BATOOL1

0 0 0
                                        

💖 *BATOOL* 💖

By Qamshi✍🏻

*All* *thanks* *goes* *to* *Almighty* *Allah* *for* *making* *it* *possible* *to* *start* *this* *book*

*FIRST* *CLASS* *WRITER'S* *ASSOCIATION*
(Home of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation)

_Bismillah_ ✍️

P1.

A yayinda kowane mahaluki yake kwance a d'akinsa yana hutawa sakamakon ruwan saman da ake sheƙawa tamkar da bakin ƙwarya, a lokacin Batool da ke zaune a nata d'akin ita da maƙociyarta Ramlah suna fira ta miƙe a d'an razane tamkar wacce ta tuna wani abin, "Aunty lafiya?" Ramlah ta ce ma Batool da ta nufi hanyar fita da ga daƙi, ba tare da ta waigo ba ta ce, "ina zuwa.. "amma fita ba lema?" Ramlah ta ce, ganin ko kad'an Batool ba ta da niyyar dakatawa ya sakata cewa Allah ya kyauta, don tuni ta fice da ga d'akin ba tare da yin la'akari da ruwan da ake yin ba, duk da ko muran da take fama da ita. Kai tsaye kitchen d'inta da a ka katange da kwano ta shiga, duk da ba wai an rufeshi ba ne ruf-ruf, tukunya ta dauraye, sannan ta sauke tukunyar da ta rab'a a gefe saboda ruwan da ya ke zubowa, tafasassahen tumatirinta da a ko da yaushe ba ka rasata da shi ta zuba a tukunyar sannan ta bi da mangyad'a da farin magi, wata wutar ta kuma hadawa ta dora ruwan zafi, sannan ta dakko 'yar madaidaiciyar doyarta ta fere ta zuba a tukunyar, cikin dan lokaci ta kammala miyarta da ko kad'an ba ta zuba ma ruwa ba, sannan ta sauke doyar ta saka a turmi, sosai ta daka doyar ta yi laushi, ta gama ta juye a kololi, ta kuma d'aura wata tukunyar, miyar alaiyahu ta dafa wanda hakan alamace ta ana so a yi mixing taushen with stew, a dai dai dan lokacin kuma ruwan saman ya dakata, yanda Batool ta yi matuk'ar firgita zai tabbatar maka da cewa tana da damuwa, "innalillahi wa'inna ilahir raji'un, anya Aunty kina da lafiya kuwa?" Ramlah da ita ce silar firgicin na ta ta ce, Batool ta k'irk'iri murmushi ta na share zufan da ta had'a ta ce, "me kika gani?" Tana maganar ne tana fita, Ramlah ta bita da ido baki bud'e, duk da ba wannan lokacin ba ne karo na farko da ta fara ganinta a irin wannan ya nayin ba, sai dai na yau din ya banbanta, ganin ta d'auki bokitin wanka ta dibi ruwan cikin banbunta da kusan rabinshi ya kasance na sama ya sakata saurin k'arasawa gareta, "ba dai wanka da ruwan sanyi ba Aunty?, ai dai ko ba ki duba lafiyanki ba kya duba sanyin da ake yi" Ramlah ta ce, sai dai a wannan karon ma murmushin kawai Batool ta yi mata, don ba ta san abin da za ta ce mata ba, ba kuma tare da b'ata lokaci ba ta d'auki bokitin ta nufi band'aki, ta yi wanka ta fito, ta ijjiye bokitin a k'ofar d'aki ta shiga da kwandon cikin d'aki, "wankan dai ki ka yi?" Ramlah ta ce, "ya kusa dawowa ne" Kawai Batool ta ce ta nufi bedroom, tab'e baki Ramlah ta yi ta koma saman cushing ta kwanta, da farko kamar ba za ta fita d'akin ba sai kuma ta tashi ta fita, ko da Batool ta fito parlor ta tarar Ramlah ba ta nan, hakan ya saka ta diban abinci a flate ta kai mata d'akinta, tare da yi mata sai da safe, ba k'aramin faduwar gaba Batool ta tsinci kanta a ciki ba a lokacin da ta nufo d'akinta ta ji k'amshin turaren mai gidanta, ta jima a bakin k'ofa tana tunanen abin da za ta ce mai idan ya tambayeta da ga in da take, don ya hanata fita ko da bakin k'ofar d'aki ne in dai ba bu dalili balle kuma da daddarennan, ganin tana ta k'arama kanta laifi ya sakata tura kofan bakinta d'auke da sallama, ba ta sameshi a parlor ba, sai ta nufi bedroom, tsaye ta same shi yana ta famar safa da marwa, jin shigowarta ya sakashi dakatawa, sai dai kuma hakan bai sakashi juyowa ba, "sannu da dawowa" Batool ta yi jarumtar ce mai cikin rawar murya, bai amsata ba, ya shige band'aki, ya fi 1hour a bandakin kafin ya fito, har a lokacin kuma Batool ta kasa zama, saboda tunanan hukuncin da mai gidan nata zai yi mata. Da ya fito wankan turare kawai ya shafa ya jawo trayn abinci kusa da shi, da sauri Batool ta duka domin sarving d'inshi, sai dai gigitaccen marin da ya sauke mata ya sakata saurin ja da baya har ta na k'ok'arin bige baki, bai bi ta kanta ba ya tsallake ya bar d'akin, dawowan da bai yi ba kenan har zuwa safiya. Cikin dare Batool ta dinga juyi a kan cushing saboda baccin da yaki zuwa mata, duk da ba wai ta saba kwana tare da mai gidannata ba ne, amma yau sai ta ji daban, tunanen in da zai je ya kwana ya hanata rimtsawa.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 04, 2024 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MaryamStories to obsess over. Discover now