DA IYAYENA. kashi na daya

877 61 19
                                    

*DA IYAYENA*

_Daga Alƙalamin_
*© Rahma Kabir (MrsMG)*

Wattpad @rahmakabir

GARGADI
      _Ban yarda a juya min labari ba ko a sauya min shi zuwa film ko satar fasahar wani bangare a yi littafinsa, duk wanda na kama da haka zai fuskanci kalubale mai tarin yawa, a kiyaye._

*GAJEREN LABARI*

1 ~ karSshe

Tsaye nake ina kallon saman rufin ɗakinmu, na shiga tunanin yadda muka kwana cikin saukar ruwan sama, kasantuwar muna cikin yanayi na marka-marka, har zuwa gabanin sallar asubahi kafin ya tsagaita. Ruwan da ya ƙare akanmu, ɗakin da muke ciki kwanon ya buɓɓule ruwa ko'ina yake zuba ya jiƙa duka shinfiɗarmu, a tsugune muka kwana wasu kuma a tsaye, a haka muka kasance har garin Allah ya waye ya yi tangaras, sanyi ya gama ratsa duk illahirin sassan jikinmu, in da sabo mun riga mun saba da wannan rayuwa mai cike da ruɗani, haka muka fito daga cikin ɗakin tsamo-tsamo kowa ya kama gabansa babu wanda ya yi yunƙurin yin sallar asubahi ko neman sanya tufafi.

Zama na yi akan dakalin dake gefen ɗakinmu, na yi tagumi hannu bibbiyu, tun ina ɗan shekara bakwai ban san ya duniya take ba ban san ina na dosa ba amma da garin Allah ya waye abu biyu nake fara tunani.

'Shin ta wace hanya zan samu abin karin kumallo?'

Har kawo iyanzu da shekaruna ya kai sha biyar tunanina kenan, sai kuma tunanin Iyayena da kullum yake cika min zuciya.

"Shin anya iyayena suna kaunata kuwa?"

Tambayar da ba ni da amsarta, wasu siraran hawaye ne suka sauka a kuncina, na sanya hannu na goge, sai na kuma tambayar zuciyata.

'Shin ta wace hanya zan samu kuɗin da zan ciyar da kaina?'

Domin a irin wannan lokaci ba lallai na samu abincin kalaci a gidajen mutane ba, musamman da unguwar ta kasance na talakawa suma rayuwar suke hannu baka-hannu kwarya. Ɓangaren unguwannin masu hannu da shuni kuwa, a irin wannan lokaci ba kasafai suke ta shi barci da wuri ba, musamman yau da ta kasance ranar hutun ƙarshen mako.

"Ni Ashiru yaushe zan zama cikakken ɗa mai ƴanci kamar yadda sauran ƴaƴa suke zaune a gaban Iyayensu cikin gata?"

Na tambayi kaina a fili, *DA IYAYENA*, na zama tamkar maraya wulaƙantacce a idon duniya, banda sauran gata, ni ke kula da tarbiyyata da abincina, ina nan ina gararamba a wata duniyar da babu dangin iya ba na Baba, domin biɗar abin da zan sanyawa bakin salatina, sabulun wanki da sutura, babu mai kula da lafiyata, na ci ko na sha babu mai tambayata, kuma Iyayena suna raye, suna can wata duniya ina nan ina garari a wata nahiya mai cike da rudani.

"Ko ta yaya zan mayar da hankalina na yi karatu cikina babu yaɓa, yaushe Iyayena zasu waiwayeni susan halin da nake ciki?"

Na tambayi kaina a fili babu amsa. Shi kansa Malam Tanimu in mun samu abun amfani amshewa yake yi, mun yi masa yawa babu yadda zai iya kulawa da tarbiyyar mu, kuma kullun rana sai an kawo sabbin yara ƙanana don yin karatun Allo, ba kuma ya fasa karɓansu. Iyayenmu sun kawomu Almajiranci sun yasar wa duniya ta raine mu, basa waiwayenmu balle susan halin da muke ciki.

Na sauke gauron numfashi, na miƙe tsaye domin zama bai ganni ba da hutun jaki da kaya a kai, na wuce dan samawa kaina mafita kafin cikina ya soma ƙugin yunwa, sannan ƙarfe goma na safe muna da darasu, in ban dawo kan lokaci ba, na ci baƙin duka wurin manyan Almajirai masu kula da mu.

Tafiya nake ban san ina na dosa ba, kusan hankalina baya jikina, a haka har na isa wata unguwa ta ƙun-ƙun Talakawa, na hangi yara a bakin wani kwazazzabon rafi, da sauri na isa gurin na taras da wasu yaran suna ciki suna tsamar yashi, wani guntun murmushi na saki dan tsantsar murnar samun mafita da na yi a nan take, sai na cire rigar jikina na aje akan wani dakalin wani gida dake gefen rafin, na naɗe ƙafar wandona naje na shiga cikin rafin na soma tsintar kayan tsaɓi, danginsu gwangwani, ƙarfe da sauran kayayyaki da ake samu a cikin kwatami ko rafi na tsaɓi. Lokuta da dama wayon da nake yi kenan a cikin unguwanni, dan samun tsaɓi na siyar na samu kuɗin siyan abinci, sabulu da ƴan ƙananun abubuwa da zan iya siyawa kaina.

DA IYAYENAWhere stories live. Discover now