Da sallama na shiga gidan a tsakar gida na samu Mamana da Anty suna gyaran shinkafa sannu nayi musu sannan nawuce ciki na cire kayan jikina na sanya kayan gida sannan na nemi abunda zanci, sai da na tabbatar cikina ya ɗauka sannann na fito izuwa cikin gida na zauna na sanya hannuna a cikin gyaran shinkafar ina yi ina kallon agogon wayar Mama domin kar lokacin da za'a fara wasan kwallon ya yi bana kusa. Da sauri na mike ganin baifi saura minti 2 biyu afara wasan ba Mama tana magana ko jiyota banayi har nakai daki na canja tasha na zauna kallon kwallon.

Ko kawarda idanuwa na bana yi dan bana so wani abun ya wuce ni ba tare da na gani ba duk da kasancewar yau ba team din da nake supporting bane suke buga wasan, Daya daga cikin dan wasan kwallon ya zura kwallo araga wani irin ihu nasaki daya sanya mama ta mike ta shigo ɗakin ina kallonta na bata fuska dan nasan saita hanani kallon kwallon nan. Aikuwa hakan aka yi domin masifa ta fara yi min tana faɗin.

"Sai yaushe zakiyi hankali Mami? Kin gwammaci kibar iyayenki suna aiki kizo ki zauna kallon banza? Kina ihu kamar tababbiya? Toh wallahi gara ki mike tun kafin mahaifinki ya leko yaga muna zaune muna aiki ke kuma kinanan kina kallo kin san ranki da namu gabaki daya baci zai yi." Na karairaye murya nace.

"Wallahi Mama nagaji kinga yanzu na dawo daga makarantar nan kuma zuwa jimawa karatu zan shiga dan Allah kiyi hakuri na zauna na ɗan huta." Mama tace.

"Har mai kikayi da zaki gaji? Ki tashi tun kafin ran mu duka ya ɓaci."

Mikewa nayi raina bai so ba na koma cikin gida mukaci gaba da gyaran shinkafar, muna gamawa na karɓa na shige kitchen na zuba ta a cikin tukunyar dake kam murhu wacce tun ɗazu take tafasa. Haka a tsaitsaye na taya su muka karasa aikin hankalina yana wani waje daban. Muna zaune mu dukkan mu a cikin gidan mahaifina ya shigo cikin girmamawa dukansu matan suka yi masa sannu da zuwa, ni kuma na gaisheshi dake yau fitar sassafe nayi bamu gaisa ba. Ya amsa cike da kulawa yana faɗin.

"Ya ya jarabawar?" Nace.

"Alhamdulillah da zarar munyi gobe mun gama." Yace.

"Toh Allah ya bada sa'a, amma da zarar kin gama taya su aikin saiki tashi kije kici gaba da karatun koh kar ayi wasa."

"Insha Allahu bazan yi ba Baba."

"Toh shikenan Allah yayi miki albarka." Mu dukkan mu muka amsa, yana gama magana yayi sashinsa Aunty dake itace da girki ta tashi ta bishi,

Muna zaune ƙananun ƙannena suka dawo daga makaranta. Mama tace na tashi na taimaka musu su canja uniform izuwa kayan gida. Nan na samu hanyar barin wajan da sauri na mike na shige ɗakin Aunty na fara taimakawa yaranta suka shirya. Gabaki daya yaranta guda uku ne babbar ba tafi shekaru takwas ba Meema sai twins Hassan da Hussain. Ni kuma a wajan mahaifiyata ina da ƙannena guda biyu dukkan su maza ne, Sadeeq sai Amir. Sai da na fara shirya su Meema sannan na fito daga ɗakin Aunty na shirya su Amir. Ban yarda na koma cikin gidan ba dan na san wani aikin zan riske dan haka na zauna karatuna. Koda akayi la'asar ban damu da saina tashi ba tunda nasan cewa ba sallah zanyi ba.

Washe gari kamar jiya da sassafe na fice daga gida dan zuwa zana jarabawata ta karshe. Alhamdulillah babu laifi jarabawar tayi daɗi sosai ina gamata na sanya kai na dawo gida ba tare da na tsaya wani abun ba.

Yau kam na tsaya na taya su aiki sosai dake na san ba jarabawa gareni washe gari ba kuma aranar babu wata kwallon da za'a buga. Yau kam na huta da fadan Mama dan sam ba tayi min shi ba, koda yake dama takance duk ranar da babu wasan kwallon kafa nafi kowa hazaka wajan aiki a gabaki ɗaya kaff gidan mu.

Yau ta kasance ranar Asabar tun safe na shirya kannena na sakasu a gaba muka tafi islamiyya, da safe ake zuwa duk ranar sati  ba zamu dawo ba sai yamma. A kafa muke tafiya dake bawani nisa ne tsakanin haddar tamu da gidan mu ba, sai da na tabbatar kowannen su ya shiga aji kamar yanda na saba sannan nima na wuce nawa ajin.

Karfe sha biyu Aunty da kanta ta kawo mana abinci kamar yanda ta saba, bayan an fito sallah na haɗe kannena dukkan su muka zauna mukaci abincin sannan na ɗauki ƴan canjin dake jikina na saya mana ruwa dashi.
Wannan al'adar makarantar mu kenan karfe ɗaya muke fitowa kowa yaci abinci sannan ayi sallah mu koma aji ba zamu sake fitowa ba sai sallar la'asar karfe biyar kuma a tashe mu mu koma gidajen mu. Bayan an tashi sai da nabi ajin kowanne na dauke su sannan na sanyasu agaba muka wuce gida.

Washe gari lahadi ma hakan take kasancewa acan makaranta muka wuni, sai dai yau Hussaini ya tashi da zazzabi sosai amma haka Anty tace dole sai yaje makaranta acan zai warware. Misalin karfe sha biyu muna zaune a aji malamin su Hussaini ya aiko a kirani, ina zuwa na samu jikin Hussain ya yashi zazzabi ya rufeshi sosai, sai malamin yayi min umarni dana kaishi gida na dawo. A bayana na goyashi na nufi gida, ban samu Anty ba ta fita dan haka ɗakin Mama na wuce dashi.

Bandaɗe da shigowaba Anty ta shigo ta samu halin da ake ciki, pracetamol Mama ta bashi muna nan a kansa har zazzabin ya fara sauka, Anty ta dubeni tace.

"Mamee ki koma makaranta sannan kibi kitchen ki ɗauki kular abincinku ki tafi muku dashi. "

Da toh na amsa ina shirin fita sai ga  sallamar Baban Yayan mu Ahmad Mama tace.

"A'a wanakeji kamar Ahmadu? ashe kana hanya?" Karasa shigowa yayi yana faɗin.

"wallahi ina hanya." Sannan ya gaida ita ta amsa tana tambayar.

"Yaya Maman taku acan?"

"Lafiyanta qalau." Ya bata amsa. Nima na gaishe shi ya amsa sannan ya dube ni yace.

"Me kuma kike yi agida bayan yanzu lokacin makaranta ne? Mama ta karbe zancen da faɗin.

"Kaga Hussaini ne babu lafiya shine ta dawo dashi yanzu." Uhm kawai yace Anty ganin bayi da niyyar gaidata ya sanya tace.

"Ina wuni?" Ba tare da ya kalleta ba ya dubi Mama ya canja zancen da fadin.

"Bari naje wajan Baba dan yanzu ma daga wajan nasan nake nace barina shigo mu gaisa." Mama tace.

"Toh shikenan nima zan shigo yanzu dan bai san da rashin lafiyar Hussainin ba."

Mikewa yayi ya fice jikina duk ya yi sanyi da naga yanda ya yiwa Aunty, ko dan izuwa yanzu ya kamata ace wannan lamarin yabi mana jiki amma gabaki ɗaya ya kasa bin jikin mu. Jiki a sanyaye na fito na nufi kitchen na daukar mana abincin mu na fito wajan Baba na hanga da takalman mata guda biyu sai na Ya Ahmad daya shigo yanzu.

Toh su waye waɗannan matan? Dan nasan cewa idan banda Mama da Anty babu wata mace mai shiga dakin2 Baba sai mu Yayansa, kuma nasan su Mama ma basu san da zuwansu ba. Ganin banida amsar tambayata kuma banida lokacin tsayawa ganin ko su waye dan yanzu kannena na can suna jirana. Fita nayi na wuce zuwa makaranta koma su waye idan na dawo nasan tabbas zanji.


PAID BOOK
Littafin BIBIYATA YAKEYI (WAYE SHI) na kudine ki biya Naira Dari uku 300 Domin kisha karatunki hankaki kwance,
account 0003075326
Zainab  m Bawa JAIZ BANK shaidar biya Ta 08161146563 da zarar kin biya zan sanyaki a group Hankli kwance  zaki samu damar karanta wannan labarin ku shigo daga ciki kar ayi babu ku domin wannan
tafiyace wanda salonta da tsarinta ya bambamta da ko wace irin tafiya karki bari ayi babu ke."
Idan Kuma kina bukatar Aringa tura miki pc kullum Dari hudu 400 kacal zaki biya batareda an Sanyaki cikin group ba zaizo ya sameki har yanda kike."

✔️ote
Comment
Like
Share please

To be continued

Zaynab Alabura."

*HASKE WRITTERS ASSOCIATION*💡

BIBIYATA YAKEYI ( WAYE SHI?)Where stories live. Discover now