𝒇𝒂𝒏𝒔 𝒑𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆

15 2 0
                                    

_𝑨𝑫𝑬𝑬𝑴𝑨__
(𝒓𝒂𝒓𝒆)

_𝒘𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒏 𝒃𝒚 𝒎𝒆𝒆𝒆𝒓𝒂𝒓𝒉_

_ 𝒇𝒂𝒏𝒔  𝒑𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_

_ 𝒑𝒂𝒊𝒅 𝒃𝒐𝒐𝒌_

___نصر من الله  و فتح قريب___

After 30 minutes sai ga wani kyakkyawa matashin saurayi Wanda zaiyi kimanin 25yrs ya k'araso inda take.

Hugging juna sukayi cike da farin cikin ganin juna bayan shekaru da dama, Taheer ďan Mamma ne shine babban ďanta kafin Jannah, yana aiki ne a garin Abuja inda yake saida motoci .

shi kanshi yana da arzik'in kansa wanda da k'arfin ikon Allah ya tara har aka sanshi a duk faďin Nigeria kasancewar sa ďan Mamma.

Bayan wani lokaci sukayi breaking hug ďin tana ta zarar ido, ai kuwa caraff Taheer ya kama kunnen ta yana faďin, "ni zaki Kira kice mun Taheer ko, wato in command irin uwar gida ďinnan, Taheer ka kawo mun mota ina Airport".

"Am sorry Yaya bazan sake ba you know me I was just kidding"ta faďa tana k'ok'arin k'wace kunnenta.

Murmushi yayi tare da sakin ta ya rungume ta yana faďin, " I really miss you Jannah I miss Mamma too, I wanted to go home, amma abubuwa sunyi mun yawa".

K'wace kanta tayi tare da faďin, " I just remember ban kira Mamma na faďa Mata na sauka ba, she must be really worried ".

Bayan ta kira Mamma da ita da Taheer suka  sukayi ta kinkiman Kayan da ta kwaso, kusan akwatuna manya bakwai , amma wai anan bata gama siyayyar ba , sai idan ta huta zata shiga kasuwa.

Wani beautiful flat dake Maitama suka shiga bayan mai gadi ya buďe musu gate, sai da ta shiga ta huta tayi komai sannan ta fito suka ci gaba da hirarsu ta 'yan uwa.

Haka sukayi ta hira har dare yayi , sallah kawai suke su dawo suci gaba, a haka har dare yayi ko wannensu ya shige ďakinsa.

Washe gari Tuesday haka ta tashi cike da farin ciki, yau ne zata fara zuwa aiki a JANNAH GROUP OF COMPANIES,  so gaba ďaya ji takeyi kaman Aljanna zata shiga.

Sosai Taheer yayi ta mamaki , dan duk tsawon rayuwar da sukayi bai tab'a ganin ta cikin farin ciki har haka ba.

Bayan ta gama shiryawa haka ya ďauke ta a mota saboda ta matsa mishi akan shi zai kaita.

Suna tafiya sai ruwan murmushi take saukewa kaman wacce zata ga masoyin ta after so many years.

A k'ofar companyn ya danna horn, ba'a tsaya bincike ba saboda kowa yasan motan waye.

Haka suka shiga ciki Jannah kaman ta tashi sama saboda sauri, sai da yayi parking suka fito su duka.

Hannun su sak'ale da na juna suka shiga cikin reception na companyn, duk Wanda yaga Taheer sai ya gaishe shi.

A haka suka samu guri Jannah ta zauna , shi kuma ya nufi gurin masu kula da reception ďin da ya sanar da zuwan jannah.

Bayan an duba da sauri suka ce su k'arasa Office ďin CEO da yake hawa na uku, lift suka shiga suka nufi Office ďin Mr Abeer.

Bayan sun isa hawa na ukun sosai Jannah taji zuciyar na matsanancin duka, nan take jikin ta ya fara rawa.

Shi kuwa Taheer da yaga halin da take ciki sosai ya zaci nervousness ne yake damun ta, amma ita kam bata ma san me ya saka ta rawan jiki ba.

Duk taku ďaya da zatayi yana tafiya ne tare da bugun zuciyar ta, b'angaren Mr Abeer ma haka abun yake.

Ji tayi zuciyar sa na duka , Wanda Rabin da zuciyar sa tayi kalan wannan dukan tun Jannan sa tana nan.

Dam haka k'irjin sa ya buga a sanda yaji ana knocking a k'ofar sa, har sai da wayan dake hannun sa ta faďi.

Dak'yar ya saita kansa tare da bada izinin shigowa, Taheer ne a gaba so baiga waye a baya ba .

Amma zuciyar sa na basa ko waye a bayan tabbas yana da muhimmanci a rayuwar sa, mik'ewa yayi tsaye yana faďin,"hello Mr Taheer, welcome".

Murmushi Taheer yayi yace, "hello Mr Abeer, am here with my sister Jannah", rass rass , gaban sa ya faďi , sai yanzu yasan dalilin bugawa zuciyar sa.

Wato wannan Jannan ce ta zo, nan take fuskan sa ya canja lokaci ďaya, sosai kyakkyawan murmushin fuskarsa ya faďaďa.

Hakan kuwa sosai ya bawa dukkan su mamaki, da sauri ya k'arasa inda Jannah take, wacce jikinta ke rawa sosai.

Rungume ta yayi , hakan kuwa ya bawa Taheer mamaki , gyaran murya yayi , abun da yasa Abeer ya sake ta yana murmushi ya bata hannu yace, " hey Jannah welcome to JANNAH GROUP OF COMPANIES ".

Murmushi ta k'ak'alo ta bashi hannu ba tare da tace komai ba, saboda gaba ďaya bakin maganar ya rufe, ya kasa furta komai.

Haka Taheer ya tafi yabar Jannah a Office ďin Abeer, su kuwa dukka shuru sukayi babu mai cewa kowa k'ala.

Sai daga baya Abeer ya ja hannun ta tare da zaunar da ita a seat dinsa, Wanda duk da bata cikin hayyacin ta, amma tayi mamaki.

Shi kuwa durk'usawa yayi a k'asa ya kama hannun ta yana kallon cikin idanuwanta, sosai yake jin wasu sauyuka a jikinsa da ruhinsa.

Wanda hakan ya tabbatar masa bayan shekaru da dama ya samu wacce zata maye mishi gurbin Jannah, itama hakanne a zuciyar ta,  gani take yi kaman ma Abeer ďinta ne a gaban ta yake rik'e da hannayen ta.

Sai da suka ďau lokaci a haka sannan yace, "Jannah zaki zama PERSONAL ASSISTANT ďina", da sauri ta ďago kai ta kalleshi tace.

"thank you Sir , yes sir, zan zama ",zanso yin hakan , sosai yaji farin cikin jik hakan da yayi , Wanda ya bayyana har a fuskarta.

I will stop here for today,  kuyi sauri ku siya naku, saboda wannan book ďin ya fita cikin sauran.










RAYUWA SUKEYI CIKIN BURI DA SOYAYYA, YA RASA TA TUN SUNA YARA, TSAWON SHEKARU SHA BIYAR KENAN DA YAKE RAYUWA DA GUILTY CONSCIENCE D'IN CEWA SHINE DALILIN DA YASA BATA TARE DA SHI A YANZU, ITA D'IN TA KASANCE WANI B'ARI NA RUHI JINI DA JIKIN SA, YANA RAYUWA NE KAWAI SABODA ITA, TABBAS ZUCIYARSA TANA BUGA WANE DA SUNAN TA, ITA CE RAYUWAR SA, ITA CE ZUCIYAR SA, ITA CE JINI DA RUHIN SA.

BA ZAKU SO A BARKU A BAYA BA, ADEEMA ONE OF BEST PAID BOOKS.

500 NAIRA ONLY

NOTE : EDITED

THANKS YOU MEEERARH

𝐴𝐷𝐸𝐸𝑀𝐴(𝑟𝑎𝑟𝑒)Where stories live. Discover now