Peg 2

495 35 0
                                    

💓💓INDO AISHA💓💓

               *LITTAFIN*
              Nafisat Aliyu
          (Ummuh fadimah)

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________________*
©🎆
*AL'UMMA WRITER'S ASSO...* ✍🏻

  _A• W• A•_

_{{Al'umma writers_
_Kungiya daya tamkar da dubu farin cikin mu mu fadakar da Al'umma domin su farfado sugane   gsky al'umma sai dan Al'umma  Allah ya bamu ikon fadakar da Al'umma}}_
https://www.facebook.com/Alumma-Writers-Association-101394218126525/?referrer=whatsapp
*_________________________________________*

Peg 2

Da gudu abuwa ta isa Gida tana wani irin kuka me bala in cinrai
Hankalin Gwagwgo atashe tazo ta daga yar tata tana tambayar ta abinda ya faru abuwa taki magana kuka kawai takeyi
Ana haka saiga su talatu sun shigo cikin gidan Gwagwgo tana ganin su tayi wajen su tana tambayar su me yasami autar tah
Talatu tace ba indo bace muka ganta Chan tana shashancinta abakin rafi shine abuwa tace tayi sauri taje ta kawo miki ruwa kina jiranta ba
Shine tace bazataje ba aiba tsoronki takejiba kuma ta dinga zagin abuwa wai harda cewa abuwa me kirar maza
Kutumar babbar...... Wata irin ashar Gwagwgo takeyi tana cewa wlh yau saina ci kaza Kazan uwarta shegiya gantalalliya
Abuwa kuwa ido suka hada da kawayenta sukayi dariya batare da Gwagwgo ta ganiba talatu da jummai sukaci gaba da ziga Gwagwgo ita kota ta hau ta zauna da ram
Abuwa saifama kuka takeyi su Gwagwgo na lalla shinta

Jiki amace ta shigo gidan tana bin bango chanta hango abuwa kwance ajikin gwagwgo
Saifaman shagwaba takeyi tana lallashin ta
Yawwa Gwagwgo kinga shegiyar nan ta dawo
Ai Gwagwgo jikin ta har cira yake saboda masifar da ke cinta dama ya lafiyar giwa bare tayi hauka

Dan girman Allah Gwagwgo kiyi hakuri wallahi abuwa ce ta tureni tulun ya fashe
Wata zabura abuwa tayi tanacewa kinde jiko Gwagwgo barni da ita kinji yar albarka kede kwanta ki huta

Wata irin fusga Gwagwgo tayiwa indo ta watsar da ita atsakar gidan nasu icce naci da wuta ajikinshi Gwagwgo taciro taci gaba da dukan ta dashi
Indo tun tana Iya ihu da karfi har saida muryarta tade na fita saida iccannan ya babbale a jikinta tukun ta kyaleta lokacin ko motsi me karfi indo bata iyawa

Batasan Iya dadewar datayi ba acikin wannan haliba saukar ruwa kawai taji ajikinta da kyar ta dago ido ta kalli ko waye abuwa ce tsaye akanta tana Binta da wani mugun kallo yunkurawa tayi ta mike da kyar tana hada hanya tabi hanyar dan akurkin ta tana gab da shiga dakin taji Gwagwgo ta buga Mata wata irin tsawa me furgitar da mutum da sauri ta juyo tana kallonta
Bazakibar kallona ba da wa innan shegun idanun naki ba mayya kawai
Dukar da kanta tayi kasa da sauri tabar kallonta
Da kike kokarin shigewa daki ubanwa zeyi miki wannan aikin
Simi simi ta juya ta dauki tsin tsiya tafara shara tanayi tana nishi tanagama sharar taje ta hada kwanonin ta wanke ta dauki tsawan lokaci tanayin aiki kafin ta gama komi ga zafin Rana na dukanta ga jikinta gadaya ciwo yakeyi mata

Bayan ta gama taje deden kofar dakin Gwagwgo a hankali tace Gwagwgo na gama kingama duka eh ta yunkura zata tashi taji maganar abuwa tana cewa Gwagwgo kisata ta wanke min kayan da zansa inje dandali in anjima kinsa yau akwai bakin birni kuma zasu zo kalloh kinga ma kila insamu wani yace yana sona ko ya kaini birni (wayaga meroh zata birni🤪)

Indo de tajuya ta cigaba da tafiya taji ihun Gwagwgo tanace kizo kije ki wanke Mata kayanta ko bakiji ba tace naji amma wallahi Gwagwgo yunwa nakeji ki taima kamin da abinda zanci sannan
Kajimin shegiyar yariya to anki abaki abincin saikinyi wankin rabuda ita Gwagwgo bakin ciki takeyi Dani aiko zai kashe ta kamar yanda ya kashe uwar ta inno

Haka dole ta kwashi kayan takoma cikin ranar ta wanke su tayi tana gumi saboda mugun ta irin ta abuwa harda wankakku ta hada Mata
Sai yamma likis ta gama wanki kuma har lokacin bata sama cikinta komi ba sai ruwa gashi sallah ko guda bata samu da maryi bah
Tana gamawa tayi alwallah ta shige dakinta da sauri domin yin sallah
Tana idarwa ta fito taje madafin su wani bakin busashshen tuwone tsabar huce war da yayi miyar ma harta bushe ajikin shi

Haka ta zauna gefen murhu ta dinga sassakar tuwon nan harya kare tawanke hannuta da kwanon ta fito tana fitowa taga Gwagwgo na irga fura acikin wata fanteka kiranta tayi ta matsa kusa da ita tace gata nan ta murtala bakwai ce da goma kuma wallahi daya inta bace koki ka dawomin da ita jikin ki saiya fada miki........

Yawan comments
Yawan typing

Read & share pls


💓(Ummuh fadimah ce)💓

INDO AISHA Where stories live. Discover now