TRILLER

77 0 0
                                    


Asmy b Aliyu
   &
Jeeddah Aliyu

*Assalamu Alaikum wa rahmatullah ta'alah wa barakatuhu Ya hayatiess.*🥰

WE ARE BACK ONCE AGAIN ARE YOU READY?"""🏃‍♀️

#Best hausa Novel 2023/2024
#Team tagwaye novels

GIDAN SARAUTA!"

(Part ɗin mai Babban ɗaki)
Mai babban ɗaki tana zaune a cikin ɗakin baccinta ranta a ɓace yake matuƙa al'amari Aliyu ya fara kaita bango jakadiya ce ta buɗe ƙofa ta shigo bakinta ɗauke da sallama tana zuwa ta zube a gaban mai babban ɗaki "Ranki ya dade gani na amsa kira.
Shiru mai babban ɗaki ta yi na ɗan takaitaccen lokaci kafin cikin izza ta yada ganinta akan fuskar jakadiya wacce ke durƙushe tana jiran umarni "Jakadiya na kira ki ne dangane da naɗin sarautar Aliyu gashi lokaci sai daɗa karatowa yake amma babu wani shiri da Aliyu ya yi kuma ko na nemi shi a waya bana samun shi. Shin kin aiwatar da aikin da na saka ki?"
"Ranki ya dade ɗazu cikin hukuncin Ubangiji cikin dabara na dinga bugun cikin Magaji ƙarami ya tabbatar min da Sarkin sabon birni yana ikko (Lagos) babu wata kasar turawa da ya je a lokaci da muke tattauna wannan maganar da Magaji ƙarami zuciyata har wani zafi take min miyasa Sarkin sabon birni yake so ya watsa miki ƙasa a ido? Bayan yasan 'yan baƙin ciki da masu son gani bayansa burinsu kenan yabar gidan sarauta da masarauta ba ki ɗaya.
Ajiyar zuciya mai babban ɗaki ta sauke wani irin nauyi take ji ƙirjinta ya yi mata har sai yaushe Aliyu zai san muhimmanci da sauratar nan take da a wurinsa?" bata taɓa gani jinin sarauta dake gudun sarauta irin Aliyu ba.
"Jakadiya dauko ɗaya daga cikin wayoyina ki kira Anaal.
"An gama! Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana mai amfani.
Jakadiya ta yi magana tare da miƙewa ta dauko wayar, ta yi dialling numbern Anaal har ta tsinke Anaal ba ta ɗaga ba. "Allah ya ƙarawa uwar magajin masaurata lafiya na kira Anaal amma cikin rashin dace ba ta ɗaga ba.
"Ki aika ɗaya daga cikin bayi su kira min sarkin fada akwai tattaunawa da za mu yi dashi. Sannan ki faɗawa Rahane ta tabbatar magaji ƙarami ya ci karin kumallon sa.
"An gama Ranki ya dade faɗa taki cikawa ta mu makiyanki faɗawa balbale ba ki yi farin banza ba, ki yi naki ki yi na wasu baya goya marayu Allahu ya haskaka kabarin Sarki Usman na Uku.
"Amin jakadiya!
Mai babban ɗaki ta faɗa cikin wata irin izza da taƙama kafin ta kishigiɗa tare da lulawa duniyar tunani.

KUMALLON MATA!!!"

"Zan kara yimaki laifi Rumaisa amman karki manta a kowanne yanayi sonki ne manne a zuciyata karki dauka da son raina zan yi miki wannan laifin ina sonki!"inason ki Rumaisa wallahi ke ce macce ta farko da zuciyata ta fara so da ƙauna.
Yadda yake ta maimaita yana sonta yana kara narkar mata da zuciya har ya fara daga mata hankali kamar wani abu mai girma zai gifta a tsakaninsu.
"Zan dauki kowanne irin laifin da za kayi min banda....
Tun kafin ta karasa ya katseta dan yasan me zata faɗa."Daddy ya yanke shawarar auramin Aydah a karo na biyu nan da jibi.!"
Shi kansa yadda bakinsa ya faɗi kalamar cikin sauri yasha mamaki yana kallon yanayin Rumaisa da ya canja lokaci ɗaya, tamkar bata fahimce me yake nufi ba. Ganin yadda ta zama lokaci ɗaya yasa ya dawo kusa da ita hannunta ya kama ya damƙe cikin nasa yana ganin yadda idanunta suka cicciko da kwallah lokaci ɗaya, "Ki sani Rumaisa aurena da Aydah ba zai canja alakarmu ba Rumaisa idan mahaifinki ya amince dani bayan aurena da Aydah zan aureki saboda ke ce zaɓin zuciyata.
Kalamansa banda ƙona mata rai babu abunda suke cikin tsanani ɓacin rai ta ce "ka aureni a ina? Na haƙura da ka Bashir da gaske na haƙura da kai.
Ta faɗa cikin fita hayacinta. Wasu irin hawaye ne ke fita akan fuskarta tana jin yadda jikinta ya ɗauki wani kalar dumi kamar zazzaɓi zai rufeta lokaci ɗaya. Babu abunda zai canja Rumaisa."meyasa kike shakkar soyayyar da nake yimaki?" Aure za kayi me ya yi saura a tsakanin mu kuma auren da Aydah
Wani irin murmushi take saki wanda bai da alaƙa da farin ciki "Daga ranar da ka haɗa gado da wata macce daga ranar zan daina sonka.! Ba zan boye maka ba ina da kishin da ni kaina ban san kalarsa ba musamman akan ka Bashir. Tun kafin ma hakan ya faru na faɗa maka kar ya faru kaga na canja ka ce dan me?"
Kallonta yake yana juya Kalamanta aransa, kina nufin da ƙanwar tawa zan haɗa gado Aydah ce fa?
Ya faɗa a hassale hakikanin gaskiya Rumaisa ta fara harzuƙa shi akan me za ta ce ya haɗa gado da Aydah, sai kace bashi da ƙwaƙwalwa a kokon kansa, maganganun ta su yi matuƙar yi masa muni.
Rumaisa ta kalle shi a lalace ta ce "Wannan ɓangaren bai da yare"!
Ni dai na hakur....
Tun kafin ta ƙarasa ya fisgota cikin jikinsa abunda bai taɓa faruwa ba a tsakaninsu tana jikinsa tana jin yadda ƙirjinsa ke wani irin bugawa sosai ta rungumesa hawayenta na sauka kan ƙirjinsa "Zan iya mutuwa habibty idan kika sake cewa na haɗa gado da Aydah she's like a daughter to me babu wannan zance a tsakanin mu

Love Story 2023/2024
#Jeeddah Aliyu
#Asmy b Aliyu
#Team tagwaye novels
#Kurman Allo

Share with family and friends
Best regards,Asmy b Aliyu with Jeeddah Aliyu.😍






*BAQEER*
Ayusher Muhd
Umm Asghar

*KURMAN ALLO*
Asmy b Aliyu
Jidda Aliyu

*AKWAI SIRRI*
Zee Bawa
Hajja ce

*MUTALLAB ASAD*
Nana Diso
Billy S Fari

*KULUWA*
Zee yabour
Sadiya Dan

Duka Biyar ɗin akan 2k
Hudu 1600
Uku 1200
Biyu 800
Ɗaya 500

VIP💕🔥
Duk guda ɗaya 1k

KATIN MTN Ta👇
07043079282
Shaidar biya

KURMAN ALLOWhere stories live. Discover now