" _Innalillahi waʼinna ilaihi rajiʼun....!_ Suleiman ina can daki ina jiranka ka kawomun kaza ashe wayau kamun kazo nan kana cin taka kazar hankali kwance,,tou na rantse da Allah bazan tabʼa yafe muku cin amanata da kukai ba...ʼʼ ta rushe da kukan haushi,,su kuwa ah firgice suka saki juna tare da dagowa suna dubanta don bbu wanda yayi tunanin zata fito falon,gara ita hearthrob tayi tunanin hakan shiyasa take ta turjewa ammh shi sahibul kalbin he never saw it coming at all😆

  cike da kunya ya shafa kansa yace''Hafsah! am so sorry nayi kuskure...ʼʼ

  kallon rainin wayau ta wulla masa tace''Kamar naji ka ambaci kuskure??tou ka sani wannan ba kuskure bane illah son zuciya,,ayau daya kamata ace ina cikin tsantsar farin ciki ammh gashi u guys hav spoilt my wedding night wanda ya kamata ace nabar dadadʼar tarihi akansa,,ammh ga dukkan alamu sun nuna cewa tarihin nawa daren farkon zai rufe ne da kayan takaici wanda aduk sanda na tunashi zai jefani cikin kunci ne,Allah ya isa tsakanina daku kuma sai Allah ya bi mun hakkʼina,,wayyo kishiya bata yi ba wallahi.....ʼʼ ta sake rushewa da kuka tare da kʼarya gwiwowinta zuwa kʼasa,,jikin Jameelah ne ya dauki rawa sosai sai hawaye sharrrr cuz she felt so guilty,,da rawan murya tace"Haf...sah...don girr..man Allah kiii yaaa...femun wallhiii bazan kuumaaa ciin amanarkii ba...ʼʼ

Adaidai lokacin wayar Gidado ta dauki kidʼa,yana dubawa yaga Sagir ne,bayan ya dauka yace masa"Kai mallam yi sauri ka sameni awaje dare yaja....ʼʼ da tou kawai ya amsa masa sannan ya mikʼe yace da Jameelah"Ke wuce part dinki kuma karki sake na dawo na sameki anan...ʼʼ

Ta amsa masa daa tou,ya dubi Hafsa ransa ah matukʼar bʼace yace"Kema haka...ʼʼ

Tsoki taja tace cike da tsiwa"Anki atafin maci amana kawai...ʼʼ murmushi kawai yyi sannan yasa kai ya fice don yasan bbu yadda zaʼayi Hafsah ta taka matsayin Jameelah ah zuciyarsa,,rashin kunyarta kadai ma ya riga yasa tayi fail,bayan fitarshi Jameelah ta koma Jameelarta fuska ayamutse tace"Ke! bari kiji idan kina cin kʼasa tou tabbas ki kiyayi ta shuri don naga kamar da rawar kai kika shigo gidan,ni idan kika takani bazan wani damu ba ammh karki bari kice zaki dauki wannan banzar dabiʼar ta cin mutuncin mijina agaban idona ko agaban wani don asannan ne zaki san ainihin kalata sbd ni hawainiya ce mai canzawa aduk sanda taso,, _*DCP  SULEIMAN ALASSANA GIDADO*_ ba abun rainawarki bane harki tsaya kina tanka masa magana muryarki asaman nashi,,don haka hattara amarya in ba haka ba uwargida zata gyara miki zama....!ʼʼ

   Cike da tsantsar mamaki Hafsah ta mikʼe tsaye tana fadin"Lallai na yadda kishiya da ababen mamaki take,,wato kukan da kike ta sharbʼawa da kuma tsantsar tsoron da kika bayyana mana duk ta munafurci ce ashe,zuwa dakkoni da kikai ma nasan tabbas akwai wani abunda kika kulla ammh sai Allah besa kinci nasara ba,,kai kishiya akwai munafurci wallahi ammh ki......ʼʼ

Jameelah tayi sauri taran numfashinta"Malama abunda kika gani ba munafurci bane illah kishin ilmi irinta wayayyun mata ba irin naki na en kʼauye masu nuna kishin jahilci ba,,ada kin so ne na dunga biye miki don mu hana masa kwanciyar hankali agida?sannan ya koma ya tsaneni?tou wallahi kinyi kʼarya kuma kinyi kadan,,ki sani ke baki isa kija da mace kamata ba matar dʼan sanda....ʼʼ

Wani miyau mai dʼaci Hafsah ta hadʼiya kan tace"Dake ni dʼin kuma ba matar dʼan sandar bʼace sai matar direban gidanku ko?idan kuna ma da direban kenan,waya sani ko daga cikin tsiya aka tsamoki zuwa cikin daula...ʼʼ

Akʼaikaice Jameelah ke kallonta don sosai kalamanta na kʼarshe suka soya ranta,murmushi ta sakar mai ciwo kan tace"wannan kuma ina ganin ba damuwarki bace ammh abunda kawai nakeso ki sani shine ke dʼin ba dʼaya kike dani ba,zaman kishi da matar dʼan sanda is very annoying sbd sheʼs already trained,sumbar da kika kamamu ma muna yi na tabbata you were very shocked and suprised sabida baki tabʼa ganin irinsa ba,kadan kenan kiga gani kuma idan kikai sakaci zan dauke hankalin mijin ya dawo kaina ke kuma ki rasa gane kanshi gabaki dʼaya,don haka kibi asannu....!ʼʼ

KISHIN MATAWhere stories live. Discover now