MAH~NOOR🌹

By AfricanQueen300

85.4K 8.1K 1.3K

Free book I grew up with this, I had best friends became enemies and then best friends again. I love it now... More

Prologue
destinations
Welcome to Hamoud Boualem Company...
Meet Mr Hot Guy
She take my position
Hamoud Boualem Family
Promotion
Personal information
Sisterhood
Big Mistake
Dreams
Interview
MR Arrogant
hateatfirstsight
Courage
My Nikkab
The Name
hypocrisy
Kidnapped
Escape
Injured
Exclusively
Approched
My Favorite
Silent
You are my Destiny
i'm in luv
Contract Marriage
Confessing
Bonus page
Tracking
stupidly
Chased Game
The Game is Over..
My wife...
Hopefully
Am sorry
Other side
The Family
Faruq
Happy end.... Mr And Mrs Mahir Hamoud Boualem
Lover

Mine

1.9K 224 36
By AfricanQueen300

https://my.w.tt/VtYbk6o8Ecb
MAH~NOOR
My First Wife♡
Chapter 2️⃣3️⃣
MrsUsman400
Free book 🤩
For You Jikar kulu

"Wannan kuma matsalarka ce, itama Adeemah zanci zarafin ta, idan na shiga cikin gidan, wallahi idan baka fita hanyar kanwata ba, zan baka mamaki banza kawai wanda kazamtar shi bai tsaya a iya shi ba."

    Nan Mahir ya sille shi sannan ya bar gurin, duk da ya razana amma dan kar ya nuna cewa ya razana sai ya bi Mahir da harara.  Shi kuwa Mahir da ya shiga cikin gidan sai ya rasa me zai mata ya huce bakin cikin da ya gani dan haka ba tare da cewa kome ba, ya riko hannun da ya gani akan cinyar Nazzir.

     Murdewa yayi baya, sai da ta sake fitsari a jikinta.
"Na kuma ganin ki a cikin gidan su Nazzir ki kuma na ganki da shi sai na ɓalle hannunki mara mutunci kawai."

Cillata yayi ta fadi, kallon Ummi yayi cikin baƙin ciki ya juya zai fita cikin tsawa yace mata.
"Kar na dawo baki gyara gidan ba! Daga yau ita zata cigaba da aikin gidan ta tunda tasan daura hannunta akan cinyar namiji."

               Kallon shi Ummi da Hajiya suka yi, sannan suka ce.
"Da haka ba gwara idan tana da wanda yake sonta ya fito ai mata aure ba,"
        "Ita tasani gata nan dai." Ya fadi haka, bayan ya bar falon. Tsabar tashin hankali, a ranar kasa barci yayi, yana hango Abinda aka soyiwa Noorh da wanda Nazzir yayiwa Deemah, gani yake da zaran ya bar kasar Nazzir zai samu damar lalata mishi tarbiyyar kanwar shi.

      Dan haka, washi gari hana Haroon aiki yayi, ya nufi gidan Ummi ya karya sannan ya turawa haroon sakon yayi mishi abinci sai fita da shi.
Kallon juna suka Mahir da Ummi,
"Hmm! Sai kumbiya kumbiya kake min meye nufinka?"
      "Hmm! Ke bani wayar ki, da laptop din ki."

    Babu musu ta dauko kome ta bashi, sannan ya kalli Ummi yace mata.
"Hmm ina son zanyi tafiya!"
"Ina zaka?"
"Canada!"
"Allah ya tsare kuma a kiyayye tab'a yar wasu domin kar haka ya faru akan na ka"

     "Insha Allah" ya faɗa a takaice,
   Mikewa yayi ya bar gidan ya nufi gidan shi ya dauki abincin ta, tunda ya isa cikin asibitin yaga yadda mutane suke bin shi da ido, ya fahimci akwai matsala. Yana nufar hanyar da zai kai shi ya samu anata kiciniyar kaita d'akin ta, taki sai dambe suke da nurses, yana isa gurin ya mikawa wata nurse basket din abincin yazo ya rikota, d'ago kai tayi sannan ta fashe da kuka tare da fadawa kirjin shi, lumshe idanun shi yayi tare da rufa hannun shi a bayanta.
"Don Allah Sir idan mun daureta karka kunceta."
Dakin ya nufa da ita, yana shiga ya rufe kofar ya ajiye ta a bakin gadon. Juyawa yayi ya bude kofar ya karbi abincin sannan yazo ya ajiye shi daukar brush da maclean yayi ya saka mata, sannan ya riko hannunta suka shiga ban daki, karshe dai ta shanye maclean din.

        Brush kuwa karya shi tayi zata taune ya matse bakinta sai da ya fitar, sannan ya koma ya dauko wani ya kuma, lakata mata dakyar ya wanke mata baki da idanunta suka fito, zama yayi da ita ya zuba mata.
      A hankali yake ci yana hura mata iska, tare da bata a bakinta tana ci hankalinta yana kan kofar dakin da take ganin wucewar mutane ta kasa, can sai ta rufe idanunta, sai da ya lura da haka ya mai da ita tana kallon kofar shi yana zaune a inda take.

        Yasan bata cewa bata san koshi ba, dan haka ya shiga bata dai dai tare da kai hannun shi cikin ta, jin ya d'an taso ya ajiye abincin ai kuwa ta fara ihu, haka ya bata tayi mugun koshi, sannan ya dauke abincin.

         Kwanciya tayi a kafar shi, yana shafa kanta, a hankali yana wasa da gashin kanta,  sannun sannu yaji ya kama barci, gyara mata kwanciya yayi sannan ya kuma gyara mata gashin kanta, yana kallon yadda take b'ata fuska, tana numfashi dai-dai kamar wacce ta dauki kaya.

             ••• idan akwai abinda yake ɗaukar hankalin shi, toh surar Jikinta ne, tana da zubin halittar da yake son matar shi da ita, tana da cikar kamala a fiskarta, kallon shedar sallar goshinta yayi, yayi tare da sake murmushin jin dadi, duk yadda aka yi ma'abociyar ibada ce.

      Lokaci daya yaji tana samun nasarar yaki da duk wani matakin jin haushinta da yake ran shi.

      •••
Bayan kwana uku, ya gama shirin shi tsaf, yana lura da yadda Nazzir yake mishi shishigi da son sanin, me yake fitar da shi.
Kwana na uku ya suka bar kasar bayan an mata alluran barci, haka kawai yake jin. Wani yanayin da bai tab'a kawowa a ranshi ba, ji yaƙe kamar ya daukota zasu tafi yawon cin amarci ne, domin yanayin yana masa kama da ita din mallakar shi ce, baya jin ita din ta wani ce. Yanayin yana kara mishi kwarin gwiwar jin shi kamar ango ne. Lumshe idanun shi yayi ya bude akan kyakyawan fuskar ta, tana barci cikin nutsuwa.

       •••
Lokacin da suka isa, an karb'e su hannu bibbiyu, asalima suna ganinta suka daurata akan magani.

     Kwana goma, tana amsar magani kafin kuma aka fara kula da matsalar ta, su kansu. Jikin su yayi sanyi, sakamakon idan aka ce Za'ayi aikin za a iya rasata dab haka suka mai da hankali gurin bata magani tare da nimo Dr Zeng chang, na babban asibitin Beijing da ke China. Wanda a tarihin likitanci ya sami lambar yabo, sakamakon yadda yake aikin shi idanun mutum biyu.

      Shi aka turawa sakon, Amma ya basu hakuri tare da cewa, ba zan sami zuwa ba, sai nan da wata uku, su fara bata wasu magunguna. Duk yadda suka so yazo ya gaya musu yana da abubuwa ne,kuma dan babban asibiti ne ma suka nime shi da ba zai saurare su ba, sai bayan shekara daya, sakamakon baya zama yana yawan zuwa ƙasashen waje aiki yanzun haka ma ya amshi aiyukan wasu ne na kusan wata bakwai.

   Insha Allah idan ya gama nasu, zai zo amma a Cigaba da bata magani kafin yazo, abin ya dami Mahir dan har tayin kudi masu mahaukatar yawa ya bashi, yace mishi a'a ya bari zai zo dan kanshi.

             A haka Mahir ya hakura tare da zubawa Sarautar Allah ido, ya kuma cigaba da kula da ita. tare da shawarwarin da suka bashi yake daukarta suna fita, yawo, idan lokacin sallah yayi yana tare da ita idan taga yana yi itama yi take, sosai wani irin jituwa da shakuwa ya shiga tsakanin su, gabaki daya Mahir ya tattara zuciyar ya mikawa Noorh, ba tare da sanin ya mutu a kanta ba.

    Sai da ta fara ciwon cikin period, zarewa tayi tana ta ihu. Tare da dukar shi, dakyar aka mata alluran da zai rage mata ciwon tare da barci, shine aka sami saukin abun. Tana barci, duk ta jika jikinta da jini, koda ta farka ganinta cikin jini ihu ta saka tare da niman kwace jikinta daga saka mata belt, sai da Nurses har biyu suka mata allura da zai hanata kome, tana kallon shi suka mata har wanka, tare da gyara mata jikinta, suka mai da ita gadon.

           A hankali suke kula da ita, tare da bata magani da abincin da bazai kara mata karfin zubar jinin ba. Shi kuma Mahir baya zama sosai, yana can ana famar kasuwanci, amma idan ya dawo gare ta mantawa yake da kowa sai ita.

       Duk wanda ya ganshi yasan ya faɗa soyayyar Noorh amma ya kasa fahimtar kome akan haka, haka zai raba dare yana kallon ta, idan kuma idanunta biyu, haka zai sakata a gaba yana karatun Alqur'ani. Idan yana mata karatun nutsuwa take tana sauraron shi. Abinda ya Fahimta shine har yanzun bata rasa nutsuwar zuciya akan addininta ba. Dan ko sallah yake itama haka zata yi duk abinda yayi sai tayi. Kuma cikin nutsuwa da kamala. Wani abinda ya kuma kara mishi kwarin gwiwa akan ta, shine yadda take kame jikinta da kanta, bata cika dariya ko shiririta ba,.kawai dai idan larabci ya motsa ne zata cika mishi kunne da kiran Iyayen ta, da kanenta, sa zaran ta fara haka toh zuwa anjima zata suma. Kuma haka ya faru ne sakamakon shan maganin da ta fara.

       Dan haka ya mai da hankalin shi sosai akan kula da Ibadar su. After few one month, ta sami canji amma ba za ace wani abu ba, dan dai kawai tana nan sai haukar na raguwa, wanda ya haɗa da tasirin ibada da rokon ALLAH, duk da bokon da ya ratsa rayuwar shi, amma haka bai hana ya fahimtar dakai yana da ibada ba, dan mutum ne shima me yawan ibada, shi yasa Ubangiji yayi mishi iyaka da aikata masha'a, baya shan giya baya shan taba, shi mace bata gaban shi.

            Kuma baya damuwa da kallace kallacen batsa, Mahir bai damu da jin wakoki ba, abu daya zaka Fahimta a kanshi mutum ne me kishi da zafin niman na kanshi, duk inda zai zauna zaka samu yana da abun yi. Mutane suna ganin bai da mutunci, kuma ba haka bane kamewar shi, tare da bin tsarin da doka yasa ake ganin yana da zakewa.

          Kuma ko a gurin aiki ne yana yawan cewa, babu amfanin na baka hakkinka kaki sauke min nawa, ba zan maka hakuri akan hakkina ba, wannan yasa yake yawan koran ma'aikatan shi, amma kuma a haka yana musu ihsani. Toh basu gani yau da babu kamfanin zasu koka tunda yayi musu Alkhairi basu gani ba.

      •••
Yola.
Kwance take tana kallon dakin da take, yau kewar Noorh. Tashi tayi ta gangaro kasa, sanye take da wani doguwar riga me dogon hannu, amma kasar shi a tsage yake. Kana hango boxes ɗin ta fari kalar kayan, zuwa kirjinta kuwa, akwai botirin a rigar, sai dan igiyar da ta daure k'ugun ta fashi, yadda tayi kwalliyar kana ganin yan kananun boons ɗinta, a jikin rigar. Ta daura wani hular me kyau akanta.

Zama tayi Daddy ɗinta ya kalle ta, sannan yace mata.
"Ya dai baby Queen!"
"Babu dad mu yan wata ƙasa ce?"
Kallonta yayi sannan ya fara cin abincin shi.
"Dad tambayarka nake fa?" Ta faɗa tare da buga spoon din hannunta.
"Mahaifiyarki yar kasar nan ce, mu kuma annaba ne na kasar Algeria, Noorh kuma da iyayenta yan garin biskira ne, shi kenan!"

    Daga haka ya mike, kallon shi tayi cikin shagwaɓa tace.
"Dad yaushe zaka kai ni?"
"Idan kin gama Service."
   Daga haka ya fice daga gidan, ta zauna tana image yadda zata ga Zuri'ar su, dan haka cikin tsannanin farin ciki take shirya kome domin tasan idan ta tafi zata ga manyan masu kudin kasar kusan ba mamaki family ɗinta ne, haka ya saka take jin wani irin yanayi na shigar ta.

   And she promise idan ta fito one of large family house na kasar toh tabbas  sai taci Uwar Nazzir, dan haka take kallon yadda abubuwa zai tafi cikin jin dadi da farin ciki..And wat about Noorh? Idan kuma tana raye fa? Tabbas akwai matsala, domin idan taje Annaba sai taje taga yadda family ta suke.. tirkashi ga Mahir da Noorh! Mahir ya faɗa fa, Tasleem tana nata shirin cin Uban Nazzir, hmmmm
Yacin yawan Vote yawan page 🤨🤣 🙏🏼 Kuyi hakuri jiya anyi min rasuwa ne.....

Continue Reading

You'll Also Like

276K 17.7K 48
The feeling of being abandoned by one's own family was not unknown to Aadhira. She hates her family for abandoning her when she was only a newborn, l...
621K 20.7K 169
The young lady from the Xue family was talented and beautiful, and married the dream husband at the age of 16. They had a loving and harmonious relat...
55.7K 3K 22
If you knew what it felt like to have your entire life upended, that was exactly what Isabelle felt like right at this moment. From finding out you h...
BROTHERS IN ARMS By Arya

General Fiction

140K 8K 53
This is a story about three brothers. The eldest brother is serving his life for his nation while the other two brothers are following their eldest b...