💖💖 *SANADIN RAYUWA*💖💖
Ramantic story
*BOOK 2*
*FARIN JINI WRITER'S ASSOCIATION*
1️⃣
"Oh ni “ƴasu ko ina “ƴar nan tamu tashiga oho? Allah ne kaɗai masani, yanzu malam ace yarinyar nan daƙyar muke haɗa mata kuɗin biyan makaranta, ta tafi can kano taje tayi karatu shine yanzu da abunda zata saka mana dashi kenan kwana da kwanaki, a kwana atashi yanzu kusan shekara biyu 2years kenan bamu sa ƴar mu a ido ba"
Ko da jin haka Malam murmushi yayi yana faɗin, "Talatu kenan karki ce haka, abunda zamu cigaba da yi mata shine addu,ah kawai Ubangiji Allah Ya dawo mana da ita gida lafiya kawai, ina ga wannan shine mafita kuma nake ganin itace hanya mai ɓullewa, ki ka san ko cikin wanne hali ƴarmu take yanzu? Tayiwu ba yawon banza ta tafi bah, wani halin tashiga, ki diba mana ki gani gashima yanzu bugu da ƙari yadda zamanin nan ya lalace sace sacen mutane yayi yawa, ko ada ma ya aka cika ballantana kuma yanzu da wannan zamanin ya lalace sai addu'a..."malam yana gama faɗin haka yayi shiru da bakinsa.
Ko da talatu taji haka, buɗar bakinta cewa tayi, " Ƙwarai kuwa da gaske wannan haka yake malam, gaskiya ne abunda ka faɗa kuma yanzu na gamsu da jawaban ka, Ubangiji Allah Ya dawo mana da ita gida lafiya ameeen" wurin cewa ameen ita da malam har suna haɗa baki....
Malam sake ɗaga hannushi yayi ya fara addu, ah, " Ya Ubangiji Allah kai kasan mu, kafimu sanin kanmu, Ya Allah ga baiwarka nan ɗiyarmu yau kwana da kwanki bata gida, Allah kadawo mana da ita cikin aminci Ya Allah, Ya Allah kai shaidane cewa muna cikin damuwa ɗiyarmu bamu da wani kwanciyar hankali Ya Ubangiji Allah ka dubemu da idon rahma kadawo mana da ɗiyarmu gida lafiya, muna tawassali da sunayenka tsarkaka guda ɗari ba ɗaya, Ya Ubangiji Allah kadawo mana da ita gida lafiya ya arrahaman raheem, Ya Allah dan buwayarka kadawo mana ita gida lafiya..." Talatu ko da ta ji haka Malam na addu,ah ya ɗaga hannu, itama ɗaga hannunta tayi tana faɗin ameen aranta har ya gama suka shafa a fuskokinsu Ameen.
Malam gyaran murya yayi kana ya gyara zamanshi yace, "Ni a nawa shawarar ita ce mu cigaba da addu,ah mu duƙufa mukaiwa Ubangiji Allah kukan mu, saboda idan ba haka ba mukace zamu biye ma malaman zamanin nan da kuma masu ruhanai ɗinan babu inda zamuje, kuma nasan kuɗi suke kinga ko mu yanzu ma musamu musa nasawa bakin salati bawai muje mu bawa wasu ƙattin banza ba can suna zaune ni atawa shawarar fa!...." Cewar malam
Talatu tana zaune gefenshi tana jinshi budar bakinta cewa tayi, " Malam ai banda abunka abunda kace shine ai za,ayi domin ko can ɗin za,a ni ina nagata zuwa runda ba kuɗi ne da ni ba, hakan da ka kawo wannan shawara wallahi Alhamdulillah tayi dai dai" tana gama faɗin haka tayi shiru da bakinta.......
Zuwa can suna cikin hira sai ga kiran sallah magrib nan Talatu tai maza ta tashi, ta ɗaukowa malam ruwa alwala abuta domin yayi alwala...
Ko da talatu ta kawo masa ruwa alwala abuta, ya amsa ya je yayi tsarki ban ɗaki, nan ya dawo kan dakalin da ya saba zama yayi alwala ya ɗaura niyya ya fara alwala, itama Talatu ganin haka itama tashi tayi tashiga ɗaki ta ɗauko buta ta wuce banɗaki tayi tsarki, sannan ta fito ko da ta fito taraswa tayi har malam ya fita zuwa masallaci, nan itama ta tsugunna ta ɗaura niyya ta fara alwala sakamakon ita bazata iya zama ba shiyasa shiyasa ta duƙuna.
★★★★★★
Wata kyakykyawar budurwa ce tsaye, taci ado tayi kwalliya tayi kyau sosai matuka tana waya cikin shagwaɓa, ba kowa bace ke waya, ashe Nana ce faɗi take, "pls baby Kamal kai maza kazo kaji, don't keep me waiting, I'm beg u..." Ko da Nana tazo nan azancenta kashe wayarta tayi,sauke ajiyar zuciya tayi hummmm.
YOU ARE READING
SANADIN 2
Romance"Oh ni "ƴasu ko ina "ƴar nan tamu tashiga oho? Allah ne kaɗai masani, yanzu malam ace yarinyar nan daƙyar muke haɗa mata kuɗin biyan makaranta, ta tafi can kano taje tayi karatu shine yanzu da abunda zata saka mana dashi kenan kwana da kwanaki, a k...
