2nd, June, 2020AD 10/10/1441AH
JIGON LABARI
Littafi ne da aka shirya don nusarwa a kan kyawawan halaye da kishiyoyinsu, tare da hannunka mai sanda a kan kafatanin al'ummar musulmi baki ɗaya irin yarda sakaci ya sa martabar musulmi ta faɗi.
SANARWA!
Na rubuta wannan labari ne don raha, faɗakarwa da kuma ilimantarwa kawai. Ba ni da wata manufa daban, kuma ba na fatan mutane waɗanda suke ganin kamar wani labari ya shafesu, su ɗau abinda zafi. Idan akwai darasi, toh zai fi mana amfani idan aka ɗau darasin kuma a yi amfani da shi domin shugabanci, zamantakewa da rayuwarmu su kasance ingantattu.
Wannan ita ce babbar manufata.
Ina tabbatarwa da duk masu karatu cewar dukkanin waɗannan labarai nawa ne, kodayake za ta yiwu na samu matsashiyar ne daga wa su al'amura na rayuwata ko kuma daga zantuka ko rayuwar wa su mutane daban da na ji a wani guri da tarihi.
SHAWARA
Idan akwai wasu ƙungiyoyin rubuce-rubucen littattafai ma su sha'awar su yi amfani da wani sassa na labarin ko haɗaka tare dani, ina fatan za su tuntuɓe ni domin mu duba hanyoyin da suka fi dacewa a yi wannan hidima cikin nasara.
Assalamu Alaikum.
SHAFIN FARKO
Aakifah Othman, shekarun ta ashirin da huɗu, ta fito daga jihar Kaduna a tarayyar Nijeriya.
Ta haɗu da mijinta mai suna Ibrahim a sa'in ta na cikin shekara ta biyu a Jami'a, (University) zuciyarta ta kasance cikin tsatsa (Broken Heart) a sanadiyyar rugujewar soyayyar da ta yi da mutane (Broken Relationships) daban-daban, kuma a cikin wannan yanayi ne ta haɗu da shi mijin nata.
Toh, sun fara ne da ƙawance a tsakaninsu kafin daga bisani ya juye zuwa ga soyayya, da fari ta yi tunanin ta watsar da shi domin a kafar sada zumunta su ka haɗu. (Social Media)
A gaskiya Aakifah ba ta ɗauke shi da muhimmanci ba saboda ta yadda su ka gamu, amma cikin lokaci ƙanƙani alaƙarsu ta yauƙaƙa.
Ibrahim ya kasance hafsan hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, (NDLEA Officer) kuma duk da yanayin aikinsa ya na samar ma su da lokutta na ɗebe kewa da haɗuya ta zahiri.
Aakifah ta na cikin sabuwar duniya, ya maida ta tamkar sarauniya, don haka ta zamto koyaushe cikin farin ciki. Bugu da ƙari, idan aka zo batun hadima ba ya da ƙwauro, bai taɓa nuna gazawarsa wajen hidimta mata ba, kai sai da aka zo matakin da kwatsam! sai Aakifah ta ji saƙon kuɗi (Alerts) a asusun ajiyarta (Account) ba tare da ta buƙaci hakan daga gareshi ba.
Aakifah da Ibrahim ba su taɓa samun hatsaniya ba a tsakaninsu har izuwa lokacin da ya fara mata maganar neman aurenta, da farko Aakifah ta yi zaton wasa yake yi amma da ta umurce shi da ya turo magabatansa kuma ta ga ya aikata hakan, a sannan ne ta gasgata batun sa.
Magabatan nasa sun yi duk abin da ya kyautu na bibiyar aure musamman a al'adara su ta Fulani, Aakifah ta kasance cikin farin ciki matuƙa, su ma kuma ahalinsa sun yi murna na ganin cewa ya samu kyakkyawar mace, duk da cewa shi ma fagen kyau ba baya ba.
Aakifah ta samu matsala a makaranta saboda ita ɗalibar kimiyya (Science) ce a sa'ilin da take matakin sakandare (Secondary School) amma sai a Jami'a (University) aka yi rashin sa'a aka sauya mata sashen karatu zuwa ɓangaren zane-zane, (Architecture) wanda hakan ya sa ta canja fannin karatu zuwa inda tafi ƙwarewa, dole ta dawo baya domin ta ka sa ci gaba a ɓangaren da aka batan. Aakifah kuma ta na ƙoƙari sosai bayan ta sauya zuwa ɓangaren da ta fi so.
Watarana su na tare da Ibrahim sai ta tambaye shi cewar ya batun ci gaba da karatu bayan sun yi aure? Nan dai ya tabbatar mata da cewar zai sanya ta a wata makarantar daban bayan sun yi aure sun sauya garin zama.
Wannan yaƙini na Ibrahim ya daɗaɗawa mahaifiyar Aakifah rai sosai, na ganin ya aminci ƴarta ta ci gaba da karatu bayan aurensu, wanda ba kasafai ake samun mazan da suke bari matansu su ci gaba da karatu bayan aure ba, musamman a nan arewancin Nijeriya. Ita ko Aakifah daman abin bai zame mata wani sabon lamari ba domin bai taɓa watsa mata ƙasa a idanu ba, kuma ta yi imani da shi.
YOU ARE READING
LABARI NA
RandomGodiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki da manzonsa Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su ƙara tabbata a gareshi, wanda ya ba mu iko da fito da wannan littafi ga jama'a domin ya zama abin ɗebe kewa da nishaɗantarwa yayin karanta shi.
