Babi Na Daya

34 3 0
                                    

Yau ranar lahadi ce, wanki Haj Kaltume tasa yaran ta a gaba suyi. Duk da kasance wa yaran nata suna da karancin shekaru, hakan bai sa tayi kasa a gwiwa ba gurin dagewa tsayin daki kan tarbiyya ba. Yadda ranakun su suke farawa kamar haka, litinin zuwa juma'a tana shirya yaran su tafi makarantar boko da safe, da rana misalin karfe uku kuma sai su shirya su tafi islamiyya, in an dawo ayi aikin makaranta. Ranar asabar da lahadi kuma da babu makarantar bokon, sai a shirya ayi yan wasanni zuwa rana, da yamma kuma a fara bibiyar karatukan makaranta. Satin da ya fado na tsifar kitso, da wanke kai, sai a sake wani kitson. Yanayin yadda ake tafar da al'amuran gidan Abba Baba, abin sha'awa. Yaran, Firdausi, Salma, Indo da Rahma, ba fita suke yi ba in dai ba mahaifiyarsu ce ta aike su ba, kuma shima ba jimawa suke yi ba. Haj Kaltume dai bata fiya shige shige ba irin na yan unguwa, sai nace daku ma, in dai ba rashi akai ba ko abin alkhairi ya sami wata a unguwar ba, ba shiga take ba. Hakan yasa wasu suke ganin ta kamar mai girman kai, toh harkar mutane ba'a iya musu.
'Firdausi, ki hada kan yan uwanki, ku goge uniforms dinku, gobe litinin' Haj Kaltume ta fadi.
'Toh, mama. Daman dazun na ga an dauke wuta ne shiya sanya ma ban dauko iron din bama. Amma yanzu zamu yi, mama'
Indo ce ta fara cewa 'Yaya, baza mu bari sai gobe da safiya ba muyi gugar kafin muje makaranta ba?'
'Yanzu mama tace, kuma haka zamu yi'.
Abba Baba ya dawo daga gidan Hajiya Babba, haka suke cewa da ita kasance war ita ce babbar su a gun baban su, Abba Baba bai taso ya girma da baban shi ba, a gun Hajiya Babba ya taso tun yana kankani, haka nan suka dauke ta kamar babarsu shi da Auwal, Jafar da Abubakar, sai kuma shi Abba Baban wanda yaci sunan kakansa Jabir, ake ce dashi Abba Baba.
Yana dawo wa akai kiran magariba, alwala yayi, ya tafi masallacin bayan gidanshi, anan ya bi jam'i har suka idar da magariba. Ya dan fara lazumi, da akai sallar Isha ya sake bin jam'i, da suka idar ya fito, suka kara gaggaisawa da mutanen unguwa wanda sukai sallah tare, ya tafi gida.
Haj Kaltume, farar mace wanda hausa wa ke kira da 'alkyabbar mata', ta kwashe tuwon dare kenan, ta zubawa yara, suna cikin ci, sai ga Abba Baba ya shigo, yaran suka gaishe shi cikin nutsuwa da girmamawa. Ya amsa, tare da cewa 'kuna lafiya, ko?'
'Abba, yau bamu ganka ba tunda safe'
'Indo, yau naje gidan Hajiya Babba, tace tana gaishe da takwarar ta.'
Haj Kaltume ta kawo wa Abba Baba abinci tare da ruwa mai sanyi. Tasa yara sukai alwala, sukai addu'o'i, sannan sukai bacci. Ta dawo gun mijin ta suna hirar su har karfe sha daya yayi, sannan suma sukai alwala, sukai addu'a, sukai bacci.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 04, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

Kallon KaunaWhere stories live. Discover now