EPISODE FIFTEEN&SIXTEEN

231 27 0
                                    

⚜BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION
-{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}-

https://www.facebook.com/Zauren-Brilliant-Writers-Pans-111419110389493/
BAMBANCIN ƘASA
{Battle to reach}

Book By:SIYAMAIBRAHEEM
WATTPAD:FOLLOW@SIYAMAIBRAHIM

بسم الله الرحمن الرحيم
EPISODE:15&16

HISTORY OF THE ELEGANT AND MAGNIFICENT OTTOMAN EMPIRE IN DETAILS

Ya kasance masarauta ɗaya tilo tamkar da dubu a tarihi,..
A lokacin mulkin Suleiman maji ƙarfi da mulki,wuraren ƙarni ta sha shida(16th century)da ƙarni ta sha bakwai(17th century),masarautar ottoman ta kasance masarauta ce da ta gudanar da mulkin ta haɗe da haɗakar wasu ƙasaahen wato (multinational)sannan sakamakon haɗakar ƙasashen,sai mulkin ya kasance mulki ne da akwai yarurruka kala daban daban dan yaren baya ƙirguwa wato(multilingual)wanda yawa yawan fannin da masarautar ke mulka da juyawa sun haɗa da Europe ta kudu maso yamma(Southeast Europe),Europe ta tsakiya(Central Europe),Asia ta yamma(Western Asia),wani yanki a gabashin Asia(Part of Eastern Asia),da Caucasus,Afirka ta arewa(North Africa)da kuma Horn of Africa...

A farkon ƙarni ta sha bakwai(17th century)masarautar tana ƙunshe ne da da jerin mataki matakin mulki(Provinces) ɗai ɗai har talatin da biyu(32)sannan yana ɗauke da masu jan ragamar mulkin ko wanne matakin mulki a ko wani garin da ya yanka wannan masarautar ta Ottoman mai ɗauke da matakan mulki talatin da biyu wanda bayan wasu lokuta aka haɗe waɗannan rababbun matakan mulki,wasu suka shiga masarautar Ottoman wasu kuma aka bar su suka zauna zaman kan su suna mulkar kan su ba ƙarƙashin jagorancin masarautar Ottoman ba wanda hakan ya faru a lokacin rabuwar ƙarni ƙarnin da ya rinƙa gudana..

Lokacin mulkin Suleiman(Golden Suleiman)masarautar Ottoman ya kai wani matsayi da mataki da ƙarfin ikon mulkin sa ya zama abin kwatance,a lokacin,wanda ke karagar wannan mulki shine ɗan Selim wato Suleiman,.Suleiman maji ƙarfin mulki yayi mulkin sa ne a shekara ta alif dubu ɗaya da hamsin da ashirin da kuma sittin da shida(1520 66)sai kuma jikan sa Selim II wanda ya gaji sunan kakan shi mahaifin baban sa Suleiman da yayi mulkin sa shima a shekara ta alif dubu ɗaya da hamsin da sittin da shida da kuma saba'in da huɗu(1566 74)..

Suleiman,ya hau kan karagar mulki a matsayin mai kuɗi shahararre a faɗin duniya,yayi mulki ne lokacin yana ganiyar arziƙi da izzar jinin sarauta.
Ƙarfin sa da ikon sa na mai kuɗi a lokacin sarautar sa ya sa ya samar da cigaba a aikin da mahaifin sa Selim ya bari bai ƙarasa ba,wato aikin samowa da kafa gwamnati na gaskiya dan cire wasu wariyar launin fata da BAMBANCIN BAMBANCE BAMBANCE haɗe da rayuwar rashin ƴanci da tsoratarwa,sai dai wannan ƙoƙari na mahaifin Suleiman wato Selim,bai samu faruwa ba kamar yadda ya so saboda an sami rabuwar kai da BAMBANCIN aƙida,dan haka sai masarautar iran ta Safavid ta ɗaɓɓaka wannan ƙudiri ta sarkin Ottoman suka saje suna gudanar da shi haɗe da yarda da haɗakar masarautar Mamluk ta ƙasar Egypt da Syria..

A turƙiya(Turkey),Ottoman (Osmanil)ya samo ma'anar sa ne da asalin sa daga mabiya al'adar Osman a ƙarni ta goma sha huɗu(14th century)wanda daga baya kuma aka cigaba da amfani da sunan a fannin mayaƙa sojojin(Military)dake kan karagar mulki wanda aka zaɓa wato zaɓaɓɓu a nayihar masarautar...

A Europe ta kudanci,sunaye biyu da masarautar Ottoman ke da shi wato (Ottoman Empire)da (Osmanil Empire)ta ƙasar Turkey,ana amfani da su gabaɗaya a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso ba tare da an hantari wanda ya kira sunan ba..sakamakon dalilai da Turkey ke da shi na yin abubuwan da suka kamata da waɗanda ke iya wuce gona da iri sai sunan masarautar ta fi ƙamari a nan ƙasar Turƙiya,..
Ana haka sai aka wayi gari a wani ƙarni inda Osman,I ya mutu inda a lokacin ne kuma ƙasar Ottoman ta ƙara faɗaɗa mulkin ta har ta ɗaukaka ya kai ga har ya fara ɗare fannin Anatolia da Balkans..ganin haka,sai ɗan Osman mai suna Orhan yayi garkuwa haɗe da kanainaye yankin Gabas maso kudancin birnin Anatolia da birnin Bursa a shekara ta alif dubu ɗaya da talatin da ashirin da shida(1326)..

BAMBANCIN ƘASA {Battle to reach} Where stories live. Discover now