Cikin rashin fahimta ya ce "Wani irin aure kuma?"

"Haka ya ce wai ranar friday zai mini aure da wani, dan Allah ka hana shi"

"Kwantar da hankalin ki 'yar gudaliyar, zan kirashi in sha Allah, ki daina damuwa"

"A'a ba zan iya dainawa ba, ka kirashi yanzu kawai"

"To an gama, kiyi haƙuri babu mai yi miki wani aure yanzu".

Ya yi ta kwantar mata da hankali, har ta samu ta ɗan nutsu.

***
Yana zaune a falo, yana duba labarai a wayarsa, Mummy na gefe tana shan fruit, ta kalli yadda ya sha fararen kaya, da shuɗiyar alkyabba hannunsa ya sha zobbunan azurfa, sai kaɗa ƙafa yake a hankali.

Ta yi murmushi ta ce "Ka ga kyan da ka yi kuwa? Sai ka fito a basaraken ka na asali jinin galadima, Allah ya kawo gingimemiyar kujera"

Bai kalleta ba ya ce "wace irin kujera ce gingimemiyar?"

"Ka gaji Galadima mana, ko ma kujerar garin gaba ɗaya"

Mahmud ya ce "Mummy you are funny, ni fa sabgar sarautar nan ba ta dameni ba, ki bar ni da karatuna, na kammala na samu aikina period, shi dai da yake ta zazzare ido, na san bai wuce a kan sarautar ba, sai ya je yayi ta yi"

Cikin mamaki ta kalli Mahmud ta ce "Mahmud, wai kai meyasa ba ka da kishin zuci ne, sarautar nan fa taku ce, ta mahaifinku ce gaba ɗaya a ka ɗauka aka kai wani gidan, kuma muna saka ran za ta dawo mana, tun da galadiman yanzu shi ma yana can babu lafiya, kuma da zarar ya mutu babu batun wani ya gaje shi, tun da duk 'ya'yansa mata ne, Jabir kuma bai isa ya saka rai ba, dole gidan nan za ta dawo. Dan haka ba zan zuba ido a bawa Adam sarauta bayan ga ka ba, kai ma ɗan galadima ne, dan haka kai ma ka cancanci ka gaji sarauta".

Mahmud ya ɗan yi shiru ya na tunani, amma bai ce komai ba.

"Mahmud, kar ka watsa mini ƙasa a ido, idan ba haka ba, haka fa zamu cigaba da zama Giwar Galadima ta mamaye komai, ta cigaba da juyamu yadda take so, yaka ke gani idan sarauta ta dawo Adam ya samu, kai menene naka, a wani babin ka tashi?"

Ajiyar zuciya Mahmud ya yi, ya fesar da iska daga bakinsa, ya kalli agogon hannunsa sannan ya kalleta ya ce "Mummy, zan je salla daga nan zan ɗan shiga gari, sai na dawo" yana gama maganar ya miƙe a hankali ya bar falon.

Fauziyya da ke laɓe take jin su ta fito, ta nufi wurin Mummy ta zauna tana murmushi ta ce "Hajiya Mummy, mai abubuwan ban mamaki, irin wannan famfo haka?"

Mummy ta yi murmushi ta ce "Ai ba ayi komai ba ma tukuna, dole sai na sakawa Mahmud ƙawazucin kujerar nan, yaron nan akwai baƙin taurin kai, ɗan uwan ɗayan ne a taurin kai, tun da ƙuruciya nake kwaɗaita masa daɗin mulki, amma yaƙi ganewa, amma zan cigaba da gwada masa fa'idar ace mulki yana hannunsa, in sake rura wutar ƙiyayya a tsakaninsa da Adam, kuma in toshe kafar da sarautar za ta dawo gidan nan, dan ita ma Hajiya Lubabatu kwaɗayi take na ta ɗan ya gaji sarautar idan mahaifinsa ya mutu"
Fauziyya ta jinjina kai ta ce "Mummy kenan, akwai lissafi, na zo miki da wani labari ne mai daɗi"

"Wani labarin kenan?"

"Khalifa Usman wakili, kin san case ɗin su da takawa, kusan shi ne yake trending a media yanzu"

Mummy ta jinjina mata kai.

"To dai in gaya miki shi ne ya gayyaci Samha, wai yana son su haɗa kai, su kawo ƙarshen yaya Adam, ita kuma ta ce bata yadda ba, kin san son shi take yi"

"Eh, na sani, ai itama Samha wata makami ce da nake amfani da shi ta ƙarƙashin ƙasa, amma labarin nan yayi mini daɗi sosai, ke dai ku cigaba da baza kunnuwa, duk abin da ku ka ji, ko kuka gani kawai ku sanar da ni"

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now