✍️ Typing
*K'ADDARATA*
By matar dear
®© Nanamariam20... arewabook
08108353370
Ɗan tsokaci
Ƙaddara kowa yana da tashi irin ƙaddara baka san ranar da zata zo ba kai dai kai fata Allah ya baka ƙaddara mai ƙyau.
Wannan shafin ga baƙi ɗaya naku ne masoyana masu sona na nesa da kusa i love You too much 🥰 a cigaba da follow nana Mariam.
£p 1&2
✍️ Typing
*K'ADDARATA*
By matar dear
Dan babban gida ne ta ko Ina mutane ne zaka Gani suna hidimar su manya da yara iri d'aya ne kayan su atamfa ma kalar ruwan kasa ita ce jikin su, wata Yar matashiyar mata ta taho da sauri tana Ina amarsu yau kika Gani ranar ki don ke muka taru' ta idasa ɗakin ƴan matan kowa ka gani cikin farin ciki suke ana ta ƙwalliya ita kadai ce ko wankan ma batai ba balle ta fara ƙwalliyar matar ta matso kusa da ita ta ce" jiddatukhari lafiya kika kwanta nan ko wanka baki ba?''
Ɗaga kanta tai tare da faɗin uhmm anty wallahi idan na mike jiri nake gani ga ciwon kai.....kallon ta take cikin mamaki tace jiri kuma ko dai rashin cin abinci da baki bane kwana biyu gaskiya zaki sa ma kan ki wani ciwo jidda tashi ki sha tea!!
Tashi tai zaune doguwar riga ce jikinta ta Les taji ɗinki haɗa mata tea ɗin tai Mai kauri ta bata tasha tana gama sha tai amanshi, ga zazzaɓi da ya rufe ta dole aka kira su abba domin kai ta asibiti
Katsina ganaral hospital, zaune yake a office Yana duba wasu takardu da aka kawo mashi hankali ƙwance yake dubawa ƙwankwasa Kofar da akai sai da ya kusa minti 7 Sannan ya bada izini a shigo, ko da ta shiga a ɗan firgice take tace sir an kawo aikin gaggawa yanzu wata mata ce dan ya mutu a ciki aiki za ai mata..
tashi ya yi yasa riga tare da kashe phone din shi ya fito..
Ƙarfe 4pm suka fito daga ciki kai tsaye motar shi ya nufa domin lokacin tafiya gida yayi, yana isa ko time ɗin su Ummu saukar su kenan daga Abuja ya gaida su wata ƴar budurwa a hankali Cikin salon jan hankali ta ce" yaya hamad Barka da zuwa ya aikin?"
Alhamdulilah kawai ya furta don shi ba mutum bane Mai san dogon magana ya Mike domin shiga daga ciki, Ummu ta kalle ta tace" hasina ki hakuri da yadda ya maki kin san dai hamad ɗin yadda yake amma tunda kina nan zaku saba ne kinji hasina ta ta fada tare da kama mata hannu domin shiga daga ciki, daki guda ta ware mata domin ta zauna ciki har ta tafi gida...
Wanka ya shiga ya fito yasa jallabiya fara yana zaune kan kujera marar shi ta murɗa mai kichin ɗin side din shi ya nufa, Lipton ya haɗa da lemon tsami ya fito yana ɗan na waya yana sha, wani group ya shiga na abokai ana ta cemai goro yana matar shi ko haihuwar ta ba ai ba amma dai su jira time..
©©©©©©©©©©©©©©©©©©©©©©
tsoho yanzu wannan sirrin daga mu sai kai zamu barshi kenan?
Ya dafa mai kan shi ya ce"Aliyu kenan wannan sirri ni kadai nasan mainene manufar rufe shi yanzu, don haka dakai har jidda ku barshi haka, ya mika mai wata takarda amshi wannan ka adana ta idan har rai ya yi halinshi sai ka fidda shi kowa ya gani a lokacin ne zasu san mainene ya faru"
Amsa ya yi tare da kallon ta ya yi murmushi ya ce" uhmm babu abinda zaki ce ne kina ta kallon mu"
Ita abin kunya ma ya bata ta ce" baba alhaji mungode da wannan abu da kai mana Allah ya tabbatar da alheri"
