Part 1

1.1K 32 0
                                    

*MATAR NASEER...*

     *NA*

*AISHA ALTO*

_Wattpad:Aisha Alto Alto_

*Assalamu Alaikum Fans, my New Book (MATAR NASEER)* *writing will commence today In shaa Allah. I seek Allah's guidance throughout the periods of writing this piece and I Pray that ALLAH WILL MAKE IT A SUCCESS*

*NOTE*
*ANYTHING ATTEMPT TO COPY OR TRANSFORM THIS BOOK WITHOUT THE CONSENT OF THE OWNER (Aisha Alto) WILL BE CONSIDERED A CRIMINAL ACT PUNISHABLE BY THE LAW. AND ACTION WILL BE TAKEN IMMEDIATELY. ©2020*

_Bismillahir rahmanir rahim_

_1_

*KANO*
_Bichi Local Goverment_

Yarinya ce yar kimanin shekaru bakwai durƙushe agaban makara da gawa a ciki an shiryata tsab cikin likkafani tana rusar kuka mai tsuma zuciyar duk wani mai imani tana faɗin "Umma... Ummata ki tashi..ki tashi ki min magana don Allah...Nasan kina jina Umma..kice su warware miki abunda suka naɗe miki jiki dashi..Ummata!...ki tashi kinji..?" Ta faɗa da ƙarfi tana kuka sosai tare da girgizata lokaci ɗaya tana ƙoƙarin yaye likafanin dake lulluɓe a jikinta, da sauri wata mata daga cikin matan dake zaune a ɗakin ta miƙe ta kamota jikinta tana matsar ƙwallar tausayinta take faɗin "Kiyi haƙuri *JALILA*... Ummanki ta tafi kiyi mata addu'a shine kawai abunda tafi buƙata yanzu daga gareki kinji..?" Ta faɗa tana rungumeta a jikinta tana shafa bayanta alamar lallashi, wata irin zabura ta sake yi ta rarrafa ta koma gaban gawar ta ƙura mata ido ƙirrr kamar mai nazarin wani abu ajikinta, can kuma sai ta juya tana kallon wannan matar tana girgiza kai tace "A'a Maman Sa'ade.. Ni nasan Ummata na nan babu inda zata iya tafiya ta barni..." Ta faɗa a hankali tana gyaɗa mata kai cike da tabbatarwa. Kafin ta sake duƙawa akan gawar a hankali tana faɗin "Ummata ki tashi kinji... Ai nasan barci kike yi anjima kaɗan zaki tashi ki yi min wasa da tatsuniya... Kuma kince dama zaki kaini Gwarzo gidan Kawu dan in ga Yaya Naseer... Ummata ki tashi mu tafi kinji..." Ta faɗa a hankali tana ƙara girgizata da ƙarfi, ganin bata motsa ba yasa ta sake sakin wani marayan kuka tana girgiza makarar. Gaba ɗaya matan dake ɗakin sai da suka hau sharar ƙwallar tausayinta.
Ta daɗe a durƙushe tana kallon gawar kafin ta koma can gefe guda ta manne da jikin bango gwanin tausayi ta saki wani marayan kuka tana kiran "Ummata... Ummata... Don Allah ki tashi mu tafi... Ummata ga Kawun Gwarzo da Hajja sun zo tun ɗazu kina barci... Ki tashi mu tafi... Karsu tafi su barmu..." Ta ƙarasa faɗa haɗe da tura kanta a tsakankanin cinyoyinta tana gunjin kuka.

Maza ne su biyar suka shigo cikin ɗakin domin fita da gawar waje a sallaceta don a sadata da gidanta na gaskiya, matan dake ɗakin duka suka miƙe tsaye suna salati da yi mata addu'ar fatan dacewa.

Jalila na ɗagowa ta ga za'a ɗauki makarar da Ummanta ke ciki ta miƙe a zabure da mugun gudu ta matsa gabansu tana faɗin "Ina zaku kai min Ummata...? Don Allah karku fitar min da ita, ku bari ta tashi mu tafi tare da ita.." Ta faɗa tana riƙo babbar rigar mutumin da ya tsugunna domin ɗaukar makarar tana ƙoƙarin janyesa take faɗin "Kawu ina zaku kai min Ummata...? Ku bar min ita barci take yi zata tashi..." Riƙota wata mata dake zaune a gefe  tun ɗazu tana matsar ƙwalla tayi tana girgiza mata kai ta ƙanƙameta tsam a jikinta ta rushe da kukan itama tana faɗin "Allah ya jikanki Hajara Allah yasa kin huta.. Halinki nagari yabiki.."

Wata zabura Jalila ta sake yi zata miƙe matar ta sake riƙota ta ƙanƙameta tana girgiza mata kai don kuka yaci k'arfinta ta kasa furta komai. Ɗagowa tayi daga jikinta hawaye na zuba daga cikin idanunta tace "Yanzu shikenan Hajja ina gani zasu tafi da Ummata... Ban san inda zasu kai min ita ba..?" Ta faɗa a hankali tana zamewa ƙasa ta kwanta hawaye na bin gefe da gefen idanunta yana gangarawa cikin kunnenta. Ɗagota Hajja tayi ta ɗorata a jikinta ta rungumeta tana share mata hawayen fuskarta, buɗe idanuwanta tayi ta tsura mata ido tana kallonta kafin ta zame ƙasa ta zauna tana faɗin "Hajja nima to tashi ki kaini zan bisu inda suka tafi kai Ummata.." Ta faɗa tare da jan hannunta alamar ta miƙe tsaye su tafi.

MATAR NASEERWhere stories live. Discover now