"Ɗago ki kalleni" ya faɗa a kausashe, amma ta kasa ta sake sunkuyar da kanta ƙasa.

"Aure ki ke so ko?" Nan ma ba magana sai girgiza kai.

"Shikenan, na fahimta na baki nan da kwana uku, ki kawo wanda zaki aura ɗin, ranar juma'a in Allah ya kaimu sai a yi miki auren kowa ya huta"

Da sauri ta ɗago ta kalleshi, "Wallahi yaya ba haka nake nufi ba, wallahi ba aure nake so ba"

"Ƙarya ki ke yi, baki da aiki sai zance da tambayoyin batsa, aure ki ke so"

"Wallahi a'a, ban san batsa nake tambaya ba"

"Na gaya miki, sai kin fito da miji, ranar juma'a za a ɗaura miki aure"

"Wallahi bani da saurayi, saurayina bai sanni ba"

"A ina saurayin naki yake?"

"A cikin tv nake ganinsa, ɗan wrestling ne, amma ban san a ina yake ba"

Mai sunan Baba ya kalleta ya ce "To tun da baki da saurayi, ni zan nemo miki, ba har da mafarki ana bikinki ba, to saƙonki ya isa za ayi abin da ki ke so"

"Wallahi yaya ba haka nake nufi ba"

"To ya ki ke nufi? Da kunnena fa na ji ki na cewa, ayi miki aure ayi addu'a ki yi tsawo ayi miki aure, tukuna ma me ake yi a auren da ki ke son auren?"

Cikin kuka ta ce "Wallahi ban sani ba"

Ya sake tsuke fuska ya ce "Ƙarya ki ke yi, sai kin gaya mini ko na taka cikinki a wurin nan"

"Wallahi ban sani ba, 'yan ajinmu na islamiyya dai sun ce ana soyayya, kuma ina son in ga an sai mini kujeru da kuma sabuwar katifa"

"Wace irin soyayya?"

"Wallahi ban sani ba, na ji dai suna cewa, soyayya ta na da daɗi, kuma ana soyayya idan an yi aure, shi ya sa nake son na yi saurayi na ji me ake a soyayyar, amma wallahi ba aure nake so ba".

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, yanzu dai tun da baki da saurayi, ni zan samo wanda nake so na aura miki, tashi ki je ki kwanta, ranar juma'a ɗaurin aure"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan girman Allah ka yi haƙuri, manya ake yiwa aure ban da yara"

Cikin zafin rai ya ce "Ni zaki gayawa abin da zan yi, tashi ki bani wuri" jiki na rawa ta tafi ɗaki, tare da fashewa da kuka.
Gaban mama ta je tana kuka ta ce "Mama dan Allah ki saka baki, wai aure mai sunan Baba zai yi mini"

"To ai haka ki ke so ruma, Allah ya sanya alkhairi, duk wanda ya zaɓa miki shikenan"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah mama ki saka baki, wallahi wasa nake yi, ni ba da gaske nake ba wallahi"

Mama ta ce "Maganarku ce ke da shi, babu ruwana, ni gafara nan na kwanta, gobe in Allah ya kaimu na tafi kasuwa na fara yi miki sayayya"

Mama tayi kwanciyarta ta bar ruma, kuka wiwi kamar ba gobe, haka ruma ta din ga yi, ƙarshe a nan wurin bacci ya kwasheta.
Da safe kuwa wasan ɓuya aka shiga yi tsakaninta da mai sunan Baba, taƙi yadda su haɗu, ko karyawa ta kasa yi, haka ta tafi makaranta.

Ruma fa gaba ɗaya hankali ya tashi, ta rasa nutsuwa ko maganar kirki ba ta iya yi, tamkar wadda wani mummunan abu ke shirin faruwa da ita.
Mama tana kallonta, abinci sai dai ta cakala idan ta ɓuya sai kuka, duk ta rasa sukuni.
Mama ta shiga banɗaki ta lallaɓa ta ɗau wayarta, ta kira Abubakar.
Yana ɗagawa ta fashe masa da kuka, har sai da gabansa ya faɗi "Ruma, menene? Meyafaru?"

"Yaya, mai sunan baba ne"

"Me ya same shi, me ya yi miki?"

"Wai aure zai yi mini, dan Allah ka yi masa magana, mama taƙi hana shi, dan Allah ka ce masa ni yarinya ce, dan Allah kar ayi mini auren nan bana so"

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now