"Meenal yaya jikinki ina fatan kin tashi lapiya" Mik'ewabtae daga kwanciyar ta zame k'asa

"Barka da kwana Takawa ina fatan ka tashi lafiya" kallonta yakeyi yana tunawa da Salman sa, itace duk safiya idan zata gayar dashi seta duk'a kuma takawa take kiranshi dashi, da k'yar ya iya furta

"Lapia lau, kindaiji sauk'i ko"
Murmushi tayi

"Abu haidar sauk'i kam se a wurin Allah, kuma naji sauk'i sosai, nagode da d'awainiya Allah ya saka da alkhairi ya k'ara d'aukaka yakuma janye idan mak'iya, Allah ya bada ladar jinya" yarinyar nan tana matuk'ar gigita rayuwar sa wani zubin, maganarta ita da salma iri d'aya, itace take yawan masa irin wannan adu'ar aduk sanda yamata wani abin Alkhairi ya sameta ta sanadinsa wani zubin ma haka kurin seta hau masa, da k'yar ya iya furta

"Ameen" a tak'aice

"Gobe zamu koma, komai namu ya kammala, seki sanya kuyangi su harhad'a miki kayanki, ki shirya muje zaga gari" Bazata iya yi masa musuba, d'awainiyar da yae da ita ya sanyashi k'ara k'ima a idanta.

  Tunda duka fita bece da ita ci kanki ba, keke napep suka hau kurun ya saukesu inda zasu, ita mamaki yake bata yanda ya rufe idanshi yake jibgar kaya sekace besan darajar kud'in saba, iyakarshi ya d'akko abu yad'an kara ajikinta yae murmushi seya jibga a kwandon da ake saka kaya, su hidar ma da meenal haka ya dinga jibgar musu kayan sawa dana wasa, ita dai ido ne nata, sedabya gaji sannan yaje ya biya kud'i suka bar shop d'in.

Yawon shan iska sun jajje wurare duk a taxi kan daga bisani su juya zuwa gida.... Agajiye suke dansunsha yawo, duk kuma yawon nan dasukeyi bawai hira suke ba, jefi jefi yakan d'an wurgo mata magana, ita kamma jinta takeyi tamkar tana yawo tare da wani complete stranger, batare daya ce komai ba ya mik'a mata towel

"Ki cire kayan jikinki, zan tayaki wanka" waro idanta tae shikuma ya basar lokaci d'aya ya d'auke kanshi

"Abu Hidar aikuma na samu sauk'i, wankan ma zan iyayi ko d'azu da kaina nayi ai" Kallonta ya tsayayi na wasu 'yan dak'ik'u, kan daga bisani ya tako a hankali har inda take, Janyota yae tazo k'irjinsa ya rungumeta ya sanya hannu ya zuge zip na bayan rigarta, d'an rabata yae dajikinsa rigar tae k'asa ya zare hannayen rigar ya k'arasa cire, ta dawo iya under skirt ajikinta da bra se pant, d'aura mata  towel d'in yae yace

"Ki rage yawan kayan ki sako towel, xan tayaki nace" mamakin ikon sa sosai takeyi, yaya ze rik'a mata wanka sekace wata jinjira kumafa taji sauk'i, bataga alamun wasa a fuskar saba bare tayi musu, juyawa tae ta cire kayan, jiki a mace tabi bayanshi a toilet d'in, tasha mamakin ganinsa dagashi se boxer's dan kuwa duk wankan daze mata da kaya ajikinsa yakeyi, tsorata tayi taja baya wanda harya kula da hakan, murmushin dabe wuce iya labb'ansa ya sake yace
"Ki k'araso mana" ja ta k'arayi da baya

"Takawa dan Allah kayi hak'uri" Kallonta yae yaga kanta ma waje yake kallo, ya k'ara sakin murmushi

"Sekace ba zawara ba? Yana ta saba da namiji? Kodai ba k'auye ta aura, dama ta kwantar da hankalinta danshi idan ba Salma ta dawo duniya ba ya gama wannan abin
  " kije idan nagama sekizo kiyi" Da sauri ta juya shikuma ya watsa ruwansa ya fito sanye da Bathrobe yana tsane suman kanshi da k'aramun towel ko kallon ta ma beyiba ya hau sha'anin sa, ita kuma ta shige tae wankanta tana mita akan zaman takawan d'an iska, bashida aiki seso ya kalle mata jiki shiga dan iska, Allah zatazo ta soma dena masa biyayya indai shi d'an iska ne, haka kurin!.

*Nigeria*
   Kai tsaye gidansu ya kaita, shikumabya juya zuwa masarautar su inda tafiyar awanni biyu ce kacal.

  Da Talented ya fara had'uwa kanya wuce

"Menene abinda kika had'a game da wanda sukaje gidana kisan Hidar" Nisawa tayi

"Bincike fa yana nunamun basuda wata alak'a da wata masarauta ma ba tamu ba, sabida babu wani suspicious call ko txt mesaage daya fita tsakanin 'yan masarauta damuke zargi dakuma wasu mutanen, dukkaninsu babu wani abu daya nuna sunada masaniya, har gwarama Amaryarka akwai wani conversation dasukeyi akanta wanda inada record nakomai nayi using hacker na kwashe komai daga ntwrk da both of them suke using, shiri akeyi akan kisan ta, inaga ya dace ta koma zaman masarauta sabida kaga acen suna shakkar suyi wani abu akan idan idan masarauta, kasan masarauta akwaita daji dakuma gani sosai" Nisawa yae

TAFARU TA K'ARE......Anyiwa me dami d'aya sata...जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें