Jameelah dai bata tankasu ba sai kuka take mai ta6a rai,manyan na zuwa suka nemi jin ba'asi,anan ne ake musu bayanin cewa ai uwargidan Gidadon ne ita Jameelar,sosai sukayi mmkin yadda akazo daukar amarya da kishiyarta ahad'e ammh basu ce komi ba illa fada suka shiga yiwa 'ya'yan nasu akan don meyasa zasu taresu da fad'a? Ruqayyah sai cewa take tayi ta mareta fa ammh bbu wanda ya kulata sai cewa akayi ma karya takeyi itace ta mari Jameelar,suna ji kuma suna gani akayi ciki dasu Azeemar,Jameelah sai gwalo take ta aika musu dashi ah 6oye...

    ____________★★

Gidado ne yaje can ta bayan gida yana waya dasu Sagir donshi mmki yake yadda sukace masa wai Jameelah tasan gidansu Hafsah bayan bai ta6a kaita wajenta ba balle kwatance,lallai mata kenan yasan tabbas bincike tayi akan Hafsah,shidai addu'arsa dai aynzu shine Allah yasa karta bashi kunya,bayan yakare wayar da Sagir har zai koma can cikin gida sai yaji kamar ana magana kasa kasa ata wani lungu,ahankali yaja jiki ya lafe ajikin bango tare da kasa kunne yana sauraro,muryar Kasim d'an Baba Munniru ne ya daki dodon kunnuwansa,

    '' Don Allah ki yarda da kalaman da suke fitowa daga bakina,soyayyarki ce ke 6oye acikin zuciyata wadda ta zamo sirri tsakanin zuciyata da kirjina,hakika nayi tattalin wannan sirrin da cewa bbu wanda zan fadawa shi sai ke kadai da kika fi cancanta ah zuciyar yan mata,tabbas na zaga zuri'ar nan,ga yan mata nan da yawa acikinta ammh ko kadan banga wacce tamun ba kamarki *MUBEENAH* ,kuma na zabi fallasa sirrin zuciyata ne aduk randa Allah ya kawoki garin Abuja sai gashi ya fad'a ah bikin Hamma Gidado,plsss enmata kice wani abu man don Allah ki amince mu zamo mutane na farko da zasuyi auren dangi acikin zuri'ar nan kinji plsssss na hadaki da Allah Mubeenata ina sonki kuma ina qaunarki....''

Jikinta ne ya dauki rawa sosai,zufa ya shiga tsastsafo mata kota ina don sosai kalamansa suke neman rud'ata,da rawar murya tace''Ham..ma  ka...sim don girman Allah karka ce dani haka,,yabba (haka suke kiran babanninsu) zai mun fad'a sosai don ya hanani tsayawa da samari saina gama aji shidda wai,kuma zanso ka cire soyayyata aranka tun kafin wani yaji ma don kasan ba'a ta6a auren dangi ba ah zuri'armu tou baka ganin watakila asamu matsala idan zancen nan yyi kuskuren fita har akaji? Hamma Ka.....!''

  ''Mubeenah ki gane man! wlh Kasim ya kamu da mugun sonki kuma gaskiya wlh bazan iya hakura dake ba,insha Allahu akanmu za'a fara auran dangi acikin zuri'ar nan,kawai yanzu so nake ki tabbatar mun da amincewrki kar kiji tsoro nida kaina zanje na samu tsoho da maganar kinji?

Ajiyar zuciya ta sauke don idan tace itama din be kwanta mata arai ba tofa tawa Allahnta karya,tace''Tou shikenan naji ammh nidai muyi abunmu asirrance tukunnah zuwa nan gaba idan na kare makarantar saika fito da maganar ammh aynzu gaskia ban bada goyon baya ba....!''

Murmushi ya saki yana kura mata ido cike da zallar shaawarta,yace''Tou gimbiya yadda kikace hakan zaayi nidai amincewarki din dama kawai nake da bukata,tunda kuma kin amince ai komi mai sauki ne,yanzu dai bani lambobin wayarki wanda zamu dunga communicating ta hanyarshi idan kin koma....!''

Wani kasaitaccen dariya Baddo ta saki mai kayatarwa kan tace''Ai yabba ya hanamun rike waya wai saina gama school tukunnah,kaji fa shekaruna goma sha bakwai ammh sai cewa yake wai har yanzu ban mallaki hankalin kaina ba saina kai sha takwas tukun…'' ta ida maganar tare da cuno baki gaba,shi ko sake bin zubin halittarta yyi,komi yaji sai kace ba er sha bakwan ba,girgiza kai yay kan yace''Gaskia kam yabbanmu bai kyauta mana ba,ya zaayi ace zankaded'iyar budurwa kamarki ace bata da waya?yanzu miye abun yi?''

''Abunyi shine ka fita daga harkarta kafin watan soma cin ubanka ya matso kusa kana jina ko?'' ah firgice duk suka juyo kallonsu ya sauka akan Gidado dake tunkaro lungun fuskarsa ahad'e tamk'ar be ta6a sanin dariya ba,gaban Kasim ya shiga dukan chalugud'e,ba shiri ya jingina da bango yana fadin''Hamma Gi.......''

''Hammar kutumar ubanka?yarinya kankanuwa kamar Baddo ce ka jawo zuwa lungu kke kokarin 6atata?eyyy tambayarka nake…!'' ya fad'a cikin tsananin fusata,Kasim yace cikin tsorata''Hamma wlh ba 6atata nakesonyi ba kawai ce mata nayi inasonta da aure…!

Takaici duk yabi ya cika Gidado yace''Sonta?meh yarinya karama kamarta ta sani agame da so?in da gsk kake ma tou meyasa baka gaya mata ah filin duniya ba sai janta lungu kayi wato salon ka yaudareta da soyayyar karyarka ka 6ata mata rayuwa ko?ai duk ina la6e ina jinku kuma na rantse da Allah idan ka sake bari na ganka da ita ah ke6antaccen wuri kaji nace Allah sai kayi kwanan cell bayan na gama farfasa maka jiki da rodi...!""

Gidado yashiga karkad'a yatsun hannunsa biyu yana fadi cike da zafi''Oya tun daga wajen tsugunna ka soma tsallen kwad'o don idan ka bari na matso kusa abun bazai maka k'yau,,maza nace...'' ya ida maganarsa tare da zaro belt din wandonsa yana huci tamk'ar namijin zaki,da sauri Kasim ya tsugunna tare da kama kunnuwa biyu ya shiga tsallen kwadon kuma ta gabanshi zai bi hakan yasa duk ya kara tsorata,ita kuwa Baddo da baya baya ta soma ja tana zubar da ruwan hawaye tare da shessheka,zuciyarta fal tsoro,kallonta Gidado yay yace''Idan kika sake na sake jin shesshekarki Allah saina matso na miki duka black and blue,oya maza kama bakinki....!'' da sauri tasa hannu ta kama le6unanta ammh hawaye be bar zubowa ba,Gidado ba sauki ai saida ya shaud'a masa belt din sau biyu yana fadin''Dan iska mai 6ata yara kawai...'' shi kuwa Kasim aguje yyi cikin gida,kuka ya kufcewa Baddo ganin yana kusanto inda take,ta manne da bango ssai tana fadin''Hamma Gidado wlh shine y

       

KISHIN MATAWhere stories live. Discover now