TASNEEM 2 in Tasneem series✅

By ameeiyrah87

4.6K 129 38

"'Daliba ta a makaranta ze aura" "......Se da na gama kwalliya na sa kaya fa, sannan na fita nayi kwaskwarim... More

Introduction
2
3
4
5

1

456 26 16
By ameeiyrah87

Dai dai qofar wani gida Aryan yayi parking 'din motar sa, da murmushi ya kalli Tasneem Farha yace mata

"My love mun kawo gidan"

Ita ma murmushi tayi mishi sannan ta 'daga idon ta ta kalli gidan, gida ne wanda da ka ganshi kasan ya sha wahala matuqa, qofar shiga gidan an jingine ta ne saboda karyewar da tayi, daga gani dai masu gidan suna kara qofar ne kawai in dare tayi, wani labule ne wanda ya yayyage kawai yayi ma gidan sutura yadda ba'a hango mutanen cikin sosai, girgiza kai kawai Farha tayi sannan tace

"Dee ka kira ta to ta fito, nasan mun 'bata mata lokaci tana jiran ka"

Wayar shi ya 'dauka ya fara qoqarin kiran, be ida dialing number 'din ba kira ya shigo, cewa yayi

"To gashi nan ma tana kira"

Murmushi Tasneem Farha ta yi amma bata ce komai ba, 'daukar wayar yayi tare da yin sallama, banji me aka ce ba se dai Aryan 'din ne ya amsa da

"Ai ina qofar gidan ma, ki fito "

Kashe wayar yayi sannan ya 'daura hannun shi akan na Tasneem Farha, juyowa tayi da ga kallon window sannan tace

"Yadai? Tana ta jiran ka ko?"

Cewa yayi

"Uhm haka tace, wai tuntuni tana ta jira"

"Ai na gaya maka maybe tana ta jira"

"Ai gata can ma ta fito"

Tasneem Farha maida idon ta tayi dan taga wacece, gaban ta ne ya fa'di sanda tayi tozali da 'dalibarta a makaranta, qara ware ido tayi dan taga idan ba idon ta ne ke neman yaudaran ta ba, ai ko babu shakka 'dalibarta ce 'din dan ga yadda take tafiyar nan nata kamar zata qarye, kafin ta ce ma Aryan wani abu har yayi saurin cewa

"Tee ina zuwa, bari nayi mata iso"

Fita yayi a motar, Tasneem ko qara maida hankalin ta tayi dan ganin ikon Allah, yarinyar ce ta tako cikin karairaya da izza, sanye take da wani material sky blue, fitted gown ne kuma kayan ya matse ta sosai, duk wani halittar jikin ta a bayyane yake, fara ce sosai amma bata da tsayi, irin wa'dannan yammatan ne marasa jiki kuma wa'inda basu da girma, ta sha make up sosai a fuskan ta kamar zata je gidan biki, tun daga mota Tasneem tana iya jiyo qamshin turaren ta, tana isowa kusa da Aryan se ta ta'be fuska kamar zata yi kuka, Ita dai Tasneem bata iya jin abunda take fa'da ba amma daga ganin alama shagwaba take yi mishi, juyawa tayi alamun ta ji haushi, qarin gashin da tayi ne yasa Tasneem Farha sakin wani wahalallen ajiyar zuciya, a zuciyar ta kuwa cewa tayi

"Yanzu shi kuma abunda Dee ya kwaso mana kenan, Lallai akwai aiki, Allah gani gare ka, Allah kar ka ba yarinyar nan ikon cutar da mu"

Se da yarinyar ta gama yi mishi rangwa'da kisisina sannan suka nufo inda Tasneem 'din take zaune a cikin mota, suna kawowa se ta ja ta tsaya shi kuma ya qarasa dai dai bakin window ya leqo kanshi ya ce ma Tasneem

"Tee, ga Husna ta qaraso"

Tasneem tace mishi

"Dee in fito ne?"

"Eh fito muje"

"Okay"

Bu'de qofar motar Tasneem tayi sannan ta sako qafar ta 'daya waje, MashaAllah kawai za'a ce saboda qafar ta ta ha'du, ta saka flat shoe silver sannan qafar nata yasha lalle ja wanda ya zama maroon, 'daukar wayar ta tayi sannan ta fito gaba 'daya, madaidaiciya ce a wurin tsayi, sannan ba za'a kira ta fara ba haka zalika ba za'a kira ta baqa ba, kalan fatar ta me kyau ne dan daga ganin alamu tana kula da jikin ta, tana da jiki ka'dan wanda ake kiran irin su chubby, sanye take da doguwar riga na atamfa wanda yake peach ne amma yana da kwalliya navy blue, ta yi 'daurin dankwali sannan se ta yafa gyalen ta navy blue a saman kanta irin yadda matan aure ke yi, zagayowa tayi inda su Aryan suke tana yi musu murmushi wanda ya bayyanar da dimple 'din fuskar ta, qarasowa tayi inda suke sannan cikin fara'a tayi musu sallama tare da miqa ma wannan yarinyar hannu su gaisa, tun da take tunkarar su ta hango fargaba a idon yarinyar amma se ta fuske tayi kamar bata gani ba dan bata son yarinyar ta kasa sakin jiki da ita dan ta gano malamar ta ce, se a yanzu ita ma yarinyar ta miqa mata hannu suka gaisa, hannun Tasneem ya sha lalle maroon shima ga zoben gold a yatsun ta da wani bracelet silver me kyau, hannun wannan yarinyar na kalla na ga alamun bleaching a tartare da shi, fara ce amma se da ta qara da mai, irin wa'dannan matan ne wanda hasken jikin su baya isar su, Aryan ne yace

"Tee ga Husna, Husna ga uwar gida na Tee"

Gaisawa sukayi sannan Tasneem tace

"Husna ya gida, ya su mama"

"Lafiya lau kowa da kowa"

"MashaAllah, Yau dai na biyo shi inzo in ga Husna da yake ta bani labari"

"Ayyah Allah Sarki, aikam dai gani nan"

Wayar Tasneem ce ta fara qara se tayi sauri ta kara wayar a kunnen ta, waro ido na ga Husna tayi saboda ganin Iphone 11 pro, duk yadda ta qura ma Tasneem ido bata san tana kallon ta ba ta gefen ido ba, se da ta gama wayar sannan tace ma Aryan

"Dee Mami ce tace wai Airah ta dage ita gida zata je, ina ga dai daga nan can zamuje kawai"

"Alright Tohm, gara mu 'dauke ta kawai mu tafi gida gaba 'daya ma ai"

"Eh gaskia"

Murmushi Tasneem tayi ma Husna sannan tace

"Qanwa ta bari na je mota na 'dan baku wuri ku zanta ko?"

Husna ce tace

"Toh"

Shi kuma Aryan yace

"Ai ba inda zaki, tare da ke za'a yi labarin nan"

Husna bata so ba, ta so ya bar Tasneem ta tafi amma haka ya dage, hakan suka cigaba da tsayuwa suna magana wanda Husna amsawa kawai take ta yi a daqile, se da suka shiga suka gaida matar baban Husnah wadda itace mariqiyar ta saboda Mahaifiyar Husna ta bar gidan, ta amshe su hannu biyu biyu tana ta nan nan da su, se da suka gama sukayi sallama da Husnah sannan suka shiga mota, tsayawa tayi tana kallon su taga wucewar su, se da motar su ta bar layin sannan Husnah ta fara magana ita ka'dai

"Baqar makira, yau nayi niyyar muje shopping tare amma saboda munafunci da mugun hali da son ganin kwakwaf har da wani biyo shi, banza kawai"

Rungumo ta taji anyi, da sauri ta waiga ganin wacece, tana ganin qawar ta ce se tayi tsaki tace

"Kai Ramla ke fa kin iya wawanci wani lokaci wallahi, wallahi na firgita"

Ramla tace

"Kin 'dauka wadda kike zagi ce ta rungomo ki"

Harara Husnah ta watsa mata sannan tace

"Ashe maganar a fili ma nayi ta kenan, ke takaici ne ya ishe ni wallahi "

"Ai ina kallon ku tun 'dazu, se leqen ku nakeyi, wai ma tsaya ba Aryan bane yazo wurin ki?"

"Shine Mana"

"Amma se na ganshi da Aunty T Farha Ahmad, Yar uwar shi ce?"

"Wace Yar uwar tasa?, ke matar sa ce fa"

Zaro ido Ramlah tayi tace

"Matar sa fa kika ce, kut dama kinsan matar sa ce?"

"Ke ni kin ishe ni, kizo mu shiga ciki in kina son jin wani abu"

Wucewa tayi gaba tana juya jiki ita kuwa Ramlah na bin ta a baya tana hararan ta (dariya kawai nakeyi a zuciya ta nace qawayen bariki kenan wanda ba'a qawacen tsakani da Allah)

A haka suka shigo cikin gidan su Husnah, gidan baya da kyau amma kasancewar matar gidan me tsafta ce se komai ya ke a natse kuma a gyare, babu sallama haka Husnah ta fa'da cikin gidan tana harare harare, Matar baban ta Anty Zuwairah tana qoqarin fiffita wuta ta kalle ta ta girgiza kai, 'daki Husnah ta shiga ba tare da kalli Antyn ta ba ta wuce, Ramlah ce ma ta tsaya suka gaisa da Anty Zuwairan harda qoqarin cewa bari ta taya ta hura wutar, Anty Zuwairah tace

"Aa Ramlah barshi kawai wallahi, ai na ma gama"

Wucewa Ramlah tayi ta shiga 'dakin su Husnah, Khadija qanwar Husnah ta na zaune tana linke kaya ita kuma Husnah ta haye saman katifan su tana tauna chewing gum tana latsar waya, shigowar da Ramlah tayi ne ya sa Husnah 'dagowa ta kalle ta sannan ta harare ta tace

"Uwar kinibibi, tun 'dazu muka shigo amma kin tsaya se kin gama munafurci tukunna"

Murmushi kawai Ramlah tayi sannan ta zauna, Khadija ta gaida Ramlah ita kuma ta amsa cikin fara'a, Ramlah ta ce ma Husnah

"Huseey gaya mun please, na qagara inji wallahi"

"To ai se ki bari inyi wanka tukunna ko, se in zo in fa'da miki"

"Wai dama bakiyi wanka ba? Amma har kika iya yin kwalliya"

"Wallahi banyi ba, Ina bacci Aryan ya kira ni ya fa'da mun ze zo kuma se na kasa tashi inyi wanka, se daga baya na tashi na jawo kayan kwalliya na nayi sannan na shafa turare me qarfi, ke se da na gama kwalliya na sa kaya fa sannan na fita waje nayi kwaskwarima na 'dauraye qafa na da hannu na, ni brush 'din ma banyi ba, chewing gum na sa a baki na kawai"

"Chab'di jam, aiko kin bani wallahi Huseey, qazantan naki har ya kai haka"

"Ke Ramlah dalla banson irin haka, to meye a ciki, na ga dai na shafa turare ai"

Se yanzu Khadija ta tanka su tace

"Amma dai yaya Huseey babu kyau covering bad ordour fa da good scent, yana saka warin jiki"

"Inji ubanwa"

"Inji Teacher 'dinmu ta Home Management Anty T Farha"

"Qarya take yi to "

"Hmm gaskia dai ta fa'da miki Huseey"

Cewar Ramlah

Huseey tace

"Ai wallahi na lura kina son matar nan Ramlah"

"Kin manta ita ce Favorite Teacher na?"

Tsaki Huseey tayi ta sauko daga kan tsohon katifan su tace

"Bari in je inyi wanka, na tsaya ina biye ma haukan ku"

'Daukan wani zani tayi da na ga yayi duqun duqun saboda datti ta 'daura akan kirjin ta sannan ta fara cire kaya, bra milk ne a jikin ta amma saboda tsabar qazanta ya koma light brown, under wear skirt 'dinta ko duk ya zare saboda tsufa da rashin kula, kallon inner wears 'din ta kawai su Ramlah da Khadeeja ke yi, kowacce na so tayi magana amma ta kasa, har Huseey ta gama cire kaya ta 'dauki basket 'din wankan wanda shi ma yayi fari fari ya bushe da ruwan sabulu saboda rashin wanke shi, brush 'din ma a haukace yake, soson wankan kuma shima sabulu ne a cikin shi an kasa cire shi saboda qiwuya, fita tayi ta 'dauki bucket 'dinta, ganin shi tayi a wanke, komawa bakin 'dakin su tayi tace ma Khadija

"Ke kika wanke mun bokiti na?"

"Eh 'dazu na wanke shi, naga yayi datti ne sosai, Mama ce ma tace in wanke shi"

Husnah bata ce mata komai ba, ko godia ta kasa yi, inda Anty Zuwairah ta 'daura tukunya ta nufa, samun kofi tayi ta bu'de tukunyar ta iba ruwan sannan ta rufe tukunyar, bata qara ruwan ba ta sirka ruwan wankan ta shima da ruwan da Anty Zuwairah ta jawo zata yi wanki sannan ta shige bayi abunta, ko minti biyar bata yi ba se gata ta fito dai dai lokacin da Anty Zuwairah take fitowa daga 'daki, ba wanda ya tanka wani Anty Zuwairah ta nufi wurin tukunyar ta, ko da ta bu'de se ta ga an kwashe ruwan ciki, tasan aikin Husnah ne amma bata kula ta ba ta ibi wasu ruwan ta qara, Husnah ko bata ji da'di ba, so tayi Anty ta kula ta se tayi mata rashin kunya, amma sanin halin Husnah yasa Anty tayi kamar bata san me Husnah tayi ba, shigewa 'daki Husnah tayi, Ramlah tace mata

"Wai har kinyi wanka"

"Nayi mana"

'Dauko man shafawarta tayi ta fara shafawa, warin albasa man yake yi kasancewar shi man bleaching, Ramlah ce tace

"Allah yaso man naki ma ya kusa qarewa mu huta da warin albasa"

Husnah bata kula ta ba ta cigaba da shafa man nata, se da ta gama ta 'dauko wata rigar top ta sa sannan ta maida zanin kan qirjin ta a kwankwason ta, Ramlah ta sake cewa

"Zanin gado"

Nan ma dai bata kula ta ba, 'daukar wayar ta tayi ta ma Aryan text message sannan ta aje wayar, Ramlah ta sake ce mata

"Yauwa qawata fa'da min"

"Ai inda ban yi niyyar fa'da miki ba da bazance zan fa'da miki ba ko kuwa?"

"Eh hakane"

"To ki daina damu na zan gaya miki da kai na in na sarara"

Ta'be baki Ramlah tayi sannan ta cigaba da danna wayar ta ita ma.

******
A can bangaren su Aryan da Tasneem kuwa suna barin gidansu Husnah suka nufi gidan Mami wato Tasneem Matar Maheer (ta cikin littafin TASNEEM) wadda ta kasance aminiya a wurin mahaifiyar Tasneem Farha wato Hajarah, kasancewar Mami (Tasneem) a gari 'daya take da su Tasneem Farha shiyasa ake yawan kai Airah gidan, su Tasneem Farha suna zama ne a garin Kaduna inda ya kasance duk gari 'daya da 'yan uwan Aryan, iyayen Tasneem Farha ko a Kano suke zama, suna kan hanyan zuwa gidan Mami kenan se Aryan yayi parking a bakin wani super market da niyyar shiga siyan abu, Tasneem na zaune a cikin mota tana chatting se wayar Aryan tayi qara alamar message ya shiga, kallon wayar kawai tayi se ta maida kan ta wurin chatting 'dinta, kamar dai ta ga wani abu se ta qara kallon wayar, message ne daga H❤️ 'daukar wayar tayi ta fara karanta message 'din da ke kan screen 'din wayar, saqo ne kamar haka

"My Sugar, a gaskia banji da'din tafiyar da kayi da wuri ba, na so ace mun fita tare amma se ka tashi kazo da wata, ni fa kasan ina da kishi sosai wallahi, gaskia ka kiyaye"

Ta'be baki kawai Farha tayi sannan ta ajiye mishi wayar shi ta cigaba da hidiman ta, Aryan ne ya shigo cikin motar tare da cewa "Ya Allah!" Sannan ya tada motar, kiran wayar shi akayi ya 'dauka, bayan ya gama wayar se ya kalli message 'din da aka yi mai, kallon Farha yayi alamar rashin gaskia, ita ma kallon shi kawai tayi se tayi murmushi ta cigaba da chatting 'dinta, cikin qanqanin lokaci su ka iso gidan Mami, tun kafin su yi parking Airah tazo da gudu tana yi musu oyoyo, Aryan na parking Airah ta zagayo wurin Baban nata tana cewa

"Papeey Nah, I missed you!!"

Aryan ne yace

"Airiri nahh nima I missed you uwa ta"

Tasneem Farha ce tace

"Ni kuma bakiyi missing 'dina ba ko? Aucchh I'm hurt"

Tana yi tana faking fuskan kuka, dariya suka yi gaba 'daya sannan Airah tace

"Kema Ammeey I missed you"

"Daga baya kenan, Ai papeey kika fara gani, ba ruwa na dake"

A haka dai sukayi ta maganganun su kafin da ga bisani suka fito daga motan, cikin gidan suka nufa, tun daga bakin qofa suke jin Mami na kiran Airah, Suna shigowa Mami tace

"Zo nan 'yar rainin wayau, kinje kin zubar mun da powder kin mun barna ko?"

Se a yanzu su Aryan suka lura da yadda riga da hannun Airah ya 'baci da powder, Farha tace

"Haba no wonder shiyasa na ganta a waje ashe, kin yi ma Mami na barna ko Airah?"

'Boyewa Airah tayi a bayan baban ta tana kallon Mami, Aryan yace

"Oya say sorry Airiri in ba haka ba ba zan kai ki wurin Anty Noorie ba"

Da sauri Airah tace

"Sorry Mamiss"

Dariya suka yi gaba 'daya sannan Mami tace

"Wannan dai Mamiss 'din na rasa a inda ta samo shi, gashi kowa ya kama"

Farha tace

"Qyale ta Mami na, ina wuni"

"Lafia lau Baby mee"

Aryan ma yace

"Ina wuni Mami"

Cewa tayi da shi

"Lafia lau Aryanuu"

Qasa yayi da kai yana murmushi, Mami tace mai

"Da wancan dan rigiman ne nace ma Ayaanu da yanzu yana mun shagwaba, kuzo mu shiga ciki"

Shigewa ciki sukayi gaba 'daya, bayan sun gama gaisawa da Mami a haka suka zauna suna ta hira, ba su suka bar gidan Mami ba se da la'asar kuma direct gida suka nufa, suna shiga cikin gidan bayi Tasneem ta fa'da, wanka tayi ta tsaftace jikin ta sosai, tana fitowa ta sa kaya masu kyau ta feshe jikin ta da turare, Airah tayi ma wanka sannan ta shiga kitchen, nan da nan kitchen ya 'dau qamshi, Aryan ne ya leqo kitchen 'din yace

"Baby love irin wannan qamshi haka, ai se ki sa in kasa zuwa massallaci"

Ludayin miya Tasneem ta aje sannan tace

"Bana son zolaya Dee,kai dai kaje masallaci ka dawo kazo kayi wanka, kai ka'dai ne baka yi wanka ba"

"Sannan kuma inci abinci"

"Naji, je ka dawo"

Wucewa yayi ita kuma ta girgiza kai ta fito daga kitchen din, 'dauko magic coal tayi ta koma kitchen 'din, daura shi tayi akan gas sannan taje ta 'dauko kasko, kafin ta dawo yayi ja ya dau zafi, saka spoon tayi ta dauke shi ta sa a kasko sannan ta nufi hanyar 'daki, cikin qanqanin lokaci ta zuba turaren wuta gidan ya dau qamshin, tana zagawa da turaren a parlor Aryan ya shigo, cewa yayi da ita

"Wai ina Mama na ne?"

"Tana 'dakin ta tana assignment"

"Yau bazaki yi assisting 'dinta ba?"

"Ai dole na, so nake yi girki na ya qarasa se inje in duba ta"

"Okay ooo"

Hanyar 'dakin Airah ya nufa yana

"Airah nahh, Mama nahh! Wai ina Fatima Airah Ahmad Aryan ne "

Dariya Tasneem tayi tace

"Wannan irin dogon suna haka duk ita ka'dai, ita suna biyu baban ta ma haka "

Juyowa Aryan yayi yace

"Maman ta ma suna biyu gare ta ai, ai iyayen mu na ji da mu da suka mana nickname, kowa suna biyu"

Dariya sukayi gaba 'daya, Aryan ya tafi wurin Airah sannan Farha ta nufi kitchen bayan ta aje kaskon ta akan center table.

_____________________________

Husnah ce ke kwance akan tabarma tana danna waya, Khadija ko da Anty Zuwairah suna ta fama da girki, Anty Zuwairah na tsinke alaiyahu ita kuma Khadeeja tana gyara tsakin masara, Ajiye wayar ta tayi a gefe ta qara gyara kwanciya tare da fa'din

"Maman Khadeeja wai me zaku dafa ne?"

Ce mata Anty tayi

"Asma'u Fate ne za'a yi, faten tsakin masara"

"Chab!! Faten tsakin masara kuma? yau ma baban be da ku'di ne?"

"Wallahi kinsan abubuwan se a hankali, baya da ku'di amma dai 'dazu ya kawo shinkafa, to kinsan 'Yar hausa ce kuma wadda ya kawo tana da tsinta da yawa, kuma kin ga mun je gidan ta'aziya ba mu dawo da wuri ba shiyasa nace gara ayi Faten in yaso gobe ayi shinkafar"

Ta'be baki Husna tayi sannan tace

"Gaskia ni kam bazan sha Fate a daren nan ba, kuma kun cika iyayi, me wani amfanin zuwa gidan gaisuwan rasuwa tunda ba dawo da mamacin zakuyi ba, yanzu gashi kun ja ma kanka shan Fate"

Se a yanzu Khadeeja ta tanka tare da fa'din

"Gaskia yaya ki sauya irin maganar da kike fa'da ma Mama, tana iya bakin qoqarin ta fa, wannan tsakin fa yan uwan ta suka kawo mata shi, shi kuma wannan alaiyahun fa da ku'din da tayi ma mutane niqa 'dazu da shi ta samu ta siye shi, kina ganin injin 'din marka'den da ake samu ana rufa ma kai asiri se matsala yake badawa, da kyar aka samu akayi niqa biyu har aka samu ku'din cefane, in bazaki sha Faten ba ki barshi amma ba se kin gaya mana magana ba"

Husnah ce ta miqe tace

"Char uban nan!! wai Khadeeja ni kike fa'da ma irin maganganun nan, lallai yau zanci uban ki a cikin gidan nan"

Tana qoqarin miqewa tana zazzaga masifa Baban su yayi sallama tare da fa'din

"Nagode da zagin, kina ta'ba ta zaki ga abunda ze faru da ke "

A wahalce ya shigo gidan, da ka ganshi ka ga talaka, be tsufa sosai ba amma yanayin talauci ya sa girma ya taso mai, Husnah da ta san halin baban nasu se ta ja bakin ta tayi shiru, amma tana kallon Khadeeja cike da takaici, su Anty da Khadeeja gaida baban su kayi yayin da Husnah ta tashi tana tafiya kaman ana tura ta ta shige 'daki tana qunqunai.

Husnah bata fito daga cikin 'daki ba se da akayi sallar Isha'i lokacin har su Anty sun gama girki, da hijabi ta fito dag 'daki tana kalle kalle kamar mara gaskia, da ta ga babu kowa a waje se ta fice daga gidan da sauri, bata tsaya a ko ina ba se a gidan Mahaifiyar ta wacce ta haife ta, da yake gidan nasu babu nisa da inda maman ta ta kama tana zaman kanta, a bakin qofar gidan ta ha'du da wani mutum ya fito, kallon kallo sukayi sannan ta shige gidan da sauri.

Hello peeps ! The First Chapter Is Here!!!

Happy New Year !

Allah ya sada mu da albarkar da ke cikin wannan shekarar, ya sa tazo muna a sa'a Ameen

Da fatar kun nisha'dantu da wannan page 'din, Don't forget to vote, share and comment , I love you all.

Aisha Ameerah❤️

Continue Reading

You'll Also Like

1.5K 423 36
A Koda yaushe muna Jin labaran zama da kishiya Mai ban mamaki da ban al'ajabi....Labarin MAHREEN labari ne na musamman Wanda zai fad'akar, ya nishada...
27.1K 1.4K 29
LABARI NE WANDA YAKE DAUKE DA BOYAYYAR SOYYYAH, BOYYAN HALI MARA KYAU,DA TSANTSAR BIYAYYA.
13.4K 802 15
كاتبة مبتدئة أول رواية لي واتمّنى ان تنّال إلى اعجابكم كُتِبت بقلم الكاتبة:جنى الفيصل✍🏻
426K 26.5K 19
© 2018 All Rights Reserved Yusrah's life takes a dramatic turn when her parents decide to get her married to Masoud Abdullah. That wasn't the life Yu...