Cikin kuka ta ce "Dukana ya yi babu abin da na yi masa, wanke hannuna kawai nake yi shine ya dake ni, kuma wallahi ban yafe ba". Har ta gama maganar kuka take yi, jikinta yana rawa.
Yayin da hankalin ɗaliban duk ya dawo kan su ruma, da jikin Auwal da ruma ta duƙunƙuna masa kamar ya faɗa taɓo.

Haƙuri malamin ya bashi, ya ce ya je ya wanke jikinsa.
Kuka ne kawai auwal bai yi ba, amma ya ji zafin abin da ruma ta yi masa ba kaɗan ba.
Auwal ɗan ajin su Yasir ne, ya san ƙanwar yasir ce, sai dai sam bai taɓa shiga sabgar ruma ba, kuma shi bai ma san ita ce a durƙushe a wurin ba, yayi mamakin ƙarfin hali da kuma tsaurin ido irin na ruma.

Ko da labarin abin da ruma ta aikata ya kai kunnen yasir, haƙuri yayi ta bashi, auwal ya nuna ba komai, amma a cikin ransa yana jin ba zai iya ƙyale ruma ba sai ya ɗau mataki a kanta.

Babu yadda Yasir bai yi da ita a kan ta ba wa auwal haƙuri, amma mursisi ta ce sai dai ya mutu idan har sai ta bashi haƙuri.
Tun da ruma ta yiwa auwal wannan haukan, sauran prefect ɗin ma tsoron taɓata suke yi, dan sun fi yadda da aljanu ne da ita, saboda tsaurin idonta yayi yawa sosai.

*********
Gaba ɗaya ruma ba ta wani ɗokin zuwan salla, saboda ta san ba ta da kayan salla, mama da gaske ba zata ƙara mata komai na kayan salla ba, ko kayan ado da ake saya mama taƙi sai mata, a cewar mama wannan shine hukuncinta na ƙin jin magana. Ta ji haushi sosai amma ta danne ta cigaba da zuba ido, dan kuwa sallar akwai sauran lokaci.
Yau ta shigo gida daga makarantar boko, da wata takarda a hannunta sai yashe baki take yi.

"Deluwa, murmushin me ki ke yi ne haka, takardar meye a hannunki?"

Kallon banza ta yiwa Huzaifa ta ce "Na gaya maka bana son sunan amma ka ƙi daina gaya mini, sai na maka rashin kunya ace bana ji"

Huzaifa ya ce "Yi mini rashin kunyar, ki gani idan ba ɓarar da ke ba".

"Hmm haƙuri halin abin ƙaunar mu Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, shi ya sa ba zan kula ka ba" girgiza kai yayi yana murmushi, ta cire takalmanta ta shiga ɗakin mama.

Mama ce da Abdallah a zaune a falonta suna hira, yana guga.

Mama ta dubi ruma ta ce "Murmushin me ki ke yi ne?"

Ruma ta ɗagowa mama takarda ta ce "Presentation zan yi a makarantar mu, kowa aka bashi, ni ba a bani ba, na dinga kuka da ƙarfi nace idan ba a bani ba, na daina zuwa makarantar, shi ne fa Headmaster ya ce nima sai an bani, spelling b ne zamu haddace words ɗin nan ɗari biyu da hamsin, zamu yi mu da 'yan wata makaranta"

"Ai fa kai ba hankali, wai ki ka dinga kuka da ƙarfi ko kunya ba ki ji ba" Abdallah ya faɗa a hasale.

"To ai da ban yi hakan ba, ba zasu bani ba" tayi maganar cikin taɓara.

Mama ta ce "amma dai ba su san ta nawa ki ke zuwa ba ko da suka baki?"

Ruma ta tsuke fuska ta ce "Wato mama ke ma dai daƙiƙiyar zaki ce mini ko?"

Abdallah ya ce "To mecece idan ba daƙiƙiyar ba" gaba ɗaya haushi ya kamata, ba ta kuma kulasu ba ta shiga sabgoginta. Duk wanda ya shigo ta ce masa an bata spelling b sai su ce ai ba ci za ta yi ba, kada makarantar za ta yi.
Babu wanda ya bata ƙwarin gwiwa, ga yaya Abubakar ya koma makaranta, dama dai yana nan ne shine zai biye mata.

Zaune yake a cikin chemist ɗin, yana jiran mai chemist ya sallame shi, kamar daga sama ta shigo chemist ɗin ta ce "Gashi ka bawa mama maganin ciwon kai" na zai manta wannan muryar ba, ko a mafarki ya ji ta, yana ɗaga kai suka haɗa ido.
Murmushi ta yi masa ta ce "Yaya auwal ina wuni" juyawa ya yi ko da wani take ba da shi ba.

"Baka da lafiya ne?" Tayi maganar tana kallon allurar da mai chemist ɗin yake zuƙewa.

A hankali ya ce "lafiya lau, ya su yasir?"

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now