Chapter 1

534 15 4
                                        

REINA 💍

Book 1

    By Saliha A. Na'ibi (Seemahwrites)

Women of words writers

Sadaukarwa ga my dear Hanifah shamaki da addaririya ta Ramlat abdulrahman manga(mai dambu). Ina godiya da sahihiyar ƙauna, Allah ya barmu tare❤️.

Disclaimer: Ban amince a sauya min littafi ta ko wace irin siga ko a ɗaura min a wata channel na youtube ba tare da izini na ba, yin hakan babban kuskure ne kuma zai sanya mu saka ƙafar matsatstsen wando ɗaya da mutum

Any resemblance to any figure or event, deceased or living is purely coincidental

بسم الله الرحمان الرحيم

01...shi zumunci a wannan zamanin na mai shi ne, ga masu hannu da maiƙo ake sada zumunta mai bushashshiyar hannu kuwa saidai shi ya sada ta"
Taɓe baki Saudat tayi tana gyara kwanciyar Suhail a jikin ta wanda tunda iskar napep ta kaɗa shi barci yayi awon gaba da shi
"Amma abin yayi yawa Abban Yaseer. Ko wani hidima nasu muna kan zirya a hanya amma ko sau ɗaya! Ko sau ɗaya fa ban taɓa haihuwa mutanen nan suka ɗago ɗaya daga cikin su yazo mana barka ko suna ba saidai mu ko yaushe muna kan faman kashe kuɗin adaidaita zuwa gidajen su.
Yamutsa fuska yayi alamun baiji daɗin zancen ta ba, ga Yaseer ɗin dake zaune a tsakanin su ya kafe shi da idanu yana dakon amsar da mahaifin nasu zai bayar don da gaske ko shi mai shekaru 11 ya fahimci cewa yawan zirya da suke ma ƴan uwan mahaifin nashi ba buƙata ko appreciating suke yi ba balle kuma mahaifiyar da ta haife su.
"Ƴan uwana ne fa Saudah. Ki taya ni son su mana"

Girgiza kai tayi "nifa ba son ƴan uwan ka bane bana yi, kawai yanda suke treating ɗinmu ne bani jin daɗi gaskiya. Su basu ɗauke mu a matsayin ƴan uwa ba sai kaman masu aikin su kuma ba don basu da isassun masu musu hidima bane A'a! Don kawai a gwada mana matsayin mu ne"

"Nima idan na shiga wasan su Jamal kora ta suke yi wai wasan su ba na ƴan ƙauye bane" cewar Yaseer .
Kama baki Saudat tayi. "Kaji marasa kunyan yara, duk baka girme musu bane don sun samu ma kai ke binsu har zasu na maka rashin kunya?"

Kamal ya ɗaura hannu saman cinyar Yaseer ɗin gudun kada ya biye wa mahaifiyar shi su mulmula ƙaramin zance zuwa babba.
"Kuɗi shi ke bada matsayi ba shekaru ba. Ku lura mana cikin su Alhaji Tahir ne ƙarami Amma shine gaba a komi na hidimar family, ko family meeting za'a yi ba mai fara magana sai yayi, kuma idan ya bada shawara a take zai rikiɗe ya koma umarni, ba mai ja dashi a kan adalci ko rashin adalcin sa ba don komai ba sai don Allah ya wadata shi fiye da sauran. don haka kada kaji komai don ka girme su tunda nasu gidan kazo sai ka lallaɓa su har su barka ka shiga wasan ko?".

"Oh shima koya mishi jurar wulaƙanci kenan zaka yi?" Saudat tayi kicin-kicin da fuska.

Bai samu damar bata amsa ba kasancewar sun iso. Motoci ne kala-kala jere har kusan ƙarshen layin, shi yasa a tsallake mai napep yayi parking yana jiran su fita su sallame shi.
Kamal ya ɗauki Suhail dake barci saudat kuma ta janyo ƙaton cikin ta da ƙyar ta fito tana gyara zaman wuyan hijab ɗinta da baƙar jakar ta ƴar kullum wanda kwance ne Hajiya Fauziyya ta bata shine ya zamo mata na shiga taro.
Ta riƙo hannun yaseer yayin da Kamal ya biya mai adaidaita ya tafi sannan suka nufi gate ɗin tamfatsetsen gidan suna gaisawa da masu gadi don an riga an san su aka buɗe musu ƙofa suka shige. Saida suka ɗan taka suka sake shigewa gate na biyu kafin girman gidan ya daɗa bayyana da kuma mutanen dake hada² a cikin ta.

Saudat bata san me yasa jikin ta yayi sanyi ba ganin ta kusa saduwa da su sai dai shima kamal ɗin haka take a gurin sa, taya su murnar biki suka zo yi amma ba lallai a basu muhimmanci ba domin jiya da shekaran jiya ma haka ta kasance idan suka gama musu ayyukan da suke buƙata toh har su tafi ma babu wanda yake lura, kuma ko sallamar kayan biki ba'a musu tunda su ba komai suke kawowa ba. Saudat da tayi musu gudumawar  kayan su muciya, bulogari, ƙoƙo, mara, tsintsiyar kwakwa dana laushi harma dasu kuka, busasshen kuɓewa, daddawa, barkono da kanwa daga ƙauye ce mata sukayi sun gode ba'a buƙata don an daina amfani da irin wannan tarukucen yanzu, shara da injin vacuum cleaner ake yi kaɗa miya kuma ga whisker. Shine tace musu har sharar harabar gida ma da injin ake yinta? To ai sai ayi mata da tsintsiyar sauran tarukucen kuma tayi kyauta da su ga masu buƙata. Haka dai ba daraja suka amsa ballantana ta saka ran samun godiya, bata bar gidan ba tana ji tana gani aka yi rabon kayan ma sauran ƴan aiki.

REINATahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon