Chapter 5

42 0 0
                                        

Make sure kun karanta chapter 1-4 a tsohon account dina @Aseeyaaleeyu sabona ku gane littafin sosai...
Nagode...

Gabadaya yau tunda Haifa ta tashi bata jin Dadin jikinta, ko abunci ta gagaraci wanda tuni mahaifinta ya gane tana Cikin damuwa.
Mamana.... Alhaji Ibrahim Sakanau ya kira Sunan haifa Cikin nitsuwa sannan ya kama hannunta ya riqe. Dago idanunta tayi ta kalla babanta ba tareda tace komai ba...

Mamana mene yake damunki? Kin sande bana so in ganki Cikin damuwa ko kadan ko? Kuma inde Ina raye babu abunda ya isa ya dameki ban magance miki shi ba' daddy ya fadi yana shafa hannun 'yar sa.
Murmushin dole Haifa ta daki domin bata so daddyn ta yasan abunda take ciki tukunna sannan tace 'daddy don't worry, I'm just having a slight headache Saboda banyi bacci ba inata karatun test jiya but I'll be fine InshaAllah'

Kallon Cikin idonta yayi sosai da suka chanza yayi yasan cewa 'Yar sa tanada damuwa Amma de bata son fada mai yanzu, Amma dai yasan zata fada mai duk sanda ta shirya.
Murmushi daddy ya saki sannan ya shafa kan 'yar tasa yace "to shikkenan mamana, Allah ya bada sa'a ki kula da kanki kinji"
Girgiza Kai haifa tayi sannan ta rungume babanta.

Idanu kawai mummy da yayanta Abbas suka zuba musu suna kallon ikon Allah ba tare da sunce komai ba.
Suna gama cin abunci daddy da Abbas suka wuce office, mummy kuma ta dau waya ta kira 'yar uwarta Azeeza da take aure a garin Adamawa suka fara hirar su. Ita kuwa Haifa dakinta ta wuce ta shirya tsaf cikin wani pink lace dayayi mata kyau sosai sannan ta shiga motarta ta fice daga gidan.

Haifa bata tsaya ko ina ba se kofar gidan su kawarta safeena, Dama ta Riga ta kirata a waya ta shirya dukda haifa bata sanar da ita inda zasuje ba.
Tana zuwa ta dauki safeena a kofar gidansu sannan ta kama hanyar badawa...

haifa tun a waya nake tambayar ki inda zamu kinyi mun shiru, kode sace ni zakiyi?" Safeena ta fadi tana kallon haifa.
Ke rashin hakurinki yayi yawa wallahi, ki jira ki gani mana" haifa ta fadi tare da sakin dankaramin tsaki.

Sati biyu kenan da auren Najmuddeen da Zara'u har ya koma bakin aikin shi. Ba karamin godewa Allah najmu yake ba da ya bashi mata irin zahra. Kullum kwanan duniya kara santa yake kamar ze hadiye ta, ladabi da biyayya wurin zahra kuma baa magana, Dama ta saba tun Kafin suyi aure.

Murmushi wanda yake cike da annashuwa da shauqi Najmuddeen ya saki da ya tina abunda zarah tayi mai Kafin ya fita daga gida yau.
Kamo hannayen shi biyu tayi ta tsaya a gabanshi dab da kirjin shi, dayake de Najmuddeen ya fita tsayi sosai sannan tace 'mijina Allah yayi maka albarka, Allah yasa ka fita a  saa, Allah ya barmu tare'

Murmushi sosai najmu yayi sannan ya du'ko da kansa qasa ya manna bakinshi a saman lallausar nata, tsota yayi a hankali tare da lumshe idan sa  yana Jin yadda dadi yake shiga jikinsa. "Ameen"ya furta har lokacin be cire bakinshi kan nata ba.
Zare bakinta tayi a hankali sannan taje dede kunnan sa ta furta "ka kula da kanka babyna" a hankali Cikin nitsuwa sannan ta saka harshenta Cikin kunnen nashi.

Numfashi sosai ya saki tare da lumshe idanunsa Saboda duk sanda zarah tayi haka jikinsa mutuwa yakeyi sosai.
Zahra kina so in fita kasuwannan yau kuwa?" Ya fadi tare da kankame ta Cikin jikinshi yana Jin wani dadi sosai Cikin jikin nasa.
Dariya Zara's tayi tareda zare jikinta daga nashi.
"Garade a samo mana na abunci, jeka Allah ya kiyaye hanya' ta fadi tana dariya.
Girgiza Kai najmu yayi yana Murmushi sannan ya fita daga gidan.

Allah ya barmun Ke matata" najmu ya fadi yana Murmushi sosai. Inde ya zauna akan kujerar sa inda yake siyar da mai bashida aiki se tunanin matar da da take gida. Babu abunda yake katsemai tunanin zahra sede costumer ne yazo siyan mai.

To yau din ma haka ne, Haifa ce tazo ta ajje motarta gaban bunburutunsa tana jira ya karaso ya tambayeta galan nawa zaa zuba.
Tun daga nesa haifa ta hango najmu yana ta Murmushi shi kadai, hakan ya saka gabadaya ta rikice ta karaji wani sabon sonshi da kaunarshi yana kara Shiga Cikin ko wani sassa na jikinta. Allah Allah take kawai ta karasa gabanshi yayi mata magana hankalinta ya Dan kwanta.

Safeena ce ta kallota lokacinda taga haifa tayi packing motarta gaban me bunburutu.
Haifa? Yau kuma kece zakisha man bunburutu? Duk yawan gidajen mai da muka wuce? Safeena ta fadi cike da mamaki..

Shiru haifa tayi mata Dan gabadaya iya hankalinta yana kan najmu, ta kasa nitsuwa Dan ji take idan har bata ji muryarshi ba zata iya suma. Wannan wacce irin jarabar so Allah ya daura mata ?

Sakkowa tayi daga motar lokacin da najmu ya karaso wurinta dauke da galan da igiyar jan mai.
Sannu da zuwa Hajiya, galan nawa zaa saka miki? " najmu ya fadi kanshi a kasa.

Zuciyar haifa se bugawa take kamar zata bar kirjinta tsabagen Wani irin so da take ji yana kara taso mata. Kallon najmu ta tsayayi tun daga kan dogayen yatsunshi na kafarsa har zuwa kan kyakkyawar fuskarsa dake nauke da annashuwa wanda tunda yayi aure kullum fuskar tasa Cikin annashuwa take. Dogayen gashin idonsa se sama da kasa suke sakamakon kifta idanun da yake yi. Gashin Kansa sun kwanta luff luff kamar na balarabe.

Shurun da Najmuddeen yaji yayi yawa se ya dago fararen idanuwansa ya kalli haifa. Sun kwashe mintuna suna kallon juna take hawaye suka sauka kan fuskar haifa.
Ya zaayi talaka me siyar da mai akan titi yayi irin kyaun nan? Ya zaayi ya sace zuciyarta Cikin kankanin lokaci haka?

Mamaki ne da tsoro ya kama Najmuddeen gani da yayi haifa tana kuka.
Hajiya lafiya? Kin sanni ne? Me nayi miki dan Allah ? Ya tambaya Cikin rikewa...

Share hawayenta haifa tayi tare da murmushin Jin dadi sanna tace.." bawan Allah mene sunanka?"

Shiru najmu ya danyi sannan ya amsata "Najmuddeen"
Lumshe idanunta tayi zuciyarta tana kara bugawa.. ji tayi duk duniya bata taba jin suna me Dadin nasa ba..
Girgiza Kai tayi har lokacin Murmushi be bar fuskarta ba.
Saka mun mai har se tanki na ya cika" ta fadi sannan ta bude motarta ta koma ciki....

Safeena... na rantse miki da girman Allah da Alqurani ban taba jin san wani da namiji a duniyar nan ba kamar yadda nake jin san bawan Allahn ba... Safeena ya zanyi? What if yanada wacce yake so? Ni wallahi ban damu ko talaka bane, wallahi Allah Ina son shi safeena...." Haifa ta fadi tare da fashewa da wani kuka me ratsa zuciya.

Innalillahi wainnailaihi rajiun..... Abunda safeena ta iya furtawa kenan cike da mamaki...

Shima de Najmuddeen mamaki da tsoro ya kamashi don be taba experiencing haka ba a rayuwar sa. Addua yayi da kuma neman tsari daga wurin Allah a zuciyarshi sanna ya fara aikin cikawa haifa tankin motarta kamar yadda ta fadi.....

Please don't forget to vote and comment...
Saboda inaso inji ko kuna Jin Dadin labarin, idan bakwaji se in dena rubuta shi😢

Sabon Alamari Where stories live. Discover now