Sai da ya share barcina shi tukun kiran sallar magabri ya tashe shi.
     
"Wancan Ustadz din nan yana da katon voice!"
        A hankali ya bude labule yaga yadda akayi ruwa sosai, yana son yanayin sanyi, sabida tana sanya shi farin ciki, Infact ma yanayin sanyin damina tana kara mishi sanin cewa shi din namijine cikakken mai lafiya.

   A yanzun haka bai ki a ce yana da matar shi ba. Wacce da zaran anyi ruwa yazo kusa dashi. Amma ina kallon mata yake marasa sanin fa'idar so, baya son macen da zata so shi ya fi dacewa yace yana sonta.

         Ban daki ya shiga yayi wanka sannan ya shirya tsaf, cikin kananun kaya kafin lokacin zuwa dinner yayi.

        Yana fitowa yaga kowa a saman dinning table, share su yayi dan yasan Devanah ce tayi girkin.

        Diban Whiter rice tayi da vegetables sauce, sai coslow ta kawo mishi.

    Kallonta yayi dake babu masu lura dasu kowa na cin abincin sa ne, ya fincikota zuwa kirjinshi kasa kasa yace.
"Bana son Kona fix din gashin kanki da kuma nail dinki, shi yake sani jin kyamar cin abincin ki, Kinga duk inda zanje zan dawo naci abincin Mommah, kina sona but ya kamata ki koye yadda zaki kula da abinda zanci."

          "Am so sorry! Ba zan kuma ba."
         Jan abincin yayi ya fara ci, har ya koshi, zama suka yi ya janyota sosai dan ya lura yana son haka, daura kanta yayi a cinyar shi yana bata labari, wanda dayawa akan ibadarsu ba

      
    
            Wannan ba shine matsalar ba, ita kawai ya furta mata cewa.
Ina sonki. Shine damuwarta. Amma gayen nan ya shareta ya cigaba da bata labarin kanzon kurege.

             Mik'ewa tayi zaune tace.
"Baka da wani labari sai na Ibada da Addini, ni bashi ne damuwa na ba Bature ina matuƙar sonka, wanda zai iya sanyani kashe duk wacce kace kana so, Bature AM ready to take ko wani irin kalubale akanka, Matukar wata ta shigo rayuwarka zan kasheta kuma zan kashe banza. Tunda

Baka fahimci how many years na d'auka ina jigila da sonka."

    Juyawa tayi zuwa ga Father tace.
"Father! Na rantse da Yesu me tsarki bazan tab'a barin Bature ya hadani da wata mace na, koda kuwa zata zame min ajalina Father ka gaya mishi na kai makura gurin son shi sai yaushe zai furta min yana sona."

   Mik'ewa yayi zai fita, Father ƴace.
"Abraham! My Son!"
  Tsayawa yayi cak, tare da kallon Bishop.

     "Meye laifin ta?!"
         Ya tambaye shi a sanyayye,
         "Bata da matsala, kuma ni bawai bana sonta bane, ban san ya nake jinta bane a raina, Father  trying to love Devanah na kasa, Father bani ke son Devanah ba, Brother na shi yake sonta, but am."

             "Bature! Meye laifina?!"
     "Ita soyayya abace da kana iya jin shi koda baka tare da masoyin ka, Devanah idan bana tare dake Mantawa nake da duniyarki Devanah baki cikin ruhina, Kiyi hakuri ɗan ruhin me tsarki Yesu Almasihu."

          Fasa ihu tayi tare da Fad'uwa a kasa tana birgima, tsaki Joel yayi cikin fada yace.
"So what dan yace baya sonki! But am still love you!"

     "Hell you da love din banza da wofi!"

      Haka Devanah ta hauka, har ya fito daga sanye da dark grey suit, sannan ya durkusa ya d'agota.

          Kura mishi ido tayi ta kuma sake wani Irin kuka, me ban tausayi.
"Kace baka sona?!"

  Sosa goshinsa yayi sannan ya tsallake ta yayi tafiyar shi.
       ---
Husnah. POV

       Innarmu ce ta koma gida ni na zauna a jikin Baba wanda bai da Alamar farfaɗowa.

               Kura mishi ido nayi kwalla na zuba daga idanuna, na ƙasa fahimtar kome dan gani nake kamar nice silar fadawar shi wannan halin rayuwar, Baba yayi spendin all Rayuwar  shi for my Education but lokaci guda kome ya juya up side down. Duk sabida ni.

BAHAUSHIYA.....!?Where stories live. Discover now