"Allah ya sauwake." Shine abunda Baba ya fada sannan ya dubi Fadeela da Aysha yace.

"bakuga Mamanku bane ba? Ba zaku gaidata ba?" Fadeela ce tafara faɗin.

"Ina wuni?" Mama ta amsa fuska a sake sai Aysha ma tabi bayanta suka gaisheta. Mikewa tayi ta fita ta kirawo Aunty, Minti biyu gabaki dayansu suka shigo tare,

Itama sai da Baba yayi magana kafin suka gaida ta hakanma murya adakile kamar wanda bakin su ke ciwo. Bata batawa kanta lokaci wajan amsawa ba dan yanayin yanda sukayi mata gaisuwa gabaki daya babu da'a a ciki. Baba ya jijjiga kai kawai yanajin babu dadi bai san yaushe al'amarin gidansa zai gyaru ba, yana fata Allah ya kawo masa mafita a wannan lamari kafin mutuwarsa idan ba haka ba zai mutu da bakin ciki da fargabar tarwatsewar ahalinsa.

Ya ɗauki lokaci a haka saida gabaki daya wajan suka fahimci abunda ya faru bai yi masa dadi ba. Anty sai taji babu dadi data san halin da zai shiga kenan data amsa gaisuwar ko a yaya suka yi ta,

Yadauki lokaci ahaka sannan yayi gyaran murya gabaki ɗayan su suka fuskance shi sai da yai nisa sannan yace,

"Hajiya Indo (Mama) Habiba (Aunty) ga Fadeela da Aysha daga yau in sha Allahu sun dawo gidannan da zama gabaki ɗaya, anan zasu ci gaba da karatunsu har Allah ya fito musu da miji suyi aure. Na baku amanar su ina so kuji ajikinku kamar ƴaƴan da kuka haifa ne duk da cewa banda shakku akanku zaku kula dasu yanda ya dace kawai tunasarwa ce nayi. Idan laifi suka yi kamar yanda kuke yiwa kanwarsu Mamee hukunci haka suma zaku yi musu." Mama tace,

"Insha Allahu ai abunda yayi Mamee shi yayi su Fadeela Allah ya bamu ikon rike amana."

"Amin" Baba ya amsa bai jira yaji maganar Aunty ba dan yasan idan Mama ta amince itama ta amince. Anty cikin ranta ji takeyi kamar tafito ta gaya masa bazata iya rike wannan amanar ba dan ga dukkan alamu yaran dan ita sukazo aransu, amma bazata iya ba saboda bata san halin da zai shiga ba har indai ta fadi hakan. Ita ta fara mikewa tace,

"Zan koma wajan Hussaini na barshi shi daya." Baba yace.

"Toh  nima yanzu zan shigo na duba jikin nasa." Ya dubi Mama yace,

"Kuje ki nuna musu yanda zasu zauna idan kin nuna musu ki dawo." Amsawa tayi ta tashi tayi waje, bayan tafita Baba ya dube su yace,

"Ku dauki kayanku kuje wajan Hajiya Indo  zata nuna muku daki sannan dan Allah bana son tashin hankali, ku girmama su gabaki ɗayan su mahaifanku ne." Suka amsa da.

"Toh." Sannan suka fice. Yaya Ahmad wanda yake zaune a wajan tunda aka fara bai yi magana ba sai bayan sun fita ya yi masa sallam ya fita."

——————

Ina zaune a aji amma gabaki daya na kosa lokacin tashi yayi na dawo gida dan son sanin halin da Hussaini yake ciki ga kuma tambayoyin da suke raina fall inaji yau gabaki daya sai na sauke su akan Aunty, kuma ina addu'ar kowacce tambaya idan nayi tabani amsar ta.

Ana tashi kuwa jikina har bari yake na dauki Qur'ani na nafice na tattara kan kannena sannan muka yi gida. Ina shiga na riski wani labarin daban da murnata na fito daga dakin Mama zuwa dakin da aka sauke su, sun amasani babu yabo babu fallasa amma ko ajikina danni dama zaman kadaici ni kadai agidan ya isheni. Hira nake yi musu suna amsawa sai da aka kira sallar asubahi sannan na fice dan yin Sallah. Dake dakin da aka sauke su ciki ne da falo harda bandaki ya sanya tunda suka shiga basu fito ba sai da Mama ta aikani na kirawo su muci abinci. Naje na sanar dasu suka shaida min na kawo musu shi nan kamar yanda aka yi musu jiya. Mama tace lallai su fito aci dasu naje sanar musu. Sai da suka dauki lokaci kafin suka fito basu wani tsaya sunci abincin ba suka koma ciki yanzu nikam jikina ya fara sanyi yanda suke mu'amalantarmu kamar ba yan uwansu ba. Hakan yasa nima banbi takansu ba dare nayi na shige dakin Aunty.

"Anty waini menene yasa Yaya yake miki haka?" Na jefa mata tambaya,

"Ba Yaya kadai ba dukkan su haka suke min." Ta bani amsa.

"Amma Anty na Yayan yafi yawa shifa ko yaranki baya kulawa."

"Hmm Mamee kenan sarkin tambaya, kwanaki da kika tambayeni bana fada miki dalilin ba?"

"Eh kin fada amma Anty jikina yana bani kamar ba wannan dalilin bane kadai yasa yake miki haka ta iya yiwuwa akwai wani dalilin daban tunda kinga mu yana mana magana amma baya yiwa su Meema."

Sai da ta zuba min idanuwa kamar zatace wani abun saita fasa, afili tace.

"Mamee kenan sarkin wayo, kema bakya jin dadi yanda yake nuna musu koh?" Gyada kai nayi tayi murmushi tace.

"Shikenan tunda shi baya son su ke ai kina sonsu kiyi karatu sosai ki zama gatansu gabaki ɗaya."

Murmushi kawai nayi amma tabbas nasan akwai abunda Anty ke boyewa saboda ga dukkan alamu Yaya ba haushi daya yake nunawa akanta ba. Har zuciyarsa yake jin haushinta da abunda ta haifa.

Sallama nayi mata na shige dakin Mama na samu ta kwanta amma ba bacci na keyi ba. Nabi gadon nima na kwanta.

"Mama!" Na kira sunanta.

"Uhm" Ta amsa.

"Mama wai menene a tsakanin Yaya da Anty yasa yake jin haushinta?" Kamar bazata amsa niba sai can naji  tace,

"Ke ina ruwanki da kike son sani?"

"Mama ni bana jin dadin yanda al'amura suke gudana a gidan nan, idan inada hali dana gyara."

"Allah yabaki halin wata rana ki gyara. Amma kidaina bibiyar abunda ya hada Antynku da yayyunku banaso." Amin nace sannan nadaura da faɗin.

"Kwanaki Anty ta taba fadamin dalilin, Amma ni gani nakeyi kamar wannan dalilin yayi kadan a tsanar da Yaya ya ke yi mata inaji kamar akwai wani abun." Mama tace.

"Menene tace miki dalilin?."

PAID BOOK
Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab  m Bawa JAIZ BANK shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya Hankli kwance  zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike." A

✔️ote
Follow
Comment
Share please

To be continued

Zaynab Alabura 💕

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡

BIBIYATA YAKEYI ( WAYE SHI?)Where stories live. Discover now