Chapter 1❤

1.2K 35 3
                                    

Bissimillahirrahmanirrahim
  Dasunan Allah, Mai rahama Maijinkai.

😃"""Yarbaabah"""😃

Tana tsakar baccinta na la'asar Wanda yazamar mata tamkar dabi'a Idan bata Yi shiba bata samun sukuni, taji haske ya baje Mata fuskarar adalilin bude labulen Taga Da Fatie Tayi, kansancewar rana tafara Sauka, ta juya takalli Umulkhairee da ke kwance tacika tayi fal jitake kamar ta rufe yayarta da duka, Saboda ta tsaida Mata mafarkin da bashi da gaba bare bata Saboda babu ranar da Umulkhairee zata kwanta batareda tayishi. Haba ya fatie sunan da ummalkhairee take Kiran yayarta dashi , kinsan irin mafarkin Danake,saura Kadan naga fuskarshi kikazo kika tasheni dariyace ta kubuce ma ya Fatie jin maganar da ummalkhairee tayi sannan tace aikin Kenan,bakida aiki se mafarkin aljanu, dasauri Ummalkhairee ta Kalli yayarta da rashin fahimtar abinda take nufi, ba aljani bane ya Fatie wallhi mutun ne kuma saura kadan naga fuskarshi kika tadani,ta tashi daniyar Shiga toilet tayi wanka tayo alwala, yayarta tace maama tace kije kuyi girki tareda raliya,umma tace girki kuma, Fatie tace eh girki saboda maama tace dagayau zamu rika shiga Kitchen anayin girkin damu,saboda wanna asarar baccin da kika sa gaba, ummalkhairee ta turo baki tawuce tashige toilet ta banko kofar, Fatie tace yi aniya ki balle kofar ta kwashe da dariya saboda tasan ran ummalkhairee yagama baci saboda tagaji amma yazasuyi, dole subi umarnin maama.
  Tana shiga ta sakar ma kanta ruwa ta Rufe idanunta Tana jin yadda ruwan ke zubarmata tindaga samankanta har Kasa, Tana hango surar mutumin da batasaniba, bata kuma ga fuskar shiba, sai tsayinsa da girmansa da takan gani akodayaushe, murmushine dabatasan tayayaba ya bayyana a fuskarta, Lura tayi da kanta yagama jikewa, tayi sauri ta Murza sabulu ajikinta kasancewar bata wanka da soso saboda rashes dasuke fito mata,sauri tafara da ta tina hukuncin da maama ta yanke masu Fatie na fita ta nufi dakin masu aiki Taga Bilki a zaune tana tsifa tace yauwa bilki jeki gyara mana daki da Allah, ta ansa da toh, Fatie tafita tabarta tana daura dankwali a kanta.
Bilki ce tashigo rike da tsintsiya ahanunta ta ajiye tafara gyaran gado sannan ta gyara ko  ina, ta nufi inda tsintsiyar take ta dauka tafara Shara, tashare tas ta kashe AC ta kunna burner ta turaren wuta ta fita, da sauri ta watsa ruwa tafito da towel Daure a jikinta,tabude wardrobe ta dauko karamin towel ta aza A kanta tana goge gashinta saboda Yasha ruwa seda ta tabbatar da babu ruwa dake zubowa a gashin sannan ta nufi wardrobe dinta da take a gyare kodayaushe, saboda yana daya daga cikin abinda ummalkhairee bata so taga lockernta a bace ta juya jerin kayan baccinta taciro lemon pyjamas da Abbanta ya yasiyo mata riga da Wando bata gajiya dasasu duk wankin dazaa dauka dasu aciki saboda Lemon ce best colour dinta tarufe wardrobe ta nufi dress mirror ta fesa sure,tafesa light perfume sannan tabude chest of drawer ta dauki inners da hula sannan tashafa Mai tasaka kaya ta dauki hijab da salaya ta tada sallah.
    Fatie na barin dakinsu bilki ta wuce dakin maama tayi sallama sannan tashiga ta taradda mamanta Tana sanye da gilashi littafi rike ahanunta alamar azkar takeyi kasancewar anfiso ayi azkar bayan sallah magrib ba La'asar ba, samu wuri tayi tazauna seda ta idar sannan tace maama inawuni ta ansa Tamike tashiga toilet tayo alwala, maama tace Fatima Abbanku ya Dawo? Fatie tace aa maama banajin yadawo, ummafa ta tashi daga asararan baccin da take? Eh na tadata nakuma Fada mata abinda kikace tace to dakyau.Tana idar da sallah tadauko fliet tayi flieting dakin sannan takashe burner tawuce ta latsa switch din fitila ta rage AC tarufe dakin ta fita.dakin maama tawuce tashiga da sallama maama ta ansa umma tagaisheta ta ansa lfy kalau Umma ya bacci ta sunkuyar da kanta Tana dariya sannan tadago tace maama abba yadawo, maama tace Fatie tace batasaniba amma ina ganin ya isa dawowa yanzu, Bara nadubo nagani Cewar ummafa, maama tace to 'yarbaba daganan se kiwuce kitchen ki tambayi raliya idan Kan san ya dahu,idan be dahuba ki dauki padanol guda biyu kisaka aciki, se ku Dora tuwan semo miyar kubewa Danya tace to maama ta Mike tafita.
Corridor Tabi da guda da murmushi a fuskarta tabi hanyar da zata sadata da part din Abbanta ta kanjita cikin nishadi aduk lokacinda take tareda mahaifinta,dasallama tashiga bakowa Palon bakajin komai sai kamshin turaren wuta Wanda yakasance kashin dakine ako dayaushe sekuma sanyin AC da annashuwa Kai tasaye tawuce Dayan parlon kasancawa,yafi Zama a Karamin parlo saboda parlon parko girmanshi yayi y yawa da sallama tashiga nan ma gani tayi babu alamar Abbanta se tafara tinanin ko bedawoba, harta juya zata fita se tahango makullin motarshi,juyowar dazatayi taganshi yana fitowa daga guest toilet na cikin parlon da gudu takarasa ta rungumeshi Shima rungumeta yayi yace Yi ahankali Kaki Fadi Mamana banace maki kidena rugowa kina fado Mani, kin girma yanzu y'all family fuskan,sai taji dadi daya dago fuskanta yace ya akai ne minene zo inji,suka nufi daya daga cikin sofa dakin yazauna ta Zauna kusa dashi,abbana inji ummalkhairee naam uwar alkhairee, Abba ya akai Baka dawo dawuri ba yau,abba yace meeting mukayi da gwamna, mamana kinyi sallah? Eh Abbana nayi sallah, Toni banyiba bara nayi senabaki labarin meeting din damukayi yau.Toh Abba kamun addua,wanna dolene mamana,idan ban makiba wazanyiwa, toh Abbana nagode, bara naje kitchen maama tace Nida ya fatie zamu rinka shiga Kitchen anayin girki damu, Abba ya Dan bude idanshi alamar gamsuwa, kai maama ta kyauta, diyata ta girma kenan,shikenan da kin iya girki zanmaki aure .tabata fuska Kai abba am just 20 fa kuma am still a baby,yes of course u are my baby but Ai kin girma,Tayi dariya tafice tanufi kitchen, daidai balconyn kitchen tahadu da Taheer,Ya taheer inawuni, ya amsa lfy loa Auta,maama fa umma tace tana daki Abbah fa yadawo?eh shima yana daki yawuce itakuma ta Ida shiga Kitchen ta taradda raliya na fasa ledan semo,tace raliya ina San da maama tace Adora, raliya tanuna Mata dacewa gashican saura kadan ya karasa tabude ta saka spoon tafito da wani part karami ta taba taji dasauri tamaida tarufe tukinyar tace inazuwa,parloo Takoma tanufi show glass din dake dining tajawo lockern Sama taciro wani box tabude tadauki panadol Extra guda biyu kamar yadda maama tafada Mata tarufe box din tamaida locker, Takoma kitchen ta bude marfin tasaka maganin aciki ta juya naman sanan tamaida ta rufe.Tace kin tuka tuwon?raliya tace aa yanzude zan tuka miyar nakada kinsan hajiya bataso agama tuwo da wuri Kafin miya, shiyasa nafara kada miyar,Toshikenan bani muciyar nizan tuka tuwon inji Umulkhairee, raliya tamika mata muciyar,tace kirinka zuba Mani garin ta ansa da to, da bissimillah tafara ahaka suka tuka tuwon harya tuku sanan ummalkhairee ta cire muciyar ta rage gas din tamaida marfin tukinyar ta rufe,raliya da Allah miko kayan daza'a kwashe tuwon da warmers din daza'a saka ta ansa da to,ahaka suka kwashe tuwon suka saka raliya tadauka tayi hanyar dining,ummalkhairee ce ta dauko miya raliya takoma tadauko warmer cow tail suka jera komai har plates,tayi hanyar part din daddy saboda tasan maama nacan da sallama ta shiga,maama na ganinta tace umma yaya tace maama mungama mun jera komai tace to shikenan gamunan zuwa, tace to tajuya tafita dakinsu tanufa adaidai kofan dakin suka ci Karo da fatie suka koyi Karo Yar Kara umma tasaki fatie ko tabushe da dariya Wayyo ni Allah ya fatie kin Mani kurma,to aikece baki tafiya a hankali, haba sekace makauniya Kaina har yafara ciwo kungama ne ta tambayeta Tana murza goshinta daya Bugu,tin dazu muka Gama zuwa nayi nakiraki muje nafada ma maama tace gasunan kinfada masu Ya Taheer,lah kinga Namanta bara nafada masu fatie tace toh tafita.
  Direct boys quarters tanufa inda yakasance sashen yayyanta biyu, tayi knocking suka amsa dawaye tace Yauwa  Ya Taufik kuzo muyi dinner ku ake jira ya ansata da Toh we are coming, tajuya takoma cikin Gida Tana shiga Taga Abba da maama sunfito Sega ya fatie itama takarasa kowa yanemi wurin daya Saba zama Abba ne yace ina Taheer da Taufik, nakirasu bata Ida rufe bakintaba sallamarsu ta bayyana aka ansamasu, suka gaida kowa suka nemi wuri suka zauna abba yayi masu addua'a kowa yazoba yafara cin nashi,ummace tafara tashi kusan kullun, kowama yasani bata cika cin abinciba sosai shiyasa take 'yarkarama Marar jikinta, Abbane yace haba uwar alkhairi har kin Gama, umma tace Eh abba nakoshi.Shiyasa kowa yafiki girma saboda rashin cin abincin da kikeyi tayi dariya tadauki plate dinta tayi hanyar kitchen ta aje a sink tabude fridge din kitchen ta dauki fanta tafito daga kitchen din tayi hanyar dakinsu,mamana har zaki koma daki,tajuyo tace eh abba banyi isha'i ba yace to yimaza kiyi manana seda safe ko? tace eh abba seda safe yace Allah yatashemu lfy tace Ameen tawuce ciki.fitila takunna sannan ta aje fanatar tawuce toilet Tayo alwala taxo ta kabbara sallah,ta sallame ta tashi tanufi inda take hanging jukkunan ta tabude daya daga cikin bags dinta tafito da handout da small Jotter da pen tanufi reading desk dinta ta kunna side lamp ta zauna tafara bude takardar page by page ahankali take fahimtar abinda aka rubuta a paper kasancewa test zasuyi ta marketing  gobe da karfe tara
     Ahankali tabude idanunta se lokacin ta Lura da inda tayi bacci handout din ta Rufe  sanan takashe side lamp din ta Mike tamaida kujerar cikin desk din ta nufi hanyar toilet da niyar yin alwala bacci tafito ta wuce wurin switch din fitila ta kashe ta nufi Dayan side din gadon ta kwanta tabama yayarta baya. Addua'a  bacci takeyi cikin Ranta har tagama sannan ta shafa a fuskarta ta Rufe ido se dai ummalkhairee ta tsinci kanta a daniyar bacci

#teamuUmmulkhairee
#'yarbabah readers,
Don't forget to vote pls

❤Umulkhairee❤Where stories live. Discover now