Kalbim Dandano

2.1K 17 2
                                        

*_KALBIM_*
_Mamuhgee_

_DANDANO_

_Bismillahir Rahmanirraheem_

KALBIM Zuciya! Zuciya daya ce Amma rai uku ne kirjinsu yake bugawa akanta,
Zuciyar da me zuciyar sune abinda yafi so da tsananin kauna a rayuwarsa fiyeda tasa rayuwar da zuciyarsa wadda xai iya zare tasa zuciyar batareda tinanun komaiba ya bayar akansu sedai kuma lokaci daya ba zato ba tsammani wata zuciyar ta shiga tsakanin tasa zuciyar da zuciyar da itace hasken idaniya da rayuwarsa.

Kalbim ta zama zuciyar da kowa ke buqata dan rayuwa,
Kalbim itace zuciyar da zata zama sanadin ràyuwarsu su duka wadda kowannensu bazai iya rayuwa batareda bugawar zuciyaba,

Tayaya zasu fuskanci rayuwar da kalubalensu ce su dukan akan abu daya,

Bazata rayu batareda kalbim ba shima bazai rayu batareda kalbim ba..

The great AZIZ AY LIMBA zaune akan sofa sanye da Ash cashmere wanda yake lafe a farar shiny skin dinsa dayake bayyanarda asalin hutu da luxurious life din dayake cikinta.

Takardan dayake gabansa ya zubawa idanuwansa da suka saka personal person dinsa dayake tsaye gabansa sauke numfashi mara sauti sbd sanin duk duniya a rayuwar LIMBA bayan bautawa ubangijinsa babu abinda yakeda tsananin mahimmanci da da girgiza dakkakiyar zuciyarsa datake kaman a bushe irin wannan lamarin daya shafi Wannan abinda yake gabansu.

Sake kallan takardun yayi ya zubawa sunan asibitin dayake jikin takardun idanuwansa yana sake jinjina lamarin ubangiji da babu kamarsa a duniya dan kuwa shine kadai wanda ya isa yayi abinda babu wanda zai juya hakan dan gashi LIMBA da babu abinda ya rasa a rayuwa hakama babu abinda bazai iya zubarda dukiya komai yawanta ba ya bawa 'yar datake gabansa ba amma yau Allah ya hanata abinda kudinsa bazasu iya siya mata ba hakama abinda take buqata abu ne me wuyar samuwa.

Tayaya zai iya saka hannu a takardar datake kamar hakura ne da 'yar da bazai iya hakura da ita ba matiqar ba Allah ne ya dauke ranta da babu yanda zaiyi??
Tayaya zaiyi rayuwa da sanin zuciyar da  'yarsa ke buqata dan ta rayu tana kirjin wata tana bugawa bayan zuciyar itace asalin tasa rayuwar data sakasa zamowa jarumin dayake a yanzu.???

Ja me tsananin da idanuwansa sukai har suka saka dogon hancinsa yin ja shima ya saka Personal person ya dago a sanyaye ya sake kalla yana dan sake sauke numfashi me zafin gaske nasa idanuwan na kadawa jajir shima.

Sake daukan wani irin shiru mai saka duk wanda ya shiga mutuwar jiki gurin ya sake dauka securities ma dake bakin kofa da block din dasuke na lafiyayyar asibitin tsit sukai sbd sanin rayuwar LIMBA ce gaba dayanta a kwance duk da abu ne da aka saba dashi.

ZADEEN's family a nasu bangaren babu kalar tarin arziki da dukiyar da basuma san yawansa tareda duniya harma da power da Allah bai basu ba sedai duniyarsu rayuwa daya ce tafi musu duka rayuwarsu da duka abinda suka mallaka itace JANNAH ZADEENS,

Jannah itace ruhi da ràyuwarsu gabaki dayansu,
Babu wata rai ko dan adam da bazasu iya kwata ba dan jannah zad ta rayu wadda itace kadai Allah basu a halinda basuda abin yi bayan jiran saurautan Allah din akanta duk da basu taba gazawa ko fasa neman mata kalbim da itace xuciyar da zata rayar da ita tasu rayuwar ta rayu.

Kaf familyn ZADEENS babu wanda bazai iya aikata komaiba ya zubar da kowace irin dukiya dan bawa Jannah kalbim din da zata rayu taci gaba da kasancewa sanyin idanuwarsu da karfin rayuwarsu.

Zuciya daya JANNAH ZAADEN ke buqata ta rayu
Hakama zuciya daya BABY FALAK LIMBA tale buqata ta rayu,

Zai iya bada rayuwarsa da duka abinda ya mallaka komai akan 'yarsa Falak limba ta mallaki kalbim,

Zasu iya bada komai da suka mallaka da rayukan mutanen da babu adadi sun yadda su zamo masu laifi da girman barna akan tasu 'yar JANNAH ZADEEN ta mallaki kalbim.

KALBIM daya ce,amma rayukan uku ne,
Kirji daya ne kalbim zata shiga sedai babu wanda yake jin zai yadda ya rasa wanda suke ganin sune rayuwarsu,

Abin tambayar ita KALBIM din asalinta ta waye?
Tayaya zuciyar zata baro kirjin me ita ta sauka a kirjin Hasken idaniyar zadeens ko kirjin rayuwar limbas?

Waye zai samu waye zai rasa?
Meye mafitar da zata kashe wutar da babu wanda zai iya barin ya rasa nasa bayan yanada mafita.???

ALKWARI ne da sukai da rayuwarsu ko zasu karar da mutanen da duk idanuwansu suka ganar musu sai sun nemo KALBIM koda kuwa zasu karar da kowa to zasu taru su cire tasu idan har zatai.

ALWASHI ne ya dauka da rayuwarsa idan zai rasa komai da kowa da ransa saiya karbowa hasken idaniyarsa KALBIM ko a kirjin waye take indai itace kalbim din farko datake bugawa a gabansa.

LABARIN KALBIM LABARI DA ZAMU SHIGA SABON YANAYIN DA BAMU SABA SHIGA BA SBD TSARI DA NUTSUWAR DA YAKE TAFE DASHI.

SOYAYYA CE MAI ZAFIN GASKE DA ZATA SAKA KOWA YIN ABINDA BAI TABA TINANIN SAMUN KANSA DA SAMUN KANSU A CIKINTABA,

#HOTLOVE
#BESTLOVESTORY
#BILLIONAIRES WAR/REVENGE LOVE
#CRAZYLOVERS
#LIFE
#DONORS
#FAMILYSLOVE
#FATHER'SLOVE
#BROTHERSLOVE
#SACRIFICES
#ZAFAFA BIYAR

ZAFAFA BIYAR 2024/2025
1-KALBIM 500
Mamuhgee

2-A DUNIYATA 500
Huguma

3-AJIYA A DUHU 500
Billyn Abdul

4-KIRJIN ME HANKALI 500
Miss xoxo

For duka books din 2k

Pay at
0022419171 ACCESSBANK MARYAM SANI GUMMI

Shedan biya at
09033181070

KALBIMTempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang