*INTELLIGENT* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
(On word together)
*ASALINA*
*Story* *and* *writing*
By
*FIDDAUSI* *SANI*
( *damsel* *feedorh* )
*TSOKACI*
_Wanann_ _labarin_ _kirkirarren _labarine__ _banyishi_ _don_ _cin_ _zarafin_ _kowaba_ ,, _saboda_ _haka ban_ amince __ajuyaminshi__ _takowane_ _fuska_ _batare_ da _izininaba_ _akiyaye_
~Kuyi~ ~hakuri da~ ~dakatawa~ ~danayi~ na ~rubuta~ ~muku~ ~mugun~ nufi ,, ~hakan~ ~bayana~ ~nufin~ ~nabarshi~ ~bane~ ,,, ~zanci~ ~gaba~ ~insha'allah~ ~ngd~
🅿️:1️⃣
بسم الله الرحمان الرحيم
Baba dan Allah katemaka mukai ummana asibiti wallahi zata iya mutuwa,,yarinya ce yar kimanin shekara 14 take kuka tana girgiza mahaifinta Wanda shi kansa kukan yake amma babu alamun cewa zaibi yarinyar da take kuka tana jan hannunsa,,,ganin datayi baida niyyar temakonta ne yasakata sakeshi tu ruga aguje ko kallon gabanta batayi burinta kawai tasamu Wanda zaitaimaketa ,,yakai ummanta asibiti ,,domin tanaganin idan tarasata to tayi bankwana da farinciki,,,haka taketa taron mutane amma babu Wanda yakulata ma,,,gajiya da hakanne yasakata sadakarwa kila ma ummanta tarasu yanzu tasan halin da tabarota aciki a sukwance tanufo hanyar gida .
A soron gidan taga kanwarta talafe ajikin bango tanata faman kuka ,,,shikenan tafada tana mai razananniyar kara,,Wanda sanadiyyar hakan ne yasaka kanwarta lura da shigowarta ,,,umma ta mutu ko fadila,,shikenan yanzu babanmu yakasa taimakonmu bare wani ,,,
Tafada tana mai rungume kanwarta " a,a yaya Humaira ummanmu tasamu sauki tayima bacci shiyasa nafito nan ,,,wani boyayyar ajiyar zucia ta sauke ,,sannan tace " to meyasa kike kuka bayan tasamu lafiya " yaya ummansu faruk ce tazo tanata zagin umma ,,wai tayi abun kun....sauri Humaira tayi tarufe mata baki saboda bataso taji karashin maganar tasan koma menene to ba alkhairi bane,,kiyi hkr fadila mu namu kaddarar kenan duk wannan baidameniba kawai fatana ummanah tasamu lafiya ,,a wannan karon dole umma tafada mana ko itadin wacece ,,ko zamusamu sauki aranmu ,,yanzu taso mushiga ciki
da sallama suka shiga amma babu Wanda ya,amsasu ,,duk da cewa kuwa matar da suke kira maman farouk tana zaune 'yayanta sun kewayeta ,,sannuku da gida cewar Humaira " andawo yawon tazubar wato da kinga ciwon uwarku yatashi se kizagaya wurin yan iskan samarinki kuyi lalata kidawo ko ,,sauri Humaira tashige dakinsu ,,dama abunda take gudu kenan tasan matukar zata fita tadawo to abunda matar mahaifinta kejifanta dashi kenan
A,zaune tasamu mahaifiyarta alamar falkawanta kenan,,,da gudu suka rungumeta,,suna jeramata sannu itadai kai kawai take dagamusu,,,domin kuwa bazata iya maganaba
"Sannu ummah mezakice,,Humaira ta tambayeta cike da kulawa ,,girgizamata kai tayi alamar babu komai
Shiru sukayi suna kallonta ,alamar akwai maganar da sukeso suyi da,ita ,,duk lokacin da sukayimata irin wannan kallon tasan me sukenufi,,wannan dalilinne yasakata murmishin karfin hali,,,cikeda dauriya tafara magana " Mamana nasan me kukeson kuji,,,amma kisani bawai naboye muku saboda wani abubane,,,a kwai lokaci idan yayi zakusan nidin wacece,,,zaku kumasan dalilinda yasa nake zaune anan bannemi danginaba,,kunga ga kiran sallah anfara maza kuyi sallah ,,fadila tawuce makaranta ,,ke kuma zan ayke kine,, tashi sukayi
Bayan sungama salla suka gaisheta tare da tambayarta jiki,,''jiki alhmdullah naji sauki ,,fadila maza kiwuce makaranta gada kiyi latti a dakarmin 'yar auta'' kai umma kinaji da autarnan taki kuma gashi ko ba,a bugeta saboda lattiba nasan za,abugeta akan rashin karatu wasa yayimata yawa,cewar Humaira,,,turo baki fadila tayi '' ni haskiya yaya Humaira kibar maidani wata Mara kokari ,,kaf a ajinmu malaminmu yace nafisu kokari ,dariya sukayi dukansu ummah "tace kyaleta ita kanta kinfita kokari yanzudai tashi ki wuce daukar jakanta tayi tawuce ,,,shiru dakin yayi. Zuwa can Umma ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Humaira wacce tayi kasa dakanta ,,tasan bawai Umma ta tsaidata saboda akebane sedai idan zasuyi magana ne Wanda bataso Fadila taji ,,,seda Umma tagama nazarinta sannan tace Humaira waye Wanda ya,aikomin da magani ,,kallon rashin fahimta tayimata tace " bayan kinfita Sega yaro an ayko da magani yace abawa Humaira nifa nafara rashin yarda dake,,,aduk sanda ciwona zaitashi sai ankawomin magani kuma kice ke bakisan wayake kawowaba
Its ur feedorh💘
