page 1

12.8K 612 41
                                    

*Haske writer's Asso (Home of expert and perfect writer's)*

*🗿WATA FUSKA🗿*

🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉🦉

*Billy galadanchi*

*Sadaukarwa ga qawata Hafsatul Elham*

01

Cikeda nutsuwarta take tafiya dukda yake yanayin ta kad'ai ya isa ya sanar dakai cewar lallai a gajiye take kuma kallon farko dazakawa fuskarta zaka tabbatar cewar lallai tana tattare da yunwa matsananciya.....batada sukuni batada cikakkiyar lapia tamkar wacce qwai ya fashewa aciki.... Iyakar inda aka direta bakin first gate na jami'ar usman d'anfodio d'in batada ko sisi!!! Batasan se yaushe zata isa gidansu ba dake low-cost.....Mataccen agogon dake wutsiyar hannunta daduk fatarshi ta gama tashi ta wurgawa kallo qarfe bakwai ta kusa....magrib kenan fa ta doso kai idan hakane tashiga ukunta da Baba iro...... Cira kafarta tayi taci gaba da tafiya sauri da sauri......se gab da isha ta isa k'ofar gidansu Babur d'in Baba iro ta wurgawa kallo ta tabbatar yau kashinta ya bushe batasan me aka gaya masa ba,batasan qazafin da za'a mata ba....batasan me ze mata ba!!!! Cikin dokawar qirji ta shura qafarta zuwa cikin gidan had'e da wara Bakinta dasunan yin sallam amma jin muryar Baba Azumi ne ya dakatar da ita....

"Ban isa in gayawa Nanuwa tajiba malam, Ban isa na hanata fita yawonta na banza ba, d'ari biyar daka bayar na basu yanda na baiwa Ummul haka itama na bata amma tunda tafice gidannan da safe har yanzu bata shigo ba nime zance?" Kwafa tajiyo shi yayi kanyace

"Yau sena wulaqanta rayuwarta kuwa agidannan wlhy, badai burinta ta b'atan suna da sunan gida ba wlhy bata isaba aiba gidan ubanta bane nan d'in" girjinta ne ya doka amma a haka murya na rawa tae sallama, da sauri Baba azumi tazo gunta

"Nanuwa lapia kuwa meya tsaidaki se yanzu kika shigo? Gashi kuma Baban ku se fad'a yakeyi,mesa bakyajine wai?" K'wallan datake qoqarin tarewa ne ya silalo mata tace

"Baba Azumi a qafa fa na dawo" wara ido tae da mamaki

"Kud'in motarki fad'uwa yae ne?" Mamakinta ya sanya Nanuwa kasa magana ta bita da kallo kurun kan wani yae magana har Baba iro ya taso yae kanta ya hauta da duka baji ba gani seda tae lilis ga yunwa sannan Baba Azumi ta qwaceta ta kaita d'akin dayake mallakinsu itada ummul, dariya tae bayan ta wurgar da ita kan matacciyar katifarta tace

"Wahalalliya er iska, idan kina numfashi sekin bar gidannan wlhy" batace komai ba tayita kuka tana mayarda numfarfashi sama sama......Ummul ce ta kalleta ta girgiza kai tace

"Mesa baki mun wayaba Nanuwa? Dasena bi ta departments d'nku na d'akkoki ai tare da mahal muka dawo" bata kulataba ita d'inma bawai dad'inta takejiba sedai takan kwatanta mata adalci wasu lokutan. da qyar ta iya miqewa zuwa ban dakin dake cikin dakin nasu tae wanka da ruwan d'imi dayike akwai heater jonawa kurun tae ta watso ta fito tae sallan magrib da isha sannan tafita ta ebo abinci tazo tanaci tana hawaye....

**************

Washe gari tunda safe tana idar da sallan asuba taje gun Baba iro,har qasa ta duqa

"Baba ina kwana?" Kallon takaici ya mata

"Lapia lau Nanuwa, lapia dai?"

"Dama Baba kud'in handout ne da akace mu siya nace barin maka magana" murmushi yae yace

"Dad'in abin gadon ubanki kikrta cinyewa, nawane kud'in?" Sadda kanta tae qasa tace

"Zekai dubu da d'ari biyu ga kud'in xuwa makaranta kuma" zaro dubu biyu yae ya miqa mata......

"Ni Nanuwa duk karuwancin nan dakikeyi ace wai ko sisi bazaki iya ajiyewa kiyi laluran makarantar ki, Allah ya wadaran naka ya lalace an tsotsi mugun hali a nonon uwa" qwallane ya gangaro mata ta miqe tana me ganin jiri na ebarta, idan bata karb'i kud'i a hannun Baba iro da kanta ba,Baba Azumi bawai batan zatayi ba....idan kuma tazo karb'a a gunsa seya zageta tatas ta uwa ta uba tukunna yake bata kudin.....shirinta tae kaman yanda ta saba acikin doguwar rigar yadin hijabi kalar ja, wacce take had'e da hijabinta da d'ankwalinta tayi kyau daidai nata irin kyawun irinna jan buzu!!! Hartakai qofar Baba Azumi ta kirata,tasan kwanan zancen karb'e kud'in data karb'a zatayi ita kuwa bata had'a komai da karatunta ba, bazata tab'a bari a ruguza mata abinda take ganin shikad'aine abinda zatayi ta taimaki kanta ba,wannan ya sanya tayi biris da kiran ta qarawa kafanta gudu har tana hard'ewa ta ruga da gudu tabar gidan har layinsu ma da gudu tabarshi ta nemai adaidaita ya d'auketa kan naira d'ari da hamsin zuwa dandima (Bus stop).....

WATA FUSKAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt