BABI NA BIYU

1.1K 103 2
                                    

*NANNY..!*
_(Mai Reno..)_

*Alkaluman:*✍️

*AISHA ALTO*💞
*JAMILA UMAR(Janafty*💕

'''Wattpad:Janafnancy13 or Aisha Alto'''

_*DEDICATED TO OUR SWEET UMMI💔KHADIJA SALISU YUSUF..LVUSM💘*_

*BISMILLAHIR RAHAMIR RAHIM*

       *BABI NA BIYU*

  Tun bayan daya dawo daga masallaci shida Bassam lokacin 7 saura na safe, kai tsaye ɗakinsa ya koma ya iske Naila ta tashi tana ta kuka, ɗaukanta yayi yana lallashinta ya shiga toilet da ita ya tuɓe mata kaya ya zage yayi mata wanka tsab domin taji daɗin jikinta amma duk da haka Naila 'yar wata goma sha ɗaya bata bar kuka ba daga gani yunwa takeji shiyasa yana gama mata wankan ya naɗota cikin towel ya sauko ƙasa zuwa ɗakin Mufeeda yana ƙwala mata kira.

Iya dake kichen ta fito jin yana kiran Mufeeda agaggauce in kaji ance Iya zaka zata tsohuwa ce ko ɗaya matashiyar dattijuwa ce mai kimanin shekaru hamsin da wani abu kawai su Basma ne ke kiranta Iya tun sanda Mami ta aiko ma Farida da ita daga Kano, shine kowa ya kama.

Ganin Tahir da kanshi yasa ta washe baki tana faɗin "Alhaji kai ne..? Kar dai 'yar rigimar ta tashi da kukanta yau, barka da safiya..?" Yana murmushi ya ranƙwafa yana faɗin "Ina kwana Iya..?" Ta amsa cike da jin daɗin yadda Tahir ke girmamata da darajata, take faɗin "Hala rigima Naila keyi bata ga uwarta ba..?" Yana sosa kai yace "Eh wallahi Iya inaga yunwa takeji ne, na mata wanka amma har yanzu bata bar kuka ba shine nazo zan bama Mufee ita ta bata madara ko tayi shiru.." Iya ta miƙa hannu ta karɓeta tana faɗin "Eh kuma da yunwar inaga bari na dama mata inaga Mufeeda barci ne ya kwasheta don nima yau najita shiru bata fito ba..." Miƙa mata ita yayi kafin yace "To Iya..." Daga haka ta juya ta nufi ɗakin Mufeeda inda kayan madaran Nailan suke da komai nata, shi kuma ya juya ya haura sama.

Wanka ya shiga yafi minti talatin kafin ya fito domin Tahir akwai daɗewa wajen wanka, yana fitowa ko mai bai tsayawa shafawa ba don Tahir kwata kwata baya ƙaunar shafama jikinsa wani abu, wardrope ɗinsa ya buɗe ya ɗauko ɗaya daga cikin fararen gezner ɗinshi ɗinkin tazarce, wanda ya amsheshi sosai aikin jikin shaddar baƙi ne,  hular kansa zanna bukar mai zanen baƙi ce, haka rufaffen takalmin ƙafarsa ma baƙi ne, sai kyakkyawan haɗaɗɗen baƙin agogon fatar dake hannunsa na kamfanin Rado, shi kanshi Tahir daya kai duban kanshi a cikin madubi sai da ya murmusa a ransa yasan cewa tabbas shi mai kyau ne kuma ko a cikin maza sai an tona uwa uba kuma Baba Hakimi zaiji daɗin ganinsa yau cikin shigar manyan kaya.

   Yana gyara zaman hulan kansa wayarsa riƙe a hannunsa yake saukowa daga saman step ƙamshin turarensa na Man na tashi tun kafin ya ƙariso, Basma da Bassam da Mufeeda wacce ke goye da Naila bayan ta bata madaranta ta sanya mata wata bulawus mai kyau tayi shiru ta goyata ram a bayanta, haka itama tana sanye da riga da siket na atamfa cikin wanda Daddy ya ɗinka musu ita da Basma, sai Iya dake gefe suna zaune bisa wani ƙaton ƙayataccen teburin cin abinci mai kama dana alƙarya guda, dama haka aƙidar gidan Tahir yake ba'a nuna bambamci da bare dana gida duk ɗaya ake, kowa dake gidan, in ka ɗauke Megadi da Direba ne kaɗai basu haɗuwa suci abinci tare Farida kuma bata damu ba, don bata cikama zama agidan ba balle ra'ayin Tahir ya dameta, tun Iya da Mufeeda basu saba ba har sunzo sun saba domin dukkansu sun haura shekara biyu a gidan..

Tun daga nesa yaran suka zuba mai ido suna kallonsa harda Mufeeda wacce duk sanda taga Tahir sai taji ta raina duka mazan duniya domin ya gama cika kowani mizami da zati, ga kyau ga asali ga nasaba da kyan hali har misaltawa takeyi a cikin ranta Allah ya bata miji irin Daddy wanda ya iya ɗaukan wanka da gayu, tunaninta ya katse ne sanda taji su Bassam na gaisheshi, amsawa yayi yana shafa kan Basma yana faɗin "Babyna kin tashi lafiya..?"

NANNY Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin