Aylin's pov

158 13 0
                                        

Sanye take da doguwar rigar material brown gashin kanta kwance luf a bayan ta tana rike da baqar teddy mai ratsin baqi yatsan ta a cikin bakinta tana kallon tareeq yana saka takalmin kwallo...yaya xanje ya dago ido yana kallonta baby ai mata basa kwallo ta turo baki  Rana buga  qafa a qasa nidai xanje...Umma kisa baki mana kullum sai ki barni da ita tana min rigima

Umma dake xaune kusa da murhu tana hada wutar tuwan dare tace enace tun farko na fada maka fitar da kake da ita bashida amfani gashi nan ka sakata yarinya ai sai kaji da ita...yayah nidai xanje ta fada idonta ya cika da hawaye ohhh Allah na aylin come here ya daukota ya Dora cinyarshi ya saka hannu ya gyara gashin kanta daya rufe gefen fuskarta haba baby na miye abin kuka a nan baki San kin girma ba u are going to five years old fa next two months kina so Umma tace ke yarinyace ta girgixa kai tana tsotsar yatsan ta ewwa to daina kuka danaje ball na dawo xamuje gun hajiya xakije??? Ta jinjina kai alamar er to yi min dariya mana tayi murmushi ta soke kai a jikinshi ya lumshe ido yana bubuga bayanta

Umma ta xuba musu ido da murmushi a fuskarta marayun yaranta masu tsananin kaunar juna ta goge hawayen da ya xubo mata tanaji a ranta xatayi koma miye don inganta rayuwar su ko ba komai tasan tareeq xai ji qan qanwarsa bayan ranta  ya dirketa qasa ewwa my luvly one na tafi ko ta jinjina kai bara na boye dakin Umma banaso naga tafiyanka in yayah ya fita umma kirani...ya xuba mata ido yana jin Santa na qara shigarshi ta shige dakin ta boye bayan labulen umma ....Ummah ya tafi? Ummah tayu dariya yanxu dai qara jira ya doqa kusa da qafar Ummah shi yace Ummah na zan je wasa ta dafa kanshi Allah ya dawo da kai lafiya ka kula da kanka ka rike....ya tareta gskia da amana ko yayi dariya Umma har na haddace wannan nasihar ball xani fa ba Neman Kudi ba ya mike ya nufi qofa baby na tafi ya fice ta fito ta xauna tana sunbura baki

Tareeq's POV

Ina fitowa gidansu Habib na nufa a bakin qofa muka hadu ahh maxa yane? Habib ya fada yana bani hannu ya na ganka haka kuma kasan xamuyi wasa fa da yan dogon qarfe...habib ya bigi goshin shi oh shittttt! Wallahi na manta tun daxu baba ya aikeni na tsaya kallon marlin gashi time ya qure ya xaayi? Kaje Aiken ni xanje ball in na dawo zan baka labari ya girgixa kai haba tareeq ka rakani mana mu dawo...ya harareshi nine na hanaka xuwa aikin tun  daxu?? Haba mana habib ya langwage kayi ka gama wallhi baxan je ba ya fada yana shirin juyawa habib yasa qafa ya halbeshi banxa kawai tareeq ya bishi da gudu har cikin gida suna shiga tsakiyar gidan baba na fitowa ahh miye haka kuma ya fada yana karba jikarsa hannun mama

Baba ina yini tareeq ya fada yana Sosa Kansa cikin tsananin jin kunya...lafiya lao Ku baxaku taba girma ba ko tareeq kaima da nake gani mai hankali kana nema ka biyewa habib ina amfanin wasa gudu kamar wasu yara ko su hanif baxasuyi ba ai...mama ta kallesu tana Dan dariya ai su habif sunfi su tareeq hankali shekara goma sha bakwai xasuyi fa Amma kamar yaran goye yanxu kai habib ba Aiken alhaji yayi ba? Ya kalleta yana Sosa kai ai na fita xani kuma tareeq ya biyoni ya hanani tafiya...tareeq ya harareshi wallahi qarya yake shine ya halbeni a qafa kinga ma gun...baba ya girgixa kai ai ni nama karbi sakona tuntuni waye xai tsaya jiranka? Ya nuna habib kayi hakuri baba suka hada baki gun fada ya jinjika kai Allah ya shiryaku ni na wuce hajiya ....to alhaji Allah ya kiyaye...har qofar gidan suka biyoshi ya Shiga mota rshi civic ya tafi su habib nada rufin asiri dai dai gwargwado babanshi maaikacin gwamnati ne yaranshi ukku Anty marwa CE babba sai habib da aura hanif

Habib ya fito sanye da kayan ball hanun shi riqe da takalmi Babah inaji fa dolle na siya takalmi wannan watan ji yadda nawa ya xama fa ya fada yana dago takalmin tareeq yayi dariya wanan muguwar qafar taka ba dolle taci takalmi ba ai tafi taka mai kama data mata ya fada yana mikewa daga saka takalman mama mun tafi Allah ya kiyaye ta fada tana rufe tukunya daga kitchen tareeq in kun dawo ka biyo ka karba saqo inji alhaji to mama ya fada yana fita bayan habib

Bayan magariba suka nufo gida Sauri Sauri yakeyi habib ya tura qofar suka shiga ko sallama beyi ba mama ta fara fada tun daxu nake jiranku kunje kunyi xaman Ku ina amfanin wannan abun sa kukeyi? Mama sai da fa mukayi sallah sannan kuma ma yanxu yanxu aka gama ai habib ya bata amsa yana xama gefen ta tareeq ma xama yayi kiyi hakru mama ya fada yana yar dariya ta harareshi ka dauka ga kayan abinci nan ga Kudi dubu coma yace na makarantar ka kaida Aylin ne....tareeq ya rasa dame xai godewa mama da baba har da shi kanshi Habib ya xubawa ledar ido hawaye ciki da idonsa habib ya mike ya xiro jallabiya ya dauki ledar muje ko sai lokacin ya iya furta mun gode mama Allah ya bar xuminci tayi murmushi ameen kuje kar dare yayi suka fice sukuku tareeq yake tafiya ya rasa wane yanayi yake tabbas sun taimaka sosai sabida last shinkafar gidance sukaci yau

Habib ya tura qofar da sallama aylinta ruga da guda ta shige jikin habib ahhhhh my one and only ya fada yana dagata sama tareeq ya dauki ledar ya Isa gun Umma dake xaune kan sallaya ah habibu kun dawo ta fada tana kallon habib er Umma ina yini? Daxu naxo kina barcin rana ai er wallhi tareeq miye a ledar kuma? Wallhi baba ya bada saqo wai harda Kudi dubu goma hawaye suka xubo mata ta share su da hijabi mungode habibu mungode ya xauna da aylin a qafarshi haba Ummah ai yiwa Kaine miye amfanin tare? Tareeq ya shigar da kayan kitchen ya xubawa aylin ido wadda ko kallonshi batayi baby me nayi kuma? Ta qara narkewa jikin habib xo nan ya fada yana mika hannu ta maqale kafada aaah ta fada tana shirin kuka...Malam ka qyalemin mata tace bata xuwa ana dollene? Habib ya fada yana ture hannun tareeq ta xunbura baki bashi ya tafiyanshi ba ya barni tareeq ya mike bara naje yawo na tunda Baki sona ya nufi qofa iya qarfi ta ta ruga ta rungumeshi a baya ya dagota yana share mata hawaye sorry erh baxan qara ba ta kwanta jikinshi habib yana kallonsu cike da shaawa


I can't believe it! I make it this far please vote and comment love u all

TAREEQحيث تعيش القصص. اكتشف الآن