"Kingani koh kingai koh" Mama ce tashigo dakin da Sallama mu duka muka amsata amma ni ban juyo na kalleta ba gabaki daya hankalina nakan ball din, mama tace "mamee tashi kije ana shirin kiran Sallah shima baban naku yanzu zai tafi masallaci"

Mikewa nayi zan  fice sai da nakai bakin kofa Baba ya kirani "Mamee" na juyo nace "Na'am" ki dafamin Baƙin shayi idanna dawo a masallaci saiki kawomin toh na amsa sannan na fice . Ina fita mama tadubi Baba tace"

"Yarinyar nan yanzu tanaso tafika kallon ball abun har damuna yakeyi idan tafara kallo" murmushi Baba yayi yace .

"Ke baki fahimceta ba amma ni na fahimceta. tafara kallon ball ne kawai danta farantamin tun shekarun baya idan tazo taganni cikin damuwa saita canja tasha zuwa ta kwallo tunda tasan inaso dan kawai ta cireni a damuwa. Yarinyace karama amma tanada matukar wayo, duk wani abunda zai kawo farin ciki a cikin gidannan shi takeyi yanzu ki kalla taci jarabawarta dan kawai ta faranta mana inaji ajikina ta dalilinta kan gidannan zai dawo ya hade kamar yanda yake a shekarun baya. Kinga ta dalilinta yan uwanta guda biyu sun dawo gareni inaji wata rana zatayi abunda zaisa gabaki dayansu su dawo" mama ta kalleshi da rashin fahimta, Baba ya nisa sannan yace.

"Aysha da Fadeela sun dawo nanne saboda mahaifiyarsu tasamu labarin na sanya Mamee a makaranta shiyasa taturomin yaran acewarta suma na biya musu ita gani takeyi kamar ta kuntatamin saboda ta turamin yaran bazan iya daukar dawainiyarsu duka ba, amma abunda bata saniba shine naji dadin hakan matuka domin kuwa sun dawo gidan mahaifinsu kenan dawowa tahar Abada, kuma a yanda na lura sunajin dadin zama da mamee sosai Alkhairai dayawa idan zasu faru dani ta dalilin mamee ne inaji ajikina itace silar yayewar duk wata damuwarmu."  Cikeda damuwa Mama tace.

"Toh amma yaya zaka iya daukaan dawainiyar karatunsu duka? Ko Mameen zata hakura fadeelah tunda itace Babba tafara a hankali sai musan yanda za'ayi"  Girgiza kai yayi yace.

"Baza'ayi hakaba Mamee tayi kokari taci jarabawar ne danta faranta min nima ya zamenin kamar dole na faranta mata dole mamee zataci gaba da karatunnan ta farantamin nima zanyi mata haka kyautatawar da zanyi mata kenan"

"Amma tayaya? Tayaya zaka iya daukan nauyin karatun yara uku?" Karki damu Allah zai kawo mana hanya, shiru kawai tayi amma tausayinsa ya cikata tasan baida halin daukar nauyin karatun yaran gabaki dayansu, yanzu haka zaije ya takura kansa ne gashi ba cikekken lafiyane dashi ba, sai takeji inama ace Mamee tafadi wannan jarabawar dan tananne kadai zai samu sauki, kiran Sallar magrib da aka fara yine ya sanyashi mikewa yashige ciki yayi alwala yafito yawuce zuwa masallaci."

Ban tashi daurawa Baba ruwan shayinba saida aka kira isha'i saboda nasan idan yafita sallar magrib baya shigowa  gida sai yayi Sallar isha'i bayan nagama najuye a flask ina jiran shigowarsa na mika masa  ruwan shayin. Dauka nayi nakai masa bayan naji shigowarsa wannan ka'idane kullum sai Baba yasha ruwan shayi idan banice na dafa masa ba toh matansa ne zasu dafa sukai masa.

   Da wayar Mama nakira maryam na shaida mata cewa nima na haye jarabawar domin jiya tun tana tsokanata har itama kanta tadawo ta damu. Ganin yanda nashiga damuwa yasa itama tashiga damuwa amma dake nayi zuciya yasa harna taho ban kulata ba.

Maryam tayi murna sosai kamar yanda nayi ihu haka itama najiota cikin wayar tana ihu tana fadawa mahaifiyarta kashe wayar nayi dan kada mucinyewa mama kudin wayarsa. Mintuna kalilanta biyo da kira cikin sigar zolaye tace.

"Kai ashe dai babu rabon za'ayi miki aure da karancin shekaru" tsaki naja sannan nace.

"Kefa maryam baki iya samun abuba wallh shiyasa wata rana har banaso nabaki labari banza"

"Malama kina sake zagina zan kashe wayata" cikin halin ko inkula nace.

"Toh kashe mana dama ni nasaka ki kirani" mtsewww taja tsaki takashe wayar bin wayar nayi da kallo Afili na furta.

BIBIYATA YAKEYI ( WAYE SHI?)Where stories live. Discover now