda zai yi da ita, dan haka yana juyawa, ya fincikota yayi waje da ita. Tare da rufeta a daki, yazo ya d'aga takardar yana kad'ewa, kamar ya tsalla ihu, yana shan iska, ya duba abin mamaki, sai ga abinda yake bukata da project, din ya fito yadda yake bukata, kallon kofar da take bugawa yayi cikin nutsuwa, murmushi yayi tare da bude kofar yaga tayi tsuru tsuru, cikin tsoron kar ya buge ta...

Continue Reading

You'll Also Like

23.3K 1.6K 15
RATHOD'S - the name which can make anyone kneel in front of them. manish rathod ,father of 4 children but is unknown of the 4th one who is youngest a...
393K 13.3K 53
Anhay Sharma:- Cold business tycoon who is only sweet for his family. He is handsome as hell but loves to stay away from love life. His female employ...
59.9K 1.4K 40
standalone ~ mafia siblings series "You can't make me stay here! I will get an emancipation." I yell. Flashbacks of the gun in my hand, the almost-de...
276K 17.7K 48
The feeling of being abandoned by one's own family was not unknown to Aadhira. She hates her family for abandoning her when she was only a newborn, l...