part 1-43

1.8K 37 1
                                        

1⃣➖5⃣

Sunana Munah Abdullahi, mahaifina da mahaifiyata da sauran 'yan'uwana kai har ma kadan daga cikin dangina duk muna zaune ne a kaduna, to amma ainihin tushen mu mutanan katsina ne gaba da baya, mahaifiyata wadda muke kira innar mu, ita kadai ce mata wajan baban mu amma ta cika gidan da 'ya'ya maza da mata dan haihuwarta goma sha shidda sai dai hudun karshe sun koma ga mahaliccin mu sai ya zamana na koma auta a gidan.
Manyan 'ya'yan gidan mata ne guda uku duk sunyi aure kowa tana da iyali, sai namiji ke bi masu mai suna Hammad, sannan aka sake haihuwar wasu matan guda uku, sai kuma maza zalla karshe na kasance ni daya mace kuma auta, na taso cikin jin dadi da kulawar iyaye harda 'yan'uwa, tun ina 'yar karama na gane cewa iyayena sunfi sona da kaunata, kowa ji yake dani tamkar ni dayace diya

Ranar wata juma'a bayan an sauko daga sallar juma'a gidan namu yayi albarka, da yake duk juma'a kowa yana ziyartar gida domin sada zumunci, lokacin shekaru na goma sha shidda, ina aji hudu makarantar gaba da primary, ka'idar mahaifinmu ne mace tana kare secondary zai aurar da ita maza kawai ke yin zurfi cikin ilmi, Nafi'u da Habib sune gaba dani dan haka suna matakin farko a jami'ar Danfodio dake sokoto, sai Hammad dake aiki a ABUJA, alokacin shekarun shi ashirin da biyar da haihuwa. ~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~~ Ranar yau ta juma'a ana kwala rana daya ke lokacin damuna ne.
Ni daya ce mace na rage banyi aure ba agidan, dan haka nike ta jigilar kaiwa da komowa na raba ma kowa abinci, Hammad ne kawai bai iso ba sai bayan la'asar ina daki na samu ina hutawa domin gaskiya na wahala ayau, na gaji tubus ko wanka na kasa yi kwance kawai nake kan gado ina lumshe ido tare da fatan bacci ya dauke ni, inajin muryar innar mu tana sallama amma nauyin baki yasa na kasa amsawa, ta shigo tana kallona, sannan tace, auta duk gajiyar ce haka?
Na danyi mika ina fadin gaskiya innar mu yau mutan gidan sun bani wahala da yawa, Ko fa wanka na kasa yi duk da yake yau rana ce mai muhimmanci, tayi murmushi, a'a kema ai dama wankan ba damunki yayi ba, gashi kuma Hammad ya dawo yace ki hadu mashi nashi abinci, na marairaitar da fuska alamun bana son tashi, innar mu tayi dariya tana shirin juyawa tace, dama kin tashi Danni baban ku yasa ni wani aiki, tana gama fadin hakan tayi ficewar ta.
Sai da nadan bata lokaci sannan na tashi na fice ina kunkuni ni daya dan dai ya zame mani dole ne.

Nayi sallama bangaren Hammad, jin babu amsa yasa nayi tunanin baya ciki sai kawai na afka da tray din kayan abincin, banyi zato ba balle tsammani mukayi karo da shi ya fito daga toilet, gaba daya dani da kayan abinci muka afka jikin shi, ni dai maza nayi na mike a tsorace ina kallon yarda salat da miya da kuma juice suka tarwatse mashi a lallausan farin yadin jikinshi, ya dade idanuwanshi suna kallon jikin shi, ina ga yana takaicin bata mashi kwlliya da nayi ne, fuskar shi adaure tamau ya dago yana mani mummunnan kallo, wani abin mamaki sam saina gaza bashi hakuri kallonshi kawai nake jikina yana rawa, dan nafi kowa sanin zafin ranshi da rashin daukar raini gana kasa dashi balle kuma ni da tamu batazo daya ba.
Ya matso ya dago hannunshi ya rike mani kunnena na dama da iyakacin karfinshi yake ja yana fadin zako ki gane kuskuranki tunda naga yawan shekarunki basu sa kinyi hankali ba ko ki gane yarda na tsane ki cikin gidan nan, sam Munah bana sonki bana kaunarki bana fatan ina bude ido ina ganin ki cikin gidan nan, yana Magana ni kuma hawaye ke shatato mani ba wai na jin zafin kunne na daya ja bane a'a na jin zafin kalaman shi, duk da cewa ya kamata in saba da jinsu, ya saki kunnan ya jawo ni da kayan jikina ya share nashi kayan sannan ya ingiza ni tare da cewa ki tabbatar kafin in kwanta bacci kinzo kin bani hakuri, fita ki bani waje sakara dabba kawai, tuni nayi waje ina kuka.

Takaici da bakin cikin Hammad suka hanani wanka sai da zan kwanta wajan goma na dare kenan, kwance nake ina son yin bacci amma na saka saboda fargabar zuwa bangaren Hammad inba shi hakuri kamar yarda ya umurce ni, naja tsuki tsanar shi na kara yawaita atare dani, nina rasa abinda nayi mashi ya tsane ni yaki jini na tun ina yarinya yake gwada mani azaba da jaddada mani rashin sona da baiyi, hakan yasa nima na tsaneshi arayuwata, kwata-kwata baya burgeni baya bani sha'awa duk da cewa shi daya ne na miji da mutan gidan ke sonshi suke gudun duk wani abinda zai taba zuciyarshi, na sake kallon agogo karo na uku, ya nuna karfe goma da kwata, na mike na zura rigar bacci na ta sama na sanya silifas na fice zuwa bangaren shi.

MUNAHStories to obsess over. Discover now