Episode~2

336 99 0
                                    

*_💐💐WAHALA DA GATA💐💐_*
_{Novel series}_
*_[♠️SEASON.2 ♠️]_*

*WATTPAD @Smart_Feenert ...✔️*
*_[🥀Be ~ Smart 🥀]_*

*_🍂BISMILLAHI RAHMANI RAHIM🍂_*
—•—•—•<>•<>•<>•<>•—•—•—

*_DEDICATE THIS PAGE 2U HUSAINI 80k_*

_Episode 2_

Yana fitowa daga wajenta Ya nufato bangaren Hajiya Kaka..

A zaune a wajen da take tin dazu ya sameta.

cikin wani mugun tashin hankalin ganin yanayin da take ciki ya k'araso gurinta, ya ce "Hajiya lafiya? meke damunki ne? ba kya jin dadin jikin ki ne? dan Allah Hajiya taso mu shiga ciki." Duka a rikice yake jero mata dik wadannan tambayoyin.

Da wata makirar harara ta bishi da kallo tare da tsuke k'aton bakinta takin, taja wani mahassadin tsaki wanda sai da ya yi sanadiyyar fad'uwar wani kofin silver dake kusa da ita Lol, hadi da bud'e kwadon sharan bakinta cikin mugun bala'i, ta ce

"Ina ruwanka halan bak'in munafuki? ai ni wallahi tsakanina da kai sai dai kallo, ko shi kuma bai zama dole'ba, idan naga dama sai na maida fuskata k'asa in kalli k'asa dan yanzu ta fika muhimmanci a wajena."

Cikin damuwa ya ce "Subhanilillah! Hajiya wani abin ne ya faru? dan Allah ki sanar da ni ko ma mene ne wallahi zan dauki mataki akai."

"wai bak'in munafurci! wato ni zaka maida sakarya ko? dan ubanka!, to tin kafin ka tafo duniya na san da wannan munafurcin, dan haka ka b'ace man da gani bana son na sake ganinka a gurina, ka je can ka ci gaba da zama da waccen mayyar da ka zab'a a matsayin mahaifiyarka, kaci gaba da kai mata kaji da namomi ta na sawa a baki tana ci har lokacin da ya fito mata a jiki! marar zuciya kawai."

Cike da wani mugun tashin hankali da bidar k'arin haske, Uncle Muhammad ya ce

"Innalillahi wa'inna Ilaihim raju'un! Me kike nufi Hajiya? ni fa har yanzu ban fahimta ba."

Cikin masifa ta ce "Au! ai dole ka ce ba ka fahimce ni ba, tinda an riga da angama da kai wajen malamai, an baka kasha kuma an saka maka ka ci! ai ni tsakanina da Saudatu wlhy sai dai Allah ya'is...." da sauri ya dakatar da ita da ce wa "Dan Allah Hajiya karki ida, wallahi summa tallahi Umma bata taba jifanki da wani mugun abu makamance wanda kike zato ba! haba Hajiya me ya sa ko da yaushe tunaninki yake baki hakan ne? Hajiya kufa yanzu kunyi girman da kun wuce a kiraku da yara, ya kamata ace dik wani kishin da kuke yi da junanku ku daina domin Rayuwa bata da tabbas Hajiya dan Allah ku samu lokaci ku zauna ku sasanta junanku mu kanmu zamu fi jin dadin hakan! dan darajar Alqur'ani Hajiya ki ajiye komai da kike ji a cikin zuciyarki, gefe, ki kama gaba ki manta da baya."

"Hmm! To sannu da kokari fa Shehi! ai wannan ya zama dole ne a gareni
tinda kai ka halicce ni kuma kai ka busaman rayuwa tinda da ikonka nake numfashi a halin yanzu."

"Innalillahi wa'inna ilaihim raju'un! Hajiya Ina mai qara baki haquri dan Allah a bar wannan magan..." bai ida zancen ba, ta katsashi da ce wa

"Billahillazi Idan baka rufe man bakinka ba sai na mazgeka a wajen nan! shege marar Imani, ko kana tantama akan ba zan iya dukanka bane tinda yanzu tunanin ka ke girma ya fara rufeka dan ka ajiye iyali harda wani munafukin gemu da qasumba da ka tara wadda ta k'ara maida kamarka sak da ta gwaggon Biri, wlhy sai dai ka nuna mata hasken fata ko shi kuma nawa ne dan dik hasken Ubanka bai kai nawa ba! to da kazat uba na sake jin wata kalma makamancin haquri ta sake fitowa daga bakinka, wlhy sai na tsige maka Albasa mai shegen kai kamar an daka doya a turmi.!"

A rauna ne ya ce "To shikenan Hajiya Allah ya baki hak'uri.!"

"Ameen dan ubanka."

A fusace ya ida k'arasawa d'aki ya ajiye masu kayan da ya zo masu dasu, sannan ya yi sallama da Ita,  ya yi ficewarshi daga nan ya nufi part din Hajiya khadija_

WAHALA DA GATA season2 Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon