UMMU AYMANA PART 1

24.2K 447 87
                                    

🎀🎀🎀🎀🎀
*UMMU AYMANA*
🎀🎀🎀🎀🎀

Zahra Muhammad Mahmud

*Pure Moment of Life Writers (p.m.l)*

*Happy Sallah to all Muslims ummah over the world*

*Dedicated to my Gorgeous Sister,Fatima Abubakar Radda,always you are looking fine,once again happy Sallah to you and your family.*

Bissimillahi rahmanir raheem.

*page 1-2*

Ruga ce ta Fulani me d'auke da yawan jama'a Dan Rugar tana da girma sosai.

Wannan Rugar ba a ko ina take ba se a cikin Garin Gwongola,mutanan cikin wannan Ruga suna da al-adu kala-kala,kuma koda wasa basa sake da al-adun su Sun d'auki al-adun kamar ibada.

Malam Audu yana d'aya daga cikin mazauna rugar shida zuri"arsa gaba d'aya.

Malam Audu tsohone d'an kimanin shekaru 77 yana da mata d'aya Gwaggo Uwani da yara guda uku duka maza,Hamisu shine babba seme bimasa Shu'aibu,se k'aramin su Mahmoud wanda ake kira da Mudi.

Gaba D'ayan yaran na Malam Audu sunyi aure Sun hayayyafa ma kuma suna zaune tare dashi a Gida d'aya, shiyasa akewa Gidan kirari da Gidan gandu,gaba d'ayan su babu wanda yayi karatun Boko acikinsu dagasu har matansu sede na muhammadiyya sukayi.

Baba Hamisu kamar yadda yaransu ke kiransa,matarshi d'aya mesuna Saude, da yara guda hud'u,duka maza na farin sunanshi Jamilu,se Uwaisu,Nura,Usman.inna Saude macece mara mutunci ko kad'an bata ragawa duk wani mahaluki A cikin Gidan, shiyasa gaba d'aya Gidan kowa yake jin tsoronta harda shi kanshi Mijin nata yana under her control,be isa yayi abinda ba itace tasashi ba shiyasa kosu sirikan nata tsoronta sukeji, sabida gwanace gurin iya Bin bokaye da y'an bori.

Shu'aibu shima matarsa d'aya Furera da y'ay'a biyar biyu mata uku maza,Shafi'u shine babba se Muntari, se Hauwa,Ramatu,Suwaiba,Hauwa da Rahmatu sunyi aure tun tuni,sabida a al-adar Garin yarinya dole sede ta fara jinin al-ada a gidan mijinta, inko aka bari tafara a gidansu to ba makawa y'ar iskace,shiyasa daga shekara goma ake aurar dasu.Inna Furera irin matan nanne da ake cewa bakin ganga,munafukace ta ajin farko, tasan duk Wata hanya da zata bi ta hada mutum fad'a da Inna Saude sabida wannan halin natane ma yasa suke d'an d'asawa da ita Sauden.

Baba mudi ma matarsa d'aya me suna Zainabu da y'arsu guda d'aya me suna *UMMU AYMANA*.Zainabu Mace ce me sanyin Hali gata da hak'uri da kawaici,ko kad'an bata da d'aukar lamuranta da zafi,anashi b'angaran Baba mudi shima baya d'aukar rayuwa da zafi shima yanada hak'uri sosai da kawaici.

A al-adar Garin yara mata basa zuwa makarantar Boko, sabida acewarsu b'ata tarbiyya takeyi shiyasa kosu mazan basu d'auketa da muhimmanciba, sunfi maida hankali wajan neman kud'insu da kiwo da noma.

Baba Mudi yafi kowa rufin asiri a Gidan,dan a Rugarsu kaf babu me arzik'insa sabida d'an kasuwane, har fita yake zuwa wasu Garuruwan ya siyo kaya yazo ya siyar a rugar tasu,ganin hakane yasa mahaifinsa malam Audu k'ark'ashin jagorancin Inna Saude.ya d'oramasa nauyin ciyar da Gidan gaba d'aya da d'aukar d'awainiyar komai na Gidan, wannan hukunci beyiwa Mudi dad'iba,dan inde yaci gaba a haka wataran shima nashi k'arewa zasuyi Amman dayake shi mutum ne me kunya da kawaici Uwa Uba kuma biyayya,shiyasa ko a fuska be nuna yaji haushiba.

Tun daga wannan lokacin ko Maggi za'a siya sede a turo gurinshi,suko sauran y'an uwanshi sun mik'e k'afa basa komai sede ya je ya nemo ya kawo adafa suci, kuma ko godiya bazasuyi masa ba, sede ma su zageshi gaba d'aya haushin shi suke ji, hassada suke masa ba kad'anba.

Ummu Aymana tun tana jaririya yarinyace kyakkyawa,tana kama da mahaifiyarta sosai gata da hak'uri tun tana k'arama,wannan kyau da Allah yayiwa Ummu Aymana shine yajamata bak'in jini acikin Gidan nasu ko kad'an babu mesonta se Iyayanta,dan har kakan ninta tsoron kulata ma sukeyi sabida kar Saude taji haushi,shiyasa duk inda ta shiga kyarar ta akeyi acikin Gidan, sab'anin wajan Gidan kowa sonta yakeyi.

Vous avez atteint le dernier des chapitres publiés.

⏰ Dernière mise à jour : Sep 09, 2017 ⏰

Ajoutez cette histoire à votre Bibliothèque pour être informé des nouveaux chapitres !

UMMU AYMANAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant