"Du'a kizo an kiraki ta landline"Bata k'ara second ba ta fice.

Tashi tayi duk jikin ta amace ta fito parlour,sudai mu Mama sunji tace Ina zuwa.



Maman Yara ce ta gaza yin hak'uri tace
"Nikam gaskiya zanyi ma magana idan ke bazaki yi ba,mu mukayi mata laifi Kinga kuwa dole ne mu Kira ta mu rarrasheta,Kinga fa ko abincin Rana Bata ci ba,gashi har biyar na Neman yi"Mama tace


"Ai kinji wallah Maman Yara duk ke kike Bata d'aurin gindi take abinda take so,yoh Ina ruwana nikuwa data ci da kar taci duk d'aya ce iya ka idan ciwo ya sameta ita zata ji ajikin ta ba wani ba,don Allah ki rabu da ita,don kanta zakiga ta nutsu da dawo hayyacin ta,inba hakan yayi mata ai bazata daina abinda take ba,kina kallo dai da Yaya aka samu ta daina saka English ware a gidan nan,da wahala,yanzu kuma yawo babu d'ankwali,nifa kinsan Allah Maman Yara na fara tunanin ko,jinnu gareta saboda abin yayi yawa"ta k'arashe maganar cike da damuwa.




"Aaaa karki Soma had'amin yarinya da wanann zance ina,Allah ma ya kiyaye ya Kare,Ina karki sake fad'in haka gaskiya".Maman Yara ta k'arashe tamkar zata rufe Mama da duka.



"Tohm shikinan naji Allah yayi Mana jagora"Maman Yara ta amsa da Amin.



Tana fitowa Maman Yara ta tareta tace"Ina zuwa maka ne nikam yarinyar kirki?"..a dak'ile ciki ciki a lallai ita an b'ata mata Rai tace"Muhseen ne yazo yace Yana waje shine zan sameshi".
Sai wani cin magani take,ita kam tuni Mama ranta ya b'aci ta tashi tabar wurin ganin yadda take wani lallab'ata ita kuma sai wani basar wa take.


"Ayya kuma haka zaki fita baki ci komi ba?"Maman Yara ta fad'a tana dafa kafad'unta.




"Eh Mama bana jin yunwa shisa,sai na dawo"binta tayi da ido.
Cikin zuciyarta tace,ohh Allah ka shirya Mana,magana dai yanzu ma kan nata babu d'ankwali iya mayafi ne Shima kuma sharashara ne.



PLS SHARE AND COMMENT👌🏽

*UMMU NABIL*
[9/2, 18:31] Lovly tah 1: *KISHIYA*









®☄
*GASKIYA WRITER'S ASSOCIATION✍.*
_{Gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta sai barinta,burinmu mu faɗakar da al'umma domin ribantar duniya da kuma lahira.}_


*NA*




*UMMU NABIL*




*_DEDICATED TO,ABORIGINAL WRITER'S ASSOCIATION,I LOVE U ALL_*






*NO.2*



Nikam duk wanan buduri da suke yi ina can ina bacci kasancewar mun samu hutun Babbar Sallah da akayi,sai satin gaba zamu koma,shisa sai na ci bacci na mai isata tukun nake tasowa,na dafa abinda nake so,sai da nayi wanka na shirya tsaf sanan na fito bayan da ma shi Baban mu kafin na tashi sun tafi aiki shida su Yaya Abbakar, mun gaisa da Maman Yara,na gaida Mamana naga ta amsa ni ciki-ciki,ban damu ba saboda nasan Ina da wata Maman,kitchen na wuce na soya k'wai na had'a tea na dawo parlour na tadda Mamana ta bata parlour sai Maman Yara,kusa da ita naje kusa da ita na zauna ina karya wa,ta dafa kaina gami da cewa


"Du'a"na d'ago kyawawan idanuna na kalleta nace

"Na'am Mama"Ina kaiwa tea bakina.Tace

"Kinsan abinda nake so dake kam?"Ta fad'a tare da kallon cikin idanu na.

Girgira mata kai nayi alamun A'a,gani tayi kamar bana fuskantar abinda take fad'a min yasata cire min abin sauraron kid'a daga kunne na tace

"Du'a baki jin magana wallah,magana d'aya kullum nace maki bani son jin wak'e-wak'en banzan nan ama ke baki ji,ace ke kullum bazaki ji karatun Allah da Annabi ba sai wanan aikin shaid'an ko,toh wallah ki kiyayeni inba haka ba ranki ne zai b'aci kinji na fad'a maki"ta kama kunnen ta alamun gargad'i.

KISHIYA                                         {COMPLETED10/2019.}Where stories live. Discover now