Story written by Ashaanty love
Bismillahir rahmanir rahim
Garin yayi tsit, kowa na gidanshi qulle saboda ruwan saman da ake sheqawa kamar dabakin qwarya.
Ga iskan da akeyi mai kafin gaske, garin yayi duhu kamar magrib dukda lokacin karfe biyarne na marece, kowa na gidanshi qudundune cikin bargo yana sauraren ikon Allah saboda irin ruwan nanne mai tsorata jama'a, ga karfi ga iska.
A can gefen titi nahangi wani Abu takure, ahankali na isa wajen don ganin komenene. Mammaki yakamani ganin mutum ne atakure, saida na matso kusa na gane Ashe macece.
Ta hada kanta da gwiwa ta rugume kaffafunta da hannayenta, bata ko damu da ruwan dake dukan bayantaba, ga iska dake tada gashin kanta.
Tafi mintina goma ahakan sannan ahankali ta dago kanta Wanda in banda digar ruwan babu abunda yakeyi, ahankali ta Daga kan sama tana kallon sararin samaniya batareda ta damu da ruwan dake dukan fuskartaba, lumshe idanunta tayi tana sauraren yadda ruwan ke dukan fuskarta sannan ahankali tadaga hannayenta ta budesu tana tarar ruwan dasu.
Kowanne digon ruwa dake saika jikinta Nada nashi tasirin, jitake kamar ta dawwama ahaka HAR ABADA.
Aduniya komai kashi biyune, komai na duniyarnan Nada kishiyarshi.
Farinciki-bakinciki
Haske-duhu
Nasara-faduwa
Farinjini- baqinjini
Fari-baqi
Masoyi-maqiyi
Aduk wannan abun da aka lissafa kowanne dafarko yake so wato farinciki, haske, nasara, farinjini, fari da masoyi.
Babu maison kishiyarsu saidai Wanda Allah ya jarabta da hakan Wanda babu daman sauyawa.
Akwai mutanenda basusan baqincikiba ko damuwa, wadanda Allah ya azurtasu da samun komai na farinciki, akwai kuma akasin haka wadanda basusan komai ba sai baqinciki da 6acin rai.
Haka Allah ke ikonshi shi yayomu kuma ya tsara yadda rayuwarmu zata kasance kuma bamuda tace wa akanshi.
Ahankali ta bude lumsassun idanunta da lashes dinsu yajiqe da ruwa tana kallon sararin samaniya, wani digon ruwa ta digomata cikin ido tayi saurin lumshewa Wanda hakan yaba ruwan dakuma maqallalen hawayenta gangarowa.
Rayuwa kenan, kowa akwai yanayinda take zomashi, ita haka tata rayuwar take, Daga wannan baqincikin zuwa wani baqinciki, haka kaddararta take, bazata ta6a samun farincikiba koda daidai da rana dayane? Tambayar datayima kanta kenan yayinda hawaye suka cigaba da gangarowa saman kumatunta.
Ahankali rayuwarta tashiga dawomata tunda ga farko kamar ana rewining din video, komai yashiga dawomata farko kamar ana budemata shafi shafin rayuwarta a littafi.
TUSHEN LABARIN
YOU ARE READING
HAR ABADA!!
Romancesoyyaya Nada dadi, soyyaya Nada daci, soyyaya cutace, soyyaya rahamace, kowa da fahimtar dayaima SOYYAYA, it depend on yanda tazo maka, amma Abu mafi ciwo shine kaso Wanda baimasan da wanzuwarkaba. wannan labarine akan soyyayar 6ari daya, wato son m...
