Washegari, har makarantar boko, yaya umar ya je ya iske ta, ya kai mata sababbin litattafai, ya sanya aka kirawo ta ofishin shugaban makaranta, nan ma ba abin da suke yi, sai wassafawa yaya Umar halin ta na rashin ji.
Ya bata litattafan, yayi mata kashedi tare da jadadda mata, idan har ta cigaba da daƙiƙanci, sai ya sa an yi mata repeating.

*********
Zaune take a kan makeken gadonta, ɗakin cike da kayan alatu kai da gani ka sam mai ɗakin 'yar gata ce.
Ta dunƙule wuri guda a kan gadon, idanunta sun yi jawurr alamar ta sha kuka.
Daga ita sai doguwar riga 'yar kanti, kanta babu ɗan kwali, kallo ɗaya zaka yi mata ka san tana cikin matsananciyar damuwa.
Turo ƙofar ɗakin aka yi, wata babbar mace ce ta shigo ɗakin, idonta sanye da farin gilashi, hannunta riƙe da tray da cup.
Cikin tausayawa ta kalli yarinyar, ta ɗan girgiza kai, ta ƙarasa ta ajiye trayn, ta rungumota tana faɗin "Haba Iman ɗina, shikenan rayuwa bawa ba zai jurewa ƙaddara ba? So ki ke ciwona nima ya tashi?"
Iman ta girgiza kai, hawaye na cika idanunta.
"To Meyasa zaki takura kan ki, haka Allah ya so dama, ai dama tun farko biyayya ce zaki yi mini, kuma Allah bai yi yiwuwar abun ba, amma ki yi haƙuri kin ji babyna"
Ta jinjina kai lokacin da take sake kwantar da kanta a jikin matar.

Ta ɗakko tea a kofa tana bawa Iman a baki, tana sha tana share hawaye, kai da gani ka san akwai tsantsar soyayya da ƙauna a tsakanin su. Ta gama bata tea a baki, ta dinga shafa gashin ta, tana yi mata nasiha.

**********
Mama ta mayar da hankali sosai a kan ibada, mutane na ta shirin zuwan watan ramadan, mama tana ta azumi ita da su yayyen ruma, amma ban da hajiya ruma da cin abincinta ne kawai ya dameta.
Yanzu haka ta cinye taliya, ba ta ƙoshi ba, ta kwaɗa garin kwaki ta zauna tana ci.
Yasir sai masifa yake mata, wai shegen ci ne da ita kamar akuyar ƙauye, ko saurarensa ba ta yi ba ta cigaba da tura abincinta.
Mama ta kalleta ta ce "Wai ke ruma, ko zuciya ba zaki yi ba, azumin nan da kowa yake yi na neman lada ko guda ɗaya ki gwada ba?"

Ɗan ɓata fuska tayi ta ce "Mama ni sai Allah ya kaimu watan ramadan, idan na fara azumi tun yanzu, ai ramewa zan yi kan salla"

"Ke ta ramewa ki ke, dan ubanki ina nuna miki ibada amma ke ba kya so"
Shiru ta yiwa mama tana cigaba da danƙarar garin kwakinta, dan ba ta ji za ta iya wannan azumin ba, idan na du gari ya zo dai ta jarraba.

Bisa ga jajircewar yaya Umar, aka samu ruma take ɗan taɓuka abin arziki a makarantar islamiyya, shima ba wani sosai ba, dan sam ba ta bayar da hadda, tana iya ƙoƙarin ta ko ba duka ba, ta ɗan iya karatun da aka biya musu, saboda idan yaya umar ya titsiyeya ta ɗan samu abin karanta masa dan ya bari ta yi barci, idan kuwa ba baka ba ta san sauran.

Yau ana can ana sallar la'asar, ruma tana zaune tana shan mangwaron ta, tuni ta yi sallarta a cewarta ba za ta iya bin jam'in nan ba, tun tana tsayuwa sai jiri ya fara kwasarta ba za ayi a idar ba.
Ta gama shan mangwaronta, ta tafi wurin alwala wanke hannu.
A wurin alwalar akwai yaran da suma ba sa sallar, suke ta wasan su.
Babu tsammani, ruma ta ji an zuba mata bulala. Tamkar wadda ta fita hayyacinta, haka ta tashi a gigice, tana duba wanda yayi mata wannan ɗanyen aiki haka.
Wani prefect ta hango, bayan ya zuba mata bulalar ya tafi kora sauran yaran da bulala.
Cikin kiɗimewa, ta ɗauki ƙatuwar buta guda ɗaya, ta bishi a guje tana ihu, ta dinga watsa masa ruwan. Ya waiwayo ya tsaya yana kallonta, ta ga hakan bai mata ba ta dinga ƙwala masa butar, daga ƙarshe ta durƙusa ta ɗibi ƙasa tana watsa masa tana kuka.

Tamkar soko, haka ya tsaya yana kallonta, ko ƙwaƙwƙwaran motsi ya kasa, balle ya kare kansa.
An idar da salla kenan, hankali ya fara dawowa kan in da kukan rumaisa ke tashi, bayan ta gama ɓata masa jiki da ruwa da ƙasa a gogaggen uniform ɗin sa, ta haɗa hannayenta biyu tana yakushinsa gami da kai masa duka.

Da ƙyar wani malami ya ɓanɓareta daga jikin matashin yaron, wanda ba dan ya girmeta ba, kuma babu dutse to babu abin da zai hana ta fasa masa kai da dutse, dan ba ta ga laifin da ta aikata zai zuba mata wannan bulalar ba.
Malamin ya dubi ruma ya ce "Meyasa ki ka yi masa haka? Meye haka ki ka yi?"

ƘANWAR MAZAWhere stories live. Discover now