Kallonta yay akaikaice yace''wato nine ma dan iskan ko?'' ya furta yana kokarin kwanto belt,da sauri ta jaah da baya tace''A'ah wlh ba kai bane niche...!'' ta fada hawaye na ziraro mata,,murmushin mugunta yyi sannan yace''Good gal....kuma daga yau sunanki yar iska,koki bari na dunga kiranki da hakan ko kuma a'ah bakiso gwara inje in fasa kwan ince musu na ganku kuna shek'e aya ah lungu ta bayan sashin Baba Haruna,,tou wanne aciki kika za6a?…!'' runtse ido tayi tana jin zuciyarta na azalzala da muguwar tsanarsa,shiru ta masa taki bashi amsa,hakan yasa murmushin mugunta sub'uce mishi yace''okay fine i will assume u choose option one and daz very good of you,,tou yar iska bani hanya in wuce…!''

     ******
Kwaryar Hajju ta karba tare da bismillah sannan ta kwararawa Hafsa tun daga kai har kasanta,ko'ina ya dauki gud'a ita kuwa fashewa da kuka tayi don dole kaji wani irin imani da tausayin kanka ya ratsa zuciyarka ah sa'ilin da ake maka wannan wanka,Hajju ta rage kadan aciki ta mika mata tace''karbi ki shanye wannan…!'' hannu na rawa ta karba ta kafa abaki ta shanye tass! sannan ta mayar mata da kwaryar,Hajju ta karba ta daga empty kwaryar sama sannan ta kifar dashi,,ji kke taratasss!ya fashe sai aka shiga rangad'a gud'a akan nada,fashewar wannan kwaryar ba karamin firgitar da Baddo tayi ba don ah tsorace ta shige jikin Gidado tare da fasa ihu jikinta na rawa,adaidai lokacin kuma Hanifa ta tunkaro dakin take fadin''Baddo kina ina ke meh son ganin al'adar wankan ruwan kwarya gashi dai an sake sha dake ku....!'' maganarta ta yanke ah sa'ilin da kallonta ya sauka akansu Baddo rungume dashi,sannan kuma ga belt din dayaso kwancewa ada ya daketa dashi ammh sai be karashe kwancewar ba ya barshi,hakan ne yataimaka wajen raya mummunar zato acikin zuciyar Hanifa,cikin rawar murya tace''Ham...maaaa ashe da...damaa kai din dan...dan iska ne ban sani ba?habba Bad..doo hadda kema kin biye masa ya 6ata miki rayuwa abanza?''

Dasauri ta juya zata koma,hakan yasa yayi hanzarin tura Baddo ta fadi kasa sannan ya finciko Hanifa,tana juyowa ya sauke mata mari yana huci yace''Ke don ubanki nine zaki kalla ki kira da dan iska don bakki da kunya?abunda kika gani is unintentionally don haka idan kika sake naji wannan zancen awaje tou wlhy saina saki kinyi zama ah prison harna tsawon shekaru biyar......'' atsorace ta dafe kirji tace''Na shiga uku ni Hanifa ah prison dai??''

Dariya ne yaso kufce masa ganin tsoron dake shimfid'e akan fuskarta,yace''Yes! you heard me right prison nace sannan kuma bayan kin fito i will cut ur head off,so be warned idan kinason ganin kanki araye,,now get the hell out of my sight....'' da sauri tace''Insha Allahu bbu wanda ma zaiji zan kiyaye Hamma...'' ta juya tabar wajen da sauri sauri har tana harde kafafu,ya dubi Baddo dake durkushe tana kuka yaji wani irin muguwar tsanarta ta sake samun matsugunni acikin zuciyarsa,yace cike da tsanarta''An saba da iskanci shiyasa aka rungumeni don jan raayina,tou bari kiji ni din ba irinsu bane sannan kuma ke baki da abunda zai iya jan hankalina zuwa gareki,,bbu abunda zaki nunawa matayena sai ma su su nuna miki daga Jameelata har hafsata,so i beg u karki sake hada jikinki da nawa koda wasa ne if not sai kin yabawa aya zakinta,,foolish gal kawai yar iska.....!'' ya ida maganarsa tare da jan wni irin dogon tsaki,komawa gaban dressing mirror din Hajju yayi ya dauki turarenta mai kamshi ya feffeshe jikinsa dashi sannan ya fita ya barta zaune tana cizgar kuka kamar ranta zai fita,dakyar ta iya dagawa ta ninke kayan sannan ta zuba mata ah wadrope ta fita waje tama tarar an gama komi sai ma shirin kai Hafsa mota ake don ayau dinnan zaa sadata da dakinta,,kuma Tsoho ya bukaci da kar kowa ya bita,yace Gidado ya kwashi matayen nasa su wuce abunsu,don haka yan'uwanta sukayi sallama suka wuce gida bayan sunga tafiyarsu Gidadon,ammh kafin su wuce saida kawayen amarya suka kasa suka kuma tsare wai fa alallai sai an sallamesu,Gidado beda lokacinsu don haka sai yabar su sagir wai suji dasu,,

Hafsa ce abaya ayayin da Jameelah ke zaune ah gidan gaba,straight Asokoro road ya nufa inda anan ne gidan nasu yake,Gida ne wanda ya amsa sunansa da gda,no long story kunsan dai mutum kamarshi mai matsayi babba awajen aiki ya dace ya mallaki gida na kece raini,Jameelah ce dai ta sake ruko hannun Hafsa suka shiga ciki,sashi daya ne ammh mai girman gaske wanda kowacce tana da part dinta ammh kofofin kowani part nata cikin makeken falon gidan ne,duk inda ka taka sai kafarka ta nutse,ko'ina clean ga wani daddadar kamshin daya gauraye guri,wannan duk aikin Jameelah ce iyayen tsafta,tanan kuwa Gidado yake tsananin alfahari da ita da kuma biyayyarta agareshi,kai tsaye part dinta Jameelah ta kaita sannan ta komo nata don watsa ruwa,

  Ah gefen gado yasamu Hafsa zaune harta kwabe mayafi ta ajje,azuciyarsa yace''Allah sarki Jameelata aranar da aka kawomun ita dakyar na iya yaye mayafinta ammh wannan ko jira na roka bata bari nayi ba she allow me to see the face free of charge,agaskia Jami tayi ne....!''

Tsokanarta ya shiga yi yace''Amarsuu ke ko dan jan'aji irin dai taku ta amare bbu?''

''Meh ka gani?''

Takaici ne duk yabi cikashi ganin ita bata masan abunda tayin ba,kamar bazai sake magana ba can kuma yace''Gani nayi baki jira na roki ah bud'emun fuskar ba kamar yadda dai naga akeyi,sai ganinshi nayi free of charge,yanzu fisabilillah idan daace da abokaina na shigo fa ai da kin kunyatani ba kadan ba don zuwa zasuyi sutayi dani wai matata ba kunya ba class.....!''

Ah zuciye tace''Suce din mana ina ruwana badai an kawoni gidan masoyina ba?sannan kuma kai din yau ne na soma ganinka da har zanji kunyarka?'' mmki ne ya kusan kasheshi tsaye anan da yadda ta karba masa magana,lallai kam zaiyi fama da ita don ya lura sosai zatayi rashin kunya abunda Jameelah bata masa kenan,tana mugun gudun 6acin ransa.....

Kala bece mata ba,har zai fice daga dakin sai ga kiran sagir na shigowa,yana dagawa Sagir yace''Kai dan iska da fatar dai ka tsaya ka siyawa amarya kaza akan hanya don nasanka akwai shegen mantuwa.....!''

Dafe goshi yayi yace''Goddd!! wlh Sagir na manta kuma gashi yanzu to eleven,,ammh bari inje Allah yasa suna nan....'' 

''Suna nan mana har 12 suna kaiwa,and please idan zaka siya ka siyawa uwargida don azauna lfy haka ake yi...''

Murmushi yay yace''Ai Jameelah bata da matsala....''

Sagir yace''Kai dai ka siya mata banson gaddama,infact jirani gani nan zuwa dashi....'' kan ya sake magana ya kashe wayar,murmushi yayi yace Allah sarki Sagiru abokin kwarai....

''Gidado wato niche ma mai matsalar ko?'' haka yaji Hafsa ta furta ah kufule,,da mmki ya waigo yana kallonta yace''Kinji na fadi hakan ne?''

Saida ta saki dan siririn tsoki kan tace''Ai cewa kayi wancan matar taka batta da matsala which means badin ina kusa ba kaso kace masa niche mai matsalar ko?''

Hmm lallai ina da aiki sosai agabana abunda ya iya ayyanawa aransa kenan,be bata amsa ba yace''Nidai kije ki watsa ruwa kafin kazar amaranku ta iso don nasan shima din gab kike da tsareni da tambayoyi akansa tunda na lura ke din kunya be isheki ba…!''

Dirowa tayi daga kan gadon tace''Lallai ma Suleiman niche din bani da kunya?...'' wani irin shewa tayi gami da tafa hannaye tace''Lallai ko ni Hafsa zan gwada maka rashin kunya irin tawa acikin gidan nan,,kai dai zuba idanu kasha kallo,,kuma wni wanka ne zanyi bayan wacce aka mun da sunan wani al'adar banza?duk anbi an jika mutum da ruwa mtswwww...''

Har ya daga hannu zai kifa mata mari,ko mai ya tuna kuma sai gani nayi ya dakata tare da dunkule hannun,zuciyarsa na azalzala,,tsantsar mmki ne ya cikata ta kama kugu tana fadin''Eyyy meh nake gani haka Suleiman?marina kke shirin yi?lallai da baka kuma ba don kana marina tou wlh matarka zata jishi ah jikinta itama...!''

Idanunsa sunyi jajur dasu tamk'ar jan gauta,yama kasa furta komi dkyar yace''Fine Hafsah nagode...!'' ya juya yabar dakin ransa ah jagule,ah makeken falon ya hango Jameelah zaune cikin night gown dinta tana rusar kuka don tana ta juyo hanyaniyar Hafsah,muryarta asaman na mijinta,,jikinsa ne yay sanyi qalau ya nufi inda take....................!!

  _*yanzu wasar zaya soma armashi😎sai ku biyoni*_

_Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *KISHIN MATA* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0824409678 Hafsat mustapha Access bank,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *07065481260* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *07065481260* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

*Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu MALIKA-MALIK na Janafty,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*...

07065481260..Ko kuma 09069067488

_*#HAFNANCY_LURF💓*_
_*#KISHIN_MATA*_
_*#2020_NOVEL*_
_*#SALO_NA_DABAN*_
_*IWA🖊*_

KISHIN MATAWhere stories live. Discover now